Page Forty

79 2 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Forty

***
Dawowana kenan daga Game field ɗin makarantar mu kasancewar yau Thursday ne,ranar da akezuwa games kowani sati a makarantar mu. Akan gadona na zube sakamakon irin gajiyar dana ɗebo,gaba ɗaya natsani Thursdays sabida gajiyar danake deba wa kowani sati indai naje Games din jarabar nan,gashi baka Isa kace bazakajeba,it's compulsory kuma har attendance prefects suke ɗauka. Ni Abunda yasa banason zuwa Games ɗin ma badan komai bane sedan irin gajiyar da mutum yake debowa agurin wallahi. Asaka kayita tsalle tsalle kamar wani inji,gaba ɗaya karfin ka yakare kadawo kanata nishi da zufa da gumi. Anma ahakan wasu so suke, abun birgesu yake yi unlike me da baya gabana.

Seda naji ana ƙoƙarin kiraye kirayen sallar maghrib sannan nasauko da lazy kafafuna daga kan bunk ɗina,nacire kayan jikina naɗaura towel sannan na ɗauki bucket nafita a ɗakinmu daniyar in ɗebo ruwa inyi wanka kafin nayi sallah dankuwa jinake inbanyi wankan ba bazan taɓa Jin daɗin jikina ba. Koda nayi wanka nayi sallah shiryawa nayi nafice zuwa hostel ɗinsu Aziza dan insameta muwuce dinning hall tare inda daganan inmunyi sallar isha'i kuma se muwuce night prep. Bayan munfito a masallaci muna hanyar tafiya class nida Aziza seta dubene tace "Rukayya gobefah Friday gashi haryau baki kira Yaya Lamiɗo kintuna masa batun visit ɗinmu ba?" murmushi nasakar Mata sannan boldly nace Mata "Basai na tuna mishi ba Aziza. I know he'll surely come insha Allah" Aziza setace "Dadai kikirashi ɗin,kinsan Ɗan Adam da mantuwa" Ƴar dariya namata sannan nace "kin taɓa gani Yaya Lamiɗo yamanta dawani abu game dani? He's never done that kekan ki shaida ce" dariya Aziza tayi sannan tace "Nasani and everytime I asked you to remind him of a day like this kema Thesame answer kike bani and baya taɓa mantawa ɗin kamar yanda kike ikirari anma ni Ina tuna mikine sabida ɓacin rana" jinjina matakai nayi cikeda gamsuwa sannan nace "toh naji Aziza gobe semuje gurin Sir Buharin ki in kirashi" Aziza tace "Allah yakaimu. Nima daganan zan kira Mommy inji karfe nawa zasuzo jibin" tayi maganar excitedly. Nidai murmushi kawai nasakar mata Ina jijjiga kaina in desbelief,wani sa'in zumuɗin da Aziza keyi in za'ayi visit har mamakin ta nakeyi. nothing has changed from her behavior haryau tunda mukazo FGc Azarai,when it comes to her family members jinta take kamar wata yar karamar baby and nima bana ganin laifin ta dankuwa irin soyayyar dakuma shagwaɓa ta da yan gidan nasu keyine yake sawa take ganin kamar bata girma.

Washegari Friday bayan antashi daga class straight wurin Sir Buhari muka wuce nida Aziza inda muka gaisa dashi,tace ya ƙira mata su Mommy,yakira suka gaisa tatambayesu time ɗinda zasu zo gobe asabar ɗin sannan tashiga irga musu abubuwan dazasu kawo Mata inzasu zo visit ɗin wanda inada tabbacin wannan ɗin shine time na yafi a ƙirga data faɗi thesame thing,bayan sungama waya da Mommyn seta bani muka gaisa da'ita kafin mukayi sallama. Haryau Mommyn su Aziza nasona sosai dankuwa jidani takeyi sosai,intazo visiting tadinga nan nan dani kenan hakanan kowani visit seta kawomin abu inkuma za'ayi resuming ma toh saitabama Aziza wani abun takawomin. Tun Ina feeling awkward inajin wani iri harma nasaba naɗaukesu kamar family yanzu. The only problem am having with Aziza yanzu shine hanata zuwa gidanmu danakeyi dakuma rashin zuwa nasu da banayi,tadai taɓa zuwa Babban buli sau biyu a wasu hutu damukayi a baya. Nafarkon a sessional hutun mu na JS1 ne ayayinda ɗayan kuma a hutun 2nd term ɗin mu na js2 ne tajeta. Sau tari kafin atafi hutu takan tambayeni address ɗin gidan Kawu Sani anma se inki bata sabida banason taje a wulakanta min ita,batun zuwa gidansu kuma gani nakeyi bamai barina inje ni dukda dazan iya sa'a in tuntunbi Yaya Salim may be yayi finding way yakaini anna in magana tadawo kunnen Ummi fah? How will she react to it? Shiyasa ma nakebama Azizan hakuri kullum. Data takuramin a hutun session dinmu na JS1 shine nace mata zanje Babban buli muhadu acan kawai.

Ranar datazo Babban buli tayi tayi inbita muje gidansu anma naki dayake tazo very late kan washegari zankoma Bauchi. Zuwanta na JS2 kuma itane ta kwana biyu a Babban buli tareda ni inda takoma gidansu bayan nan,wannan ɗin ma ta matsa muje gidan nasu anma senaki kasancewar lokacin Ina expecting zuwa Yaya Lamiɗo. Banason yazo baisameni ba muyi sabani inkoma cikin Bauchi bamu samu munga juna ba. Nikaina nasan bana kyautawa,bana acting like a genuine friend kamar yanda Aziza takeyi but circumstances ne sukasa hakan and from that very day data tafi gida naga yanayin yanda bataji daɗin abunda nayi mataba nariga nasama raina the next time dazata nemi inje gidan su insha Allah ko akwai abunda yasha min gaba I'll surely leave it and go with her because tanamin kokari,samun kawa irinta se an tona,bakowani zaisoni kamar yanda take Sona ba despite me being no one,ni ba yar kowa ba,marainiyar Allah dani. Aziza Son fisabilillahi takeyi min Kuma tunda yau nasan hakan ba shiyasa danaga kamar ni bana reciprocating nayi deciding canzawa for better anma segashi haryau muna JS3 first term bata kuma zuwa Babban bulin ba,bata kuma sake yimin maganar inje gidan nasuba dukda ma hakan baicanza kokadan daga cikin alakar dake tsakanin mu ba wanda nafi alakanta hakan da tayi zuciyane tazuba min idanu taga gudun ruwana. inda nikuma ayanzu nagama kudurta ma raina a hutun JSCE ɗinmu Insha Allah zanyi ƙoƙarin in goge laifin nawa baki daya.

QADRWhere stories live. Discover now