Page Thirty

79 7 1
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty

Haka nacigaba da rayuwana cikin FGC Azare,rayuwar dake cikeda mockery, ɗaukana ba'abakin komaiba,ganina as wawiya anma hakan kosau ɗaya bai taɓaaba hanani yin abunda yakaini makarantar ba dankuwa Aziza da books ɗina sune abokanaina acikin FGC Azare. tun ina damuwa da abunda mutane ke faɗi akaina haryazo yazamemin jiki.

Su Yaya Safiya kuwa suma kamar Sadiyar ne dankuwa ko ahanya muka haɗu baswa nuna wa ma sunsanni,sautari seniors mate ɗinsu zasu kirani su aikeni kosu sakani ɗauka musu ruwa agabansu anma ko sau ɗaya basu taɓa yin magana ba sede ma suma su haɗa danasu. Yaya Zaheera kuwa duksanda nake hostel babu wanda tamaida ɗan aikenta irina,yi takeyi kamar anturo ni makarantar specifically dan inayi mata aikene. Dankuwa ko a classes area during break nitake kawowa shopping list ɗinta inyo mata nakai mata class ɗinsu. A hostel ma kuma ban tsira ba dan har ɗakin danake take turowa a kira ni,inda Allah yataimakeni ma daman ni I'm not fund of zaman hostel shiyasa sautari ko ta aiko akirani ma za'azo atarar bananan sede in daga baya inji labari abakin Ƴan ɗakin mu.

Haka ranaku suka dinga canzawa suna komawa weeks har satin visiting yazagayo. Karkuso kuga dokin da Ɗalibai keyima zuwan wannan rana hakanan kowa shiri yakeyi babu kama hannun yaro,daga masuyin sabon kitso semasu saka relaxer. Harta kayan daza'a saka ranar visiting ɗinma wanki da guga nadaban akeyi mishi a ajiye. wani kuwa daman tun dawowarsa ya ware set ɗaya yaƙi yasaka sabida yanason yasaka ranar visiting Ƴan gidansu suganshi fes fes. Inner wears kansu sabbi akesakawa ranar visiting indai mutum yanada shi ayayinda wasu kuma har saya sukeyi.

Cikin masu shirin visit kuwa harda Aziza dankuwa tun last week take damuna da hirar yan gidansu zasuzo tana faɗamin how excited she'll be idan tagansu anma ni agurina abun bahaka yakeba. nida za'ace za'ayi cancelling visiting day ɗinma ba ƙaramin farin ciki zanyi ba dankuwa nasan ko anzo visiting ɗin ba farin ciki zanyi ba kamar yanda sauran yara zasuyi idan sunga yan gidan su sunzo.

Aziza har mita ta dingamin wai bana farin ciki zanga mutanen gida sede inyi murmushi kawai ayayinda araina nake raya "Aziza bakisan gidan danake zama ɗin ba ne shiyasa kike faɗin haka. mutanen da dagasu har Ƴaƴansu basu kauna ta"
Ranar laraba adole Aziza tajani mukaje ironing clothes ɗinmu a laundry dukda kuwa baranar nasabayin gugaba. Ni a weekends nakeyin gugana every week anma seta dage da ai na fita visiting ground zan goge ranar so inzo muje,haka mukaje mukayi gugan da yanma inda ahanyar dawowanmu mukabi ta wani shop dake hanyar hostel Aziza tasaya mana riboms guda biyu kala ɗaya kowa ɗaɗɗaya tareda inner wears kala ɗaya shima kowa ɗaɗɗaya. Nibanma san harda ni tasayaba seda mukaje hostel taɗauka tabani nawa sannan nasani. Kin karba nayi dafari anma dayake tafini tsiya setaje tasakaminshi a locker na ta datse lockern da padlock wai duksanda nashirya accepting kyautar data bani inzo inkarbi makullin a hostel ɗinsu.

Hakuri nadinga bata sannan nace mata nayarda zankarbi kayan datasayamin ɗin sannan tayarda tabani makullin. Godiya namata ayayinda na rungumeta inajin wani irin kaunarta na kara samun gurbi azuciyata. She's the only friend I can always call a real friend tunda ko ada danake da gatana batasoni kamar yanda takesona a yanzu ba.

Niba mayyar kashe kuɗi baneba sannan ban taɓa damuwa da inje inkarbi kuɗin break awurin Guardian ɗinmu ba anma ganin yanda Aziza ke kashe mana kuɗi kuma komai tasaya seta ce dole tare zamu raba yasa nima nazake damtse nafara zuwa ina karban Kudi awurin Uncle Adam akai akai inayimana abu tare.

Provision ɗina kuwa haryau bai ƙare ba dan kwata kwata ma ni baswa gabana,baiwuce incisu sau biyu ko sau uku a satiba ba sabida nafi aminta da abincin dinning. Biscuits da drinks ɗina nedai suka kare tuni dayake innatashi fita dashi nida Aziza nake fitar mana Itama kuma hakan takeyi.

QADRWhere stories live. Discover now