28

1.6K 207 99
                                    

RAYUWA DA GIƁI  28




Batul Mamman💖

This page is sponsored by SAFFADEMPORIUM the world of amazing scents. Kun san da wuya na tallata abin da ban sani ba. To jama'a akan saffademporium ni ɗin jiyau ce kuma ganau. Ido ya gani, hanci ya shaida! Safiyya Ummu Abdoul our one and only Chairlady ta Fikra Writers Association ita ce mamallakiyarsa. Komai na Fikra kuwa daban yake. Akwai Raudha turaren carpet da kujeru, Naeema airfreshner, oils zafafa guda biyar, turaren kaya na maza da mata. Khumra masu tsayawa a rai da kuma turaren wuta.

Za ku iya samunta a manhajar instagram @saffademporium ko wannan layin 07010137848.
Sayen nagari...mayar da ƙamshi gida!

~~~~~~~~

Kun kira
Kun turo saƙo
Kun zo dubiya har asibiti
Ni kuwa me zan ce da masoyan SonSo  idan ba kyakkyawar addu'a da fatan alkhairi ba?

A yayinda da nake post babu abin da yake yi min daɗi sama da kyawawan addu'o'in biyan buƙata da ku ke yi min. Wannan addu'ar ita ce babban abin dake ƙarfafa min gwiwar typing  ko da jikina baya min daɗi domin bawa bai san alkhairin bakin mutane ba. A yau ina mai ƙara godiya ga Allah da ku bakiɗaya. Na sauka lafiya na kuma sami lafiyar jiki bayan aikin da aka yi min. Ahmad Amir dani da duka ahalinmu muna godiya da karamcinku.

Nayi kewarku da sharhinku mai sanya ni nishaɗi. In sha Allah zan cigaba da posting sai dai ba zai zama kullum ba. Sai kun ƙara haƙuri saboda yanayi ya ƙara canjawa. Ga ƙaramin goyo, yara, ɗawainiyar gida da aiki. Duk da haka kada ku sare da tunanin jira zai dinga tsaho. In Allah Ya yarda labarin zai cigaba cikin amincin Allah.

SonSo

***

Idan kaga yadda ake shiga gidan Alh. Hayatu sai mutum ya rantse gayyar mutane ce masu zuwa biki. Nan kuwa kaf ɗinsu ahalin gidan ne. Babu bare ko ɗaya sai masu aiki. Ƴaƴansa ne da jikoki. Kuma a haka wasu ba a nan za su kwana ba. Falon kamar ba zai ɗaukesu ba saboda yawa. Da yake an gama gajiya, rabon wajen kwana kawai aka tsaya yi.

"Duk wanda ya san ya fita ya bar kaya a falo ko cikin ɗakuna tun wuri aje a kwashe. Ba za ku dame mu da cigiya ba gobe." Cewar Ummukulsum ga jikokin. Ita ce babbar ƴar Yaya Hajiyayye kuma jika ta farko a gidan ta girmi Firdaus ƴar ajin su Hamdi.

"Ni dai ban ga kayana da na ajiye a nan ba..."

Cigiyar da take gudu tunda ta san komai wajenta ƙannen za su zo nema mazansu da matansu aka fara yi daga rufe bakinta. Kula su ka yi falon a gyare yake. Aka tambayi masu aiki kowacce ta ce ba ita tayi ba kafin su tafi. Abin da mamaki dai.

"To ko dai Alhaji ne? Naga motarsa..."

Hamɓare bakin mai maganar Yaya Samira tayi kafin ta kai ƙarshe.

"Baban namu ne zai yi muku gyaran falo don rainin wayo?"

"Gani Mugenbo shugaban marasa kirkin duniya ko?"

Muryarsa su ka ji kafin su gan shi yana fitowa daga ƙofar ɓangarensa dake cikin falon. A gurguje masu ƙuruciyar ciki su ka yi kansa saboda sabon da su ka yi dashi. Ƴan matasan kuwa su ka shiga sunne kai.

Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj. Tsaurin ra'ayinsa bai hana shi kamanta mu'amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba. Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra'ayinsa kenan koda zuƙatansu basa son abu. Ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa.

Cikin jikokin wani ɗan shekara biyar zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan.

"Alhaji ba ya yin aikin mata. Shi ba ɗan daudu bane."

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now