10

1K 164 22
                                    

RAYUWA DA GIƁI  10

Batul Mamman💖



***

Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karɓi loudspeaker ɗin sannan ta rufe ido ta buɗe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matuƙar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da alaƙa da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ƙarfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaɗa kai kamar mai bata damar yin magana.

Mantawa tayi da kowa da komai ta yi taƙaitaccen speech ɗinta mai ma'ana wanda kalmominsa su ka dinga zuwa kamar daga sama. Wuri kuwa ya kaure da tafi. Ɗalibai ƴan ajinsu su ka dinga kiran sunanta da ƙarfi suna tafi. Haka kawai tauraruwarta ta ƙara haske a idanunsu tun bayan da ta kare martabar iyayenta.

Idanunta lokaci lokaci su na kan Taj har ta gama. Tana addu'ar gamawa taga Taj ya kalli wayarsa sai ya kara a kunne ya bar wajen. Za ta sauka aka dakatar da ita. Mai Girma hakimin Gabasawa da kansa ne zai bata kyaututukan da aka tanada dominta. Wani ƙayataccen kwando ne aka saka komai aka lulluɓe da ledar ado aka ɗaure. Ya miƙa mata aka yi musu hoto tare sannan ya ce tasa kyautar ita ce kujerar Makka a Hajjin shekara mai zuwa in sha Allah.

"Allahu Akbar" Malamin da yake MC ya faɗi, sai ɗalibai da iyayen yara su ma su ka amsa.

Murna a wajen Hamdi kuwa ba a cewa komai. Ta sauko daga stage ɗin idanunta cike da ƙwallar zallan farinciki. Wurin da su Sajida su ke zaune ta nufa da sauri. Banda Sajida da Zee harda ƴaƴan ƴan uwan Abbansu mata tsararrakinsu. Halifa ma ya baro ɓangaren maza aka yi murnar tare da shi.

"Hamdi ina kayanki? Yaya ta ce kada mu yarda mu wuce ƙarfe biyu nan."

Halifa ya ƙara da cewa "ana can ana haɗa miki ..."

Kafin ya gama magana Zee ta dage ta doke masa ƙeya.

"To fesal uban zance."

Hannu Hamdi tasa ta saƙalo kafaɗarsa tana dariya "rabu da ita Halifa. Idan ka faɗa min me ake yi zan bar maka duk ragowar provision ɗina."

Da sauri Zee ta riga shi faɗa.
"Walimar ƴan gida za ayi miki"

"Kin dai ji kunya wallahi. Da kayan ƙwalama za a sayeki cikin sauƙi" cewar Sajida tana taɓe baki.

Kayan nata ta nuna musu su ka haɗu da cousins ɗin nasu aka kwaso cikin ƙanƙanin lokaci. Ta koma cikin ƴan uwanta ɗalibai aka yi hotuna harda malamai da musayar lambobin waya. Wasu harda kuka sosai. Ita dai bata yi ba don sabon da tayi da abokan karatun nata na iya lokacin jarabawa ne. Kewar rayuwar makaranta tafi damunta.

Duk abin da take yi hankalinta yana komawa ga tunanin ina mutumin nan na ɗazu. Ta gaji da juyawa ko za ta gan shi Allah bai yi ba. Ga Sajida ta damu su tafi don ita za a yiwa faɗa idan su ka ɓata lokaci. Haka ta tafi zuciyarta tana begen sake ganin sa.

*

Wayar Amma ce ta sake shigowa, ita ce dalilin da yasa ya bar wajen. Kuka take yi wanda ya matuƙar tayar masa da hankali. Ta sanar dashi surukarta Hajjo ta ce lallai ta zaɓi tsakanin aure da aiki amma ba za ta haɗa biyu ba. Mijinta shekarsa huɗu da ritaya ya koma gida gabađaya.

"Wai zaman me nake yi a nan. Taji an ce kai ma ka dawo."

"Ba ki faɗa mata ba daɗewa zan yi ba?"

"Nayi mata bayani duk taƙi ji. Yanzu don Allah 7 months to my retirement sai nayi resigning? An yi min adalci kenan?"

Ta maza ya yi bai nuna mata damuwarsa ba ya dinga rarrashinta. Da ƙyar ta haƙura bayan ya yi mata alƙawarin zuwa Abuja ya sami Hajjo a gidan mijin Amma ɗin inda take zama da amaryarsa da yaransa.

RAYUWA DA GIƁIHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin