3

1.5K 148 40
                                    

RAYUWA DA GIƁI 3

Batul Mamman💖

Ga masu tambaya littafin ba na kuɗi bane. Ayi karatu lafiya. SonSo

***

Auren Habibu da Jinjin ba na son zuciya bane kamar yadda ƴaƴansu suke hasashe. Yar mahaifinsu da suka fi ɗorawa alhakin saboda sunanta da Zee tace wato Anti Zinatu ma ba laifinta bane. Abu ne na karamci da sanin darajar wanda ya kiyaye taka darajar.

Aure ne na zumunci domin kuwa kamar yadda Iyaa da Baba Maje suka fito daga zuri'a ɗaya su ma iyayensu mata shaƙiƙan juna ne. Mahaifiyar Habibu ita ce babba. Tayi aure a Kano da  ƴaƴanta maza uku da mata biyu. Shi ne na biyu. Ita kuwa mahaifiyar Jinjin a  garinsu Ɓatagarawa dake Katsina tayi aure. Bata sami haihuwar ba da wuri sai akanta. Ta haifota kyakkawa mai kama da dangin mahaifiyar. Idan ka ganta da ƴaƴan  Inna Batulu za ka rantse ita ta haife su duka. Sunanta Khadija amma ake kirantan Jinjin (jinjinniya don ƙauna). Soyayya da gata gwargwadon hali ta taso tana gani wurin uwa da uba kafin Allah Ya jarabceta da cutar shan inna tana da shekara biyu da rabi. Lokacin da iyayen su ka farga ƙafar ta mutu ba ƙaramar damuwa su ka shiga ba. Idan tana tafiya kafaɗa da ɓangaren ƙirjinta na dama sai ya ballaƙo waje. Wannan abu ya tsayawa uban a rai. Har ta kai indai yana wajen da ta miƙe zai ce,

"Don ubanki koma ki zauna. Kina faman tafiya kamar wata tsuntsuwa babu kyan gani."

Ko ya ce "wannan da ma ciwon tafiya ya yi dake kika huta. Meye haka don Allah?"

Da bata da wayo uwar ke kuka idan yana wannan rashin albarkar. Ƙarshe ma yayi aure shi da matar da lafiyayyun ƴaƴan da su ka haifa su ka taru su ka mayar da rayuwar Jinjin ƙuntatacciya. Yanzu ita ke kukan uwar na rarrashi. Watarana  Inna Batulu ta kawo musu ziyara ta tarar da ƴaƴan kishiyar ƙanwarta suna dukan Jinjin. Abin takaici uwarsu da ƙanwar na kusa amma wai kawaici ya hana ta ƙwaci ƴarta. Garin cangala ƙafa ta kifar da garin masarar tuwon dare. Kuma gudu ma take saboda an biyota za a ci zali.

Inna Batulu na gani tayi kukan kura ta damƙo yaran nan su uku ta bi kowa ta feffela musu mari. Ta ƙare musu zagi irin nasu na Katsinawa.

"Banda raini ba yayarku bace?" Ta juya ga ƙanwarta "shiga ki haɗo min kayanta yanzu zan wuce da ita tunda ba kya so."

"Ba haka bane Yaya."

Da takaici takalleta "kunyar marasa kunya asara ce Luba. Gidan nan kaf har mijin naki ban ga wanda ya dace ki ragawa akan kyautar da Allah Ya yi miki ba."

Jijjiga Jinjin tayi a gabanta ta ƙara da cewa "don bala'in gidan nan ƴar shekara goma sha uku ji ƙirjinta kamar anyi daɓen siminti."

"Kai Yaya Talatu?"

"Allah kuwa. Zuwa yanzu ai yaci ace an fara ganin..."

Da ɗan gudunta Jinjin ta bar wajen don bata son ƙarasa jin hirar iyayen.

Kamar wasa maigidan na dawowa Inna Batulu ta sauke masa nashi kwandon masifar ta ce kuma jiransa take a bata ƴa.

"Gata nan har abada da gaban abada na bar miki." Ya furta ko ajikinsa.

Luba sam bata ji daɗi ba amma haka ta shirya mata kaya su ka tafi. Bata da wani farinciki ko nishaɗi a gidan idan ba Jinjin take gani ba. Da ita take hira tunda miji ya juya mata baya. Sauƙinta ɗaya ta san cewa yanzu za ta sami ƴanci ta wataya kamar sauran yara.

A Kano tabbas taga gata da soyayyar da tasa har take manta da nakasar dake tare da ita. Inna Batulu da maigidanta harma da yaransu sun mayar da ita ƴar gata. Matsala guda ta kula akwai a gidan ita ce ta yayanta Habibu. Lokacin yarintarsu tana iya tuna shi da yawan wasa da dariya. Yanzu kuwa kullum iyayensa cikin kukan sabuwar ɗabi'arsa suke yi.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now