Page Fourteen - The Message

422 40 3
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Fourteen - The Message*

CIGABAN LABARI

Umma,Basma,jidda da Salma dake kwance kan cinyar Umma tana ta zuba mata shagwaɓa sukajiyo sallamar Hafiz da Lamiɗo daga bakin kofar parlournsu. Umma ce ta amsa sallamar tana mamakin miye dalilin dawowan Lamiɗon gida dawuri haka yau dan a iya saninta indai ba lokacin makaranta ba ana hutu yakan kai goma zuwa sha ɗaya na dare baidawo gidaba. karasowa cikin parlourn Lamiɗo da Hafiz sukayi inda Hafiz yasamu guri yazauna yana gaishe da Umman.

Umma amasawa tayi tana tambayarshi lafiyan Ummanshi,yace "tananan lafiyanta kalau" Umma tace "toh madallah. yaudai ansamu angama jarabawa" Hafiz yace "Eh wlhy Umma. Sekuma aji hudu dayardar Allah" Umma na murmushi tace "Allah yabaku sa'a toh" wannan karan dukansu suka amsa da "Amin" Lamiɗo datunda yashigo yazo yazauna gefenta yace "Umma zuwa nayi naɗauko maki Hafiz tundaga majalisa sabida yamiki clerifying cewa Ƴar birni ba aljana baceba.

Umma da mamakinshi tace "Wai daman bamu gama maganarnan bane Lamiɗo?" sosa kai Lamiɗo yashigayi yana murmushi yace "toh yazanyi Umma. kinki yarda dani shiyasa" Hafiz dake gefe yana murmushi shima yace "Umma ba aljana baceba,kauyen da muke saukan ma garin iyayen Kakartane taje yimasu hutu lokacin anma itada mahaifinta cikin garin Bauchi suke zama. mutanen garin nada mutunci wallahi,sanda ciwon kafar Lamiɗo yatashi ma agurinsu yayita zama suna bashi abinci Inmun dawo muɗaukeshi mukoma cikin gari" cikeda mamaki Umma tadubi Lamiɗo tace "ciwon kafarka yatashi acanne dama?" Lamiɗo yace "Eh Umma amma tun washegarin ranar ya warke" Umma tace "dukda hakadai daka faɗamin. gaskiya zamu koma wurin Mallam Buzu yasake baka wancan maganin tunda dakasha shekarun baya dasuka wuce tunda yanzu ciwon yana yawan tashi akai akai bakamar sanda aka baka maganiba,ai wancan lokacin yajima ciwon kafar bata tashiba" Lamiɗo dayagama gajiya da maganar ciwon kafar yafison ayi na tafiyanshi Babban buli yace "Umma naji saukifah basai munjeba,yanzudai maganar zuwa Babban bulin please! tunda Hafiz ya tabbatar miki ba aljana bace kibarni inje don Allah" Umma ta ɓata rai tace "bawani kunje kun haɗa baki awaje dai zakazo kanamin zakin baki" Hafiz dariya yayi sannan yace "bahaka baneba Umma. Allah duk abunda nafaɗa dagaske ne. mutum ce kamarmu" Umma tace "kai nayarda dakai Hafiz shidinnedai nakeson ganin karshen naci yau" Lamiɗo najin haka yayi sauri ya marairaice fuska sannan yace "Umma ba naci bane wallahi. alfarma nike nema kuma tunda kinyarda mutum ce kamar mu ki amince min inje goben Please" Umma hararanshi tayi tareda duban Hafiz tace "kaji nacin nashi koh?" Hafiz dai dariya yayi baice komaiba.

Lamiɗo yasake marairaice fuska yace "pleaseee Ummana. Agoben fa zandawo insha Allahu" Umma tace "sede in tareda Hafiz ɗin zakuje" dantasan halin Lamiɗo indai batabarshi yajeba yadinga mata jaraba kenan.

Lamiɗo jin abunda Umman tace cikin sauri cikeda murna yace "Zerakani Umma. Allah zamuje tare" Umma tace "katambayi ra'ayinshi ne dazaka gama kaddamar da zance?" pity face Lamiɗo yayi yana duban Hafiz yace "Ina zaka rakani?" dariya Hafiz yayi kafin yagyada masakai ahankali.

Lamiɗo yamaida dubanshi kan Umma yace "Kinji yace zairakani Koh? toh mushirya goben mutafi kenan?" Umma tace "banceba ni. banida kuɗi tukunnan kubari zuwa jibi in ankawomin kuɗin ɗinki se inbaku kujeku" Lamiɗo beso hakaba amma dayake yasan Umman batada shi ɗinne tunda har tafaɗi haka yasashi rungume ta yana murmushi tareda faɗin "Thank you Ummana. Allah ubangiji yakaimu jibin" Umma tace "Amin" ayayinda tamaida dubanta kan Hafiz tace "akawo maka abincine Hafiz?" Hafiz yace "Toh Umma akawo,daman bankoma gida cin abincin dareba kinga inna cika cikina anan sede sucinye kayansu kokuma inci dumsi gobe dasafe in Allah yakaimu" Umma dariya tayi tace "kadaiyi hakuri kaci dumamen gobe kada Ummanka tace nahana ka cin tuwon ta" Hafiz na dariya yace "Toh shikenan Umma" daganan Umma tadubi Basma dagabadaya hankalinta kekan TV tana kallon Hausa Film tace "Basma tashi kizuboma Hafiz abinci" Basma tace "toh" ayayinda tatashi tashige kitchen dan aiwatar da abunda Umma tasata tayin.

QADRWhere stories live. Discover now