29

1.5K 194 38
                                    

RAYUWA DA GIƁI  29


Batul Mamman💖

***
Wata doguwar allura Mubina ta zare daga tsakiyar cikin Kamal ta ajiyeta akan kwanon tasa daidai girmanta. Ta koma gefe ta haɗa yatsunta na hagu da dama ta sarƙesu, sannan cikin dabara ta cire gloves ɗinta. Duk abin da take yi kwata-kwata taƙi yarda ta haɗa ido dashi. Umarni kawai take bawa Nos ɗin da ya taya ta aikin akan abin da zai yi. Shi kuwa yana ta kallonta har ta gama bai ce uffan ba. Canjawar yanayinta ya sanya zuciyarsa tsirgawa don ya san bashi da nasaba da kasancewarsa  babu riga a wajen.

Baya ta bashi yana daga kwance ta harɗe hannuwanta a ƙirji.

"Sauƙin da za ka samu yanzu ba mai ɗorewa bane. Daga shi sai dialysis wanda shi ma tasirinsa ba ya wuce lokacin da za a sami ƙodar da za a dasa."

Numfashi kawai yaja da ƙarfi yana mai rufe idanuwansa. Zuciya da jikin nasa duka sun gaji. A ƙoƙarinsa na ganin bai ɗagawa kowa hankali ba yayi exhausting ɗin kansa. Duk wata lakar jikinsa mutuwa tayi sakamakon jin abin da tace. Tashi ma sai ya gagare shi. Ji yake kamar lokaci zai cimmasa yanzu yanzu. He badly needed a shoulder to cry on. A ɗan rarrashe shi a bashi baki. Sai yanzu yake nadamar ƙauron bakinsa. Sunan Happy yake kira a zuci domin shi ne zai iya bashi shawarar yadda za su fasa ƙwan a gida.

Shirun da ya yi ya sanya Mubina yin gyaran murya.

"Bari na baka wuri ka shirya."

Da sanyin jiki ya yi mata magana kafin ta fita.

"Kada ki tafi Mubina. Bana son zama ni ɗaya don Allah. Not when you just told me I don't have much time left."

Tsayuwa tayi amma bata ce komai ba har ya mayar da rigarsa ya sanar da ita. Ta juya a hankali ta dube shi. Idanunsa sun kaɗa sun yi ja sosai. Sai wata ƙwalla da take barazanar wanke masa fuska. Koma mata ɗan yaro ya yi mai jiran rarrashin uwa. Komai nata da ya danganci juriya a take ya ƙwace. Jikinta ya kama rawa a yayinda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.

"Yaya za ka yi da haƙƙina da ka ɗauka Kamal?"

Idanunsa ko buɗewa da kyau basa yi ya ɗaga kai ya kalleta.

"Me nayi miki kuma?"

"Ka san baka da burin rayuwar duniya me yasa ka bari na kamu da son ka? Me yasa kake azabtar dani ta hanyar nuna min kanka a yanayin ciwo amma ka ƙi bani haɗin kan nema maka magani?"

"Ashe kina sona..." Kamal ya tattaro ƙarfin hali yayi murmushi gami da komawa ya kwanta "kinga har naji ƙarfi a jikina. Bari na huta sai na tafi."

Wani irin kallo Mubina tayi masa "ka san ƙarfe nawa kuwa? Ko ka manta za a sake allurar ƙarfe shida na asuba?"

"Kada ki damu zan dawo in sha Allahu."

Mamaki ya bata. Ta zata gaskiyar da ta faɗa masa mai ban tsoro za ta sa ya soma tunani da yin abin da ya dace. Rai a ɓace ta ce
"You are simply unbelievable! Me za ka je yi a gidan bayan dare ya raba? Kai da ka zo a sume ne kake zancen zuwa gida."

Ya za ayi ya manta? Dama dauriya ya dinga yi a wajen dinner ɗin. Taj na fita da Hamdi ya kirata. Lokacin ta kusa gida ma tunda ita ma taje dinar. A asibiti su ka haɗu sai dai kafin ta iso ya suma a mota. Wurin parking ta dinga dubawa har ta gano motarsa tasa aka ɗauko shi.

"Zan fa dawo da gaske. So nake in sanar da Alhaji lalurata. Ko ba haka kike so ba?"

"Kada ma ka faɗa mana. Ni ina ruwana? Na daina damuwa."

Kamal ya yi murmushi "to wallahi ki canja taku don soyayya babu nunawa juna damuwa bata da armashi. It won't even last."

Ƙwalla ta goge da ƙasan mayafinta ta harare shi "kai ɗin lasting zaka yi balle soyayyarka?"

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now