Page Sixteen

83 5 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Sixteen

Lamiɗo daƙyar yasamu ya taimaka ma Baba yatashi sannan ya riƙe kafaɗunshi suka  shiga bayin. sunfi mintuna biyar aciki kafin suka fito.

Seda Lamiɗo yataimaka ma Baba yazauna yana fuskantar gabar sannan yakoma baya yatsaya wanda adede lokacina aka buɗe kofar ɗakin,Kawu Hassan ne yadawo daga gida hannunsa riƙe da ledar kayan Baba. Sannu da dawowa muka mishi nida Lamiɗo ayayinda ya ajiye ledan kan tabarma yana faɗin "Najima koh?" gyaɗa masa kai nayi ahankali kafin yace "Ai harna fito zanhau machine naga ana sallah awani masallacin ƴan izala senace bari injona su muyi kawai yanda Inna dawo basai na sake fita ba" Lamiɗo yace "akwai masallacin da har sunyi sallan yanzu? karfe ɗaya da mintunane fah" kallon Lamiɗo nayi sannan nace "masallacin unguwar mune daman sukam suna riga kowa yin sallar juma'a. Ƴan izala ne" Lamiɗo yace "ikon Allah. mukam wataran har biyu ake kaiwa kafin ayi sallah" Kawu Hassan yace "eyi akwai masallatan dasuke kaiwa biyun ananma,wasu kuma ɗaya da rabi. Kowani masallaci dai da lokacin dasukeyin nasu sallar juma'an" Lamiɗo yace "ah lallai kam" kafin yadubi wall clock ɗin ɗakin yadawo da dubansa kan Kawu Hassan yana fadin "Gashi nima abokin nawa baidawo ba bare mutafi" Kawu Hassan yace "koseya yi sallar juma'an zedawo shima?" Lamiɗo yace "bansani ba gaskiya dan bamuyi maganar ba anma tunda har ɗaya da rabi takusa gwanda intafi masallacin inyi sallah inyaso nadawo injirashi" Kawu Hassan ya jinjina kai kafin yace "gaskiya kam gwanda kaje karyazo baizoba" duban ɓangaren Baba dake sallah har lokacin Lamiɗo yayi sannan ya kalleni yace "Nana bari inje masallaci indawo in Hafiz yazo kice masa yajirani ba jimawa zanyiba" gyaɗa masa kai nayi ahankali ina murmushi kafin yajuya yafita.

Ko seconds goma da fita baiyi ba segasu sundawo tareda Hafiz.

Kawu Hassan cikeda mamaki yadubi Lamiɗon yace "har kunyi sallar ne?" Lamiɗo yace "A'a nafita kenan zantafi muka haɗu dashi abokin nawa. daga masallacin cikin asibitin nan yake,wai suma harsun idar da sallah shine kawai mukayi deciding mudawo muyi muku sallama kawai semu tafi gaba ɗaya,in yaso danayi sallah acikin gari zamu wuce tasha mukoma gida" Kawu Hassan yace "oh Allah sarki" Lamiɗo da Hafiz suka ƙarasa jikin gadon da Baba yake zaune akai wanda alokacin har ya idar da sallan.

Dubanshi sukayi Lamiɗo nafaɗin "toh Baba muzamu koma gida. Allah ubangiji yakara sauki yasa garkuwan jikine" gyaɗa mai kai Baba kawai yayi yana murmushi Hafiz ma yace "Allah yakara sauki" nida Kawu mukace "Amin" 
kafin suka dawo kan Kawu suke ce "toh mu zamu koma Kawu" Kawu Hassan yace "Allah yakiyaye hanya. Mungode mungode Allah yabar zumunci" Lamiɗo da Hafiz suka ce "Amin" for some unknown reasons senaji hawaye nabin kuncina.

Baba dake lura da mood ɗina tun ɗazu ahankali yace "Mamana tashi kirakasu waje kuyi sallama seki dawo" gyaɗa masa kai nayi ahankali Ina share kwallana da kasan hijabina sannan nabi bayansu Lamiɗo da tunda yaji Baba yace inrakasu yanufi kofa Hafiz yabi bayanshi suka fice.

Awajen ɗakin nasamesu suna tsaye kuma harlokacin ina matsar kwallah.

Lamiɗo naganin nafito ya ƙaraso inda nake tsaye ya tsuguna agabana yadafa kafaɗuna yana faɗin "yanzu kuma kukan na menene Nanaa?" Cikin gunjin kuka nace "Nima bansani ba" danni kaina bansan dalilin kukan nawaba,nidai kawai nasan I don't want him to go because seeing him around makes me believe I've someone I can count on bayan Baba,someone I Cherish so much,someone I can share my problems with,someone that only seeing him makes me smile koda kuwa acikin damuwa nake. Shakuwata da Lamiɗo,yarda dashi danayi completely,da irin yanda nakejinsa azuciyata daga Allah ne. Lamiɗo jin nace bansan dalilin dayasa nake kuka ba kuma harlokacin banbar kukan ba yasashi tashi tsaye yace "Tunda bazaki daina kukan ba bari mu tafi" cikin sauri na kamo hannunshi Ina ƙoƙarin tsaida kukana nace "Dan Allah karka tafi. Allah nadaina" dole yasake komawa yatsugana agabana yana kallon cikin idanuna yace "Then tell me. Why are you crying?" ahankali nace "sabida banason katafi. zanyi kewarka" murmushi Lamiɗo yayi sannan yasa hannu yashiga gogemin kwallata yana faɗin "Dole zantafi Nanaaa. ayau nacema Umma zankoma,I don't want to fail her. koso kike nangaba innace mata zandawo tahana ni dawowa?" cikin sauri nace "dagaske Inka tafi zaka dawo?" Lamiɗo yace "mezai hana? dole zandawo insake duba Baba inkuma karbi number wayarsa inya samu sauƙi tayanda zanna haɗaki da su Jidda dasu Umma awaya. Kokin fasa Ƴan uwantakan damu ne?" Lamiɗo yakarashe maganar cikin sigar zolaya dasauri nace "A'a Banfasa ba" sannan nakarada "yanzu Inka tafi yaushe zaka dawo" shiruuu yayi yana ɗan tunani kafin yadawo da dubansa gareni yace "Nima bansani ba wallahi Ƴar birni" make kafaɗa na nayi alamar banyardaba sannan nace "nidai ƙafa ɗa kawai" yayi murmushi sannan yace "toh nanda sati biyu?" Cikin sauri nace "A'a kadawo wani weekend dai" murmushi yayi yana kallona sannan yace "toh amma banyi miki alkawariba but I'll surely try" stubbornly nace "nidai kayimin alkawari kawai" Ƴar dariya yayi sannan yace "toh nayi alkawari. I'll come back next week Saturday insha Allah" cikeda Jin daɗi nace "Allah yakaimu. katahomin da abun daɗi" Lamiɗo yace "me kikeso inkawo miki?" Nace "koma miyene inaso" Lamiɗo yace "A"a kifaɗa dai" kafin yafara irgamin abubuwan dayake da tabbacin za'a samu a Gombe yace "Faɗamin Rake kikeso? Ko magarya? ko muruci? Ko dinya? Kogasasshen masara? Ko Dafaffen masara? ko yalo?ko gauta?ko aduwa? kooo dirimi?" zuba mishi idanu nayi inajin yanda yake lissafo sunayensu funnily harya gama sannan yace "toh faɗamin wanne kikeso acikin waɗanda na lissafonnan?" Kai tsaye nace "duka" wara idanu yayi ayayinda Hafiz yakwashe da dariya.

QADRWhere stories live. Discover now