23

1.5K 181 49
                                    

RAYUWA DA GIƁI  23


Batul Mamman




Har su ka ƙarasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya ɗaurewa Hamdi kai shi ne yadda Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi.

"Wai mene ne?"

Gefe ya kaɗa kai yana wani rufe ido "Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko mene ne."

Murmushin fuskar Hamdi ɗaukewa yayi. Ta soma harararsa.

"Banda waƙa kuma harda irin haka kake yi?"

"Irin yaya?" Ya tambaya kamar bai gane manufarta ba.

"Meye wani awwnnn don Allah?"

Hannu ya kai ya shafa kumatunta "Saboda ina son ganin wannan hararar da juya idanun naki. You always look cute."

Murmushi ta soma yi ya kuwa sake cewa "awwnnnn" yana dafa saitin zuciyarsa.

Wannan karon dariya tayi. Irin dariyar da bai taɓa gani daga gareta ba. Zuciyarta tayi fari  kamar auduga.

"Kin san wani abu? Zo mu shiga ciki kafin haƙurin Abba ya ƙare."

Bakin ƙofar gidansu ta kalla. Ai kuwa Abbanta ne yake ɗan leƙowa.   Bai yi zaton za su yi dare ba. Kuma sun iso ɗin ma taƙi fitowa. Shi ne ya kasa sukuni. Kada fa ta biyewa Taj al'amari ya kwaɓe a gaba.

"Zan kira ki idan naje gida. I hope ba da wuri ki ke bacci ba."

Bata iya bashi amsa ba da ta hango inuwar Abban da gaske. Kamar an tsikareta ta fito da sauri. Tana hango shi ya koma cikin gida ta bi bayansa. Taj ya yi murmushi kawai. Ya juya baya zai yi ribas ya yi arba da ledojin da ƴan uwansa su ka ajiye mata. Parking ya gyara ya ɗebi yadda hannuwansa za su iya ɗauka ya je ƙofar gidan yana sallama.

Caraf yaji Abba yana yiwa Hamdi faɗan kada ta manta da maganarsu. Shi ba zai iya ja da Alh. Hayatu ba. Jin sallamarsa yasa shi yin shiru. Hamdi kuma ta ruga ciki da sauri.

"Taj baka tafi ba?" Ya fito waje.

"Saƙonta ne ta manta." Ya nuna ledojin hannunsa.

"Harda wahala haka?"

"Ƙanwarsu su ka yiwa. Bari na shigar mata dasu." Taj ya wuce ciki kafin Abban ya ce shi zai karɓa. Hakan zai zama raini ma.

A tsakar gidan ya sake sallama, Yaya ta amsa da yi masa izinin shiga falon. Akan kujera ya ajiye ledojin ya ce da saura. Ta saki baki har yaje ya dawo. Lokacin ita da Abba ne a falon. Waɗanda ya dawo dasu har sun fi na farkon yawa.

"Mene ne haka Taj? Daga zuwa gaishe su kuma sai ka haɗota da wannan kayan?"

"Babu ruwana Yaya. Ƴan uwanta ne su ka bata."

Yaya dai bata jidaɗi ba. Ta san kwaɗayi ba halin Hamdi bane to amma za a iya fassara ta dashi ga wanda bai santa ba in yaga kayan. Da dai bata karɓa ba. Kiranta tayi ta dawo falon da sauri don kiran ta san na faɗa ne. Kaya dama ta tafi cirewa. Wata free doguwar riga ta saka da hula a kanta.

"Me yasa ki ka karɓo kayan nan Hamdi? Tarbiyyar gidan nan kenan?"

Durƙusawa Hamdi tayi a gaban kujerar da ya zube kayan tana ƙare musu kallo. Ita kanta bata san sun kai haka ba.

"Allah Yaya ba roƙa nayi ba. Ba ma a hannuna su ka bani ba."

Kusa da ita Taj ya dawo ya zauna a ƙasa ya fara sauko da kayan gabansu.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now