Page Nineteen

51 4 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Nineteen

Kawu idrissa yace "kunedai kuka ɗauki wannan maganar da wata manufa daban. dannidai aganina danan garin da Giyaɗe duk ɗayane anma if you two really insists on this's the right thing to do,then so be it. Shikenan tazauna anan ɗin"

Kawu Sani yace "Yauwa. hakan dai yafikam" Gwaggo Suwaiba datunda Kawu Sani yayi magana take lura da yanda yanayina yacanza lokaci guda tace "toh kodai zantafi da'ita taɗan zauna acan nawani lokacine seta dawo?" Kawu Sani kai tsaye yace "A'a Suwaiba. Babu amfanin yin hakan dan kuwa sa'anninta duk sunkoma makaranta,zango yafara yin nisa ayayinda itako fara zuwa batayiba. Yanzu abunda yakamata muyi shine mumaida hankali akan maganar karatunta inyaso in hutu yayi setazo Giyaɗen tayi muku hutu"

Gwaggo Suwaiba da dama sabida ganin yanayina ne yasata kawo wannan suggestion ɗin tace "toshikenan. Allah ubangiji yasa hakan shiyafi alkhairi" sannan tadubeni da dab nikeda fashewa da kuka tace "Toh Rukayya kindaiji abunda Kawunanki sukace,kiyi hakuri kiyi zaman ki anan. danan dacan din duk ɗayane babu wani banbanci hakanan yanda nike kanwar Yaya Umar haka suke Yayunsa sannan inada tabbacin irin kulawar dazan baki a Giyaɗe suma zasu kwatanta insha Allahu" ta dafa kafadana cikin sigar lallashi tace "ki kwantar da hankalinki. kimaida hankalinki akan karatunki na Arabia da boko dankuwa shine jigo na rayuwar kowa azamanin mu na yanzu. Maganar Yaya Umar kuma,yariga yatafi kuma dukkannin munnan tafiyar zamuyi,kowa lokacinsa yake jira sannan babu gatan dazaki nuna masa daya wuce kiyi masa addu'a aduk lokacin dakika tuna dashi dakuma duk lokacin dakike sallah"

Tunda Gwaggo Suwaiba tafara magana nakasa resisting hawayena duk da kuwa naso in riƙe kukan nawa anma abun yaci tura. Yes mutuwar Baba is still hunting me anma batun inzauna tareda iyalan su Kawu shiyafi tayar min da hankali ayanzu. Tunda nasamu nabaro wannan gidan shekarun baya dasuka wuce ban taɓa tunanin ko amafarki zankoma wannan gidan ba anma segashi rana a tsaka ana sanar dani dasu ɗin zanzauna, incigaba da rayuwa na tare dasu gashi kaf cikinsu babu gwara,babu gidan wanda zanje ince zansamu sassauci daga kan Ƴaƴansu har Matayensu bare har inyi addu'ar Allah yasa akaini gidan wane dan inji daɗi. Duka iyalansu sun tsaneni,baswa sona,baswa kuma kaunar ganina cikin farin ciki. nikaina wani sa'in nakanyi mamakin mena tare musu a rayuwa dankuwa aganina hujjojinsu are not enough. Dan Baba yana nuna yana son Mama agaban kowa,yana kuma yimata duk abunda zaisata farin ciki bekamata ace sun tsaneta ba. Mijinta ne banasuba, kuɗinshi ne bana wasu ba kuma shiyaga zai iya ba'ita tasaka shiba and moreover bashi yahana nasu mazajen suyi musu ba. ra'ayin kansu sukebi kuma kowa da irin tasa zuciyar hakanan kowa da irin nasa plans ɗin arayuwa.

Haryau Ina mamakin wannan al'amari,Ina mamakin miyasa tsanar da akayiwa Uwata yadawo kaina dankawai ubana yana sona nima,dankawai inacikin jin dadi da walwala fiye dasu se aji haushina ba wani dalili bayan shi? kukan danakeyi gaba ɗaya seyasa jikinsu Kawu Sani yayi sanyi dan haka cikin raunanniyar murya Kawu Adamu yace "Rukayya kidaina Kuka hakanan. shawarar damuka yanke shine mafi a'ala agareki,amanar ki da mahaifinki yabar mana mukeson riƙe wa kuma kobaibar amanarki a hannunmu ba mu ɗin masu rike kine insha Allahu dan tamkar iyaye muke agareki sannan danmun hanaki binsu Suwaiba Giyaɗe bahakan yana nufin zamu hanaki zuwa gidan wanda kikeso acikin muba. Kizaɓa duk inda kikeso,inma gidan Yaya idrissa ne dukda compound ɗaya mukedashi,inma gidana ne,inma kuma gidan Yaya Sani ne kizaɓa,duk inda kikadai ga zaifi miki daɗin zama nan za'a kaiki kinji?"

Cikin gunjin kuka na gyaɗa mishi kai sannan nace "ko'ina aka kaini ma duk ɗayane" dankuwa bana tunanin zan iya zaɓan gidan ɗaya acikin su ukun dan babu gwara gaba ɗayansu,nidai kawai nasan my life will surely change. From happiness to sadness,from meaningful to meaningfulness indai har a karkashin su dakuma iyalansu zanzauna.

QADRWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu