27

2.2K 199 73
                                    

RAYUWA DA GIƁI  27



Batul Mamman💖

_For Maryam Yusra because you deserve it! Allah Ya baki lafiya._




(Don Allah duk waɗanda su ka biya kuɗin talla na cikin labari kada su ƙosa. Saboda kun fi son wanda zai fito cikin labarin dole sai an zo gaɓar da zai dace. Ina fatan jinkirin ba zai sa muku damuwa ba. Har kullum ina godiya. SonSo)



***

A mafarki ko ido biyu, Alhaji bai taɓa tunanin zuwan wannan rana ba sai da ta zo ɗin. Yau dai zahiri ba zance ba shi ne yake zaune a cikin falonsa babu kowa sai masu gadi da direbansa dake bakin gate su na hira da daddare. Gabaɗaya gidan ana idar da sallar magariba su ka daɗe. Duk an tafi wajen dinner ɗin Taj da Hamdi. Hatta  masu aikin gidan babu wanda aka bari. Kasa zaman falon nasa ya yi ya shiga ɓangaren matan gidan. Nan kam sai da zuciyarsa ta motsa da tausayin kansa. Shiru ne mai ratsa ɓargo. Sai kayayyyakin ƴaƴansa da jikoki da ba a gama tattarewa ba. Wasu ma a ƙasa su ka bar nasu.

"Ganɗoki" ya yi murmushi yana mai duƙawa ya ɗauke kwalbar turaren da aka bari a ƙasa.

Samun kansa ya yi da tsince duk wani abu dake ƙasa wanda bai kamata ba. Yana yi ransa na tunatar dashi cewa duka mutanen da su ka shirya a wajen nan da ɗakunan matansa fa nasa ne. Zuri'arsa ce. Shi kaɗai a shekarunsa sittin da takwas ya tara jikoki sama da arba'in. Ga ƴaƴa ga tarin dukiyar da ko yau ya ajiye kasuwanci ba za su buƙaci komai ba a shekara goma masu zuwa.

Ya auro mata masu mabambantan tushe amma waɗanda su ka yi tarayya wajen taya shi gina gida irin wannan. Tabbas shi ma ya sani cewa arziƙinsa ba a naira da kwabo yake ba. Iyalinsa sune arziƙinsa. Banda dai abubuwan yau da gobe da ba a rasawa amma ya tabbatar cikin ƴaƴansa babu fasiƙi. Allah Ya yi masa gamdakatar Ya shirya masa zuri'a. Kuma komai ya ce ya zauna daram kenan a gidan. Duka ya ɗauka ƙarfin ikonsa da tsare gida ne wanda cikakken namiji kaɗai ke iyawa.

Sai gashi an wayi gari sun haɗa kai suna neman juya masa baya. Jiya sun tafi wajen kamu ƙwai da kwarkwata. Bayan saboda girman gidansa ƴaƴan dangi ma suna cin arziƙin ayi bikinsu a nan. Shi su ka tafi gidan Alh. Lurwanu don su nunawa duniya gazawarsa. Yau kuma Hajiya ta ce masa event centre za su je kuma sai an gansu. Abin tambaya a wajensa yanzu shi ne wai me yasa su duka su ke ganin aibun hukuncinnda ya yankewa Taj? Anya sun san yadda illar dake tattare da daudanci? Habibunsa fa daga son girki ya fara kamar wasa. Idan a baya Taj bai yi ɗabi'un mata ba yanzu zai iya. Surukuta ta shiga tsakaninsu da ɗan daudu kuma ga aiki suna yi tare. Ya numfasa a yayinda ya zauna ya kula cewa gyara sosai ya yiwa falon. Dole ne ya raba Taj da Hamdi. Barazanar da ya yi a Bauchi bata nufin ya karɓi wannan aure. Salwa ce ba zai taɓa bari ta kusanci danginsa ba. Duk lalacewar ɗan daudu yafi mushriki a wurinsa.

***

Ƙememe Yaya taƙi shiryawa,wai ba za ta je wajen bikin ba. Duk ga ƴan uwa za su wakilceta. Za ta zauna a gida da Innarta Luba da ta zo jiya. Aka kaɗa aka raya taƙi chanja shawara. Gashi ƴan matan nata duka ukun basa nan. Yanayin gidansu bai basu damar yin ƙawaye ba. Shi yasa duk wani abu da za ayi da ƙawa tare su ke yi.

Tun azahar Safwan ya kwashesu zuwa event centre ɗin inda a saman wurin ne za a rangaɗa musu kwalliya. Kowacce mijinta ne ya biya mata. Ita Hamdi lalle aka fara yi mata. Ɗaya daga cikin yayyen Taj tana da saloon da wurin lallen amare da na matan ƙwalisa. Wadda tafi iyawa ta tura ta yiwa Hamdi baƙi da ja. Tun kafin a gama ake santin kyawun da yayi. Ana gamawa aka koma kwalliya bayan tayi sallar la'asar. An fito da ita fita ta girma. Sai wanda ya sani ne kawai zai iya gane ita ɗin Hamdiyya ce ɗiyar Habibu Simagade. A haka kuwa za ka yi zaton ƴar wani ƙusa ce. Ana kammala kwalliyar tayi sallar magariba sannan ta saka kaya.

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now