Page Thirty Three

29 2 0
                                    


🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Three

Lamiɗo ɗan rusunawa yayi yagaida Ummi daketa kare masa kallo daga ƙasa har sama tanason taga kotasan fuskarsa. Lamiɗo Yace "Ina wuni Hajiya" Ummi tace "Lafiya lau. Ya aka baro mutanen gida?" Lamiɗo yace "lafiya Lau alhamdulillah" Ummi setace "Toh Ɗan samari sede bangane kaba gaskiya kuma saurayincan yace mutanen gidan kazo nema. Kozan iya sanin daga Ina kazo? Kuma wakake nema?" Lamiɗo yace "Eh Hajiya" sannan yatsaya dakyau yace "Daga Gombe nike. Ni Ɗan uwan Rukayya ne from her maternal side. I'm here to see her" lokaci guda annurin fuskar Ummi yagushe.

Zaheera kuwa tunda Lamiɗo yace daga Gombe yake tatuno inda ta sanshi takuma gane shiɗin wanene.

Ummi tsaki ta buga sannan tace "wace Rukayyan kazo nema?" Because she really can't believe cewa wai wannan Hadadden saurayin zezo musu harcikin gida wai yana neman Rukayya, Rukayya of all people,ita abunda yasa taɗan sake mishi fuska dafari ma taɗauka sabon kamu wata daga cikin Yaran nasu sukayi tunda dai bata taɓa ganinshi agidan ba seyau kuma dangin Aunty da customers ɗinta dasuke sayan kaya yawanci tasansu.

Lamiɗo yace "Rukayya Ƴar gidan Kawu Umar" Rai ɓace Ummi tace "sekuma akace maka nan ɗin gidan zuwa kallon mutane ne anyhow koh?" Lamiɗo sunkuyar dakai yayi ƙasa dukda yaji zafin maganar Ummin.

Akafule tace "toh bazaka ganta ba,Mai gidan yahana yaran gidan nan ganin gardawa irinku bare kuma wata Rukayya" Lamiɗo jiki sanyaye yace "Anma Hajiya I'm like her Brother. zuwa nayi mugaisa" wannan karan dakuwa Ummi tamishi cikin hargowa sannan tace "A'a kakanta kake ba Brother ba. Nizaka ma iyayin turanci? Nace nizaka ma iyayin turanci? Toh bazaka ganta ba and that's final. kabari intaje kauyenku kwaje kuyita shashancin ku acan anma ba'anan gidan ba. yarinyar tamai da mana gida kamar na Yan karban sadaka,kowa yazo Rukayya,kowa yazo Rukayya yazo nema" Dan bazata mantaba su Rukayya na makaranta sau biyu Buba nazuwa yana tambaya kota dawo daga makaranta. Kawu Idii ma ya taɓa zuwa sau ɗaya kuma duk da ita suke katari.

Taceda Lamiɗo "kajuya kafita kabar gidannan indai Rukayya kazo gani inkuma bahaka ba se intaro maka samari suzo su fitarmi dakai dan babu mai barinka kaganta" girgizakai Lamiɗo yayi in desbelief, because he just couldn't believe Mata wayayya a ido kamar Unmi could do something like this. Meyakawo wannan masifar haka? Daga cewa yanason ganin Rukayya?.

Tabbas kalamanta dakuma yanda take behaving ya matukar bata mashi rai,so yake yamaida mata martani,soyake yamaida mata magana anma kuma sanin darajar nagaba dashi dakuma albarkacin Rukayya yahanashi yin hakan. He really want to reply each an every word datayi uttering anma baisan maihakan zaijama Rukayya ba bayan yatafi.  Yana nemanta ma kaɗai yazama abun masifa barekuma yace zaiyi ma matar raini akan Rukayya?shibawai tsoron matar yakeyi ba kuma ai duk tsohon dabaiji kunyar hawa jakiba jakin bazaiji kunyar tiko dashi ƙasa ba.

Damuwarsa halin da Rukayyan zata shiga inyace zai yi taking action dan Allah ne kaɗai yasan abunda zasu iya yi mata. Danhaka sekawai yajuya yanufi gate ɗin gidan ayayinda ranshi keyi mishi kuna sosai. He's just imagining what Rukayya must be going through acikin gidannan.

He wish zai ganta yanzu,he wish yasan specifically inda take acikin gidan da babu abunda zai hanashi dawowa ganinta bayan mutanen nan suntafi anma tunda baisani ba seya hakura akan zeje yaganta a makaranta kawai kamar yanda sukayi da'ita last time dasuka haɗu during their visiting day. Yanajin Ummi nata babatu da masifarta anma ko juyawa baiyiba bare yayi acting as if yamasan me takeyi ahaka harya fice agidan.

Zaheera naganin yafita tajuya takalli Ummi sannan tace "Ummi shine yaron da muke baki labari nida Aisha ranan. Shine yaje ganin Rukayyan a makaranta" baki sake Ummi tace "ikon Allah! Amma ta Ina suka haɗa dangi da Mahaifiyar Rukayya? Nifa danginta danasani tunsanda muke zama gida ɗaya Yan Babban buli ne kawai" Zaheera ta tabe baki tace "toh dai cousin ɗintane,itada bakinta tafaɗa Kuma gashi yanzuma kinji yafaɗa da bakinsa" Ummi tace "toh jarabar ta menene dazai biyota har gida?" Zaheera tace "Nima bansani ba Unmi, amakarantar ma bakiga yanda yadinga rungumeta baneba,kamar wanda suke soyayya fah" Ummi rai ɓace tace "Soyayya kuma? Rukayyan harnawa take dazata san wani Abu waishi soyayya Zaheera? sede in kice akwai shakuwa sosai atsakaninsu" tura baki Zaheera tayi sannan tace "Ummmm Ummi toh ba daga shakuwar ake komawa soyayyan ba? Yanzu bakya tunanin zai iya Sonta agaba tunda haka kawai ma yana biyota harnan gida musamman dan yaganta" tsaki Ummi tayi sannan tafara tafiya tace "ke dallah mutafi ni Ina ɓata lokaci akan abunda bashi baneba. Ni abu ɗaya nasani ko uwarme ke tsakanin su da Rukayya nan bada jimawa ba zai hakura ya rabu da ita barehar yayi wani zancen yana sonta. Yarinyar da take zaune agidannan kamar Ƴar aiki,sutura maikyau ma nangaba gagararta zaiyi bare azo ga batun tayi kwalliya tayi fasalin dahar wani zaiganta yace yanaso. Inma zaki kwantar da hankalin ki kikwantar da hankalin ki dan baki kaini son ganinta cikin kunci ba"

QADRWhere stories live. Discover now