Page Twenty Nine

36 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Twenty Nine

Harsuka gama gyarama Sadiya gado suka tafi basu ganni ba dayake da goman dare yayi anyi light off kuma inda na raƙube na tsaya babu wanda ya kunna Torchlight.

Ɗakin nashiga na karasa kusa da bunk ɗina bayan fitarsu. akwatina najanyo na buɗe na ɗauki katon lantern ɗinda Aunty tasaya mana iri ɗaya nida Sadiya sannan na kunna lantern ɗin,na ajiyeshi saman locker na kafin nafara ciro kayayyakina ina jerasu cikin locker harna gama narufe namayar da akwatina kasan gado inda alokacinne kuma Sadiya tadawo daga rakiyarsu Yaya Safiya wanda inada tabbacin dasuka dawo tabi ta ɗakin Yaya Zaheera dan rakiya kaɗai beci ace tajima hakaba. Inajinta taɗauki buta tafita waje harta dawo tazo ta dale gadonta batareda tacemin komaiba takwanta. Nima shimfida gadona nayi sannan nahau nakwanta Ina tunanin yanda rayuwata zata kasance acikin makarantar ahaka har bacci yayi awun gaba dani.

***

Lamiɗo tunbayan dayayi resolving issues ɗinsa da mutanen Fada bashida wani tunani daya wuce yanda zaiyi yanemi alternative ɗin sake zuwa Bauchi. Dukda bai furtama kowaba anma abun naranshi yanakuma da yaƙinin zeje ɗin insha Allahu.

Sau tari yakanji kamar yanemi shawara gurin Hafiz anma inya tuna alkawarin daya daukar ma kanshi nacewa bazai sake yimasa maganar data shafi Rukayya ba seya fasa yimasa maganar yabar abun acikin ransa kawai. Umma kuwa ko gigin hauka yakeyi yasan bazai tunkareta da maganar ba tunda shiya mata alkawari last time data bashi permission ɗin zuwa.

A bangaren Hafiz kuwa beyi mamakiba da Lamiɗo yadaina yimasa maganar Rukayya don kuwa yasan halin abokin shi sarai da zuciya,inyace bazaiyi abuba toh bazaiyinba hakan inyace zaiyi toh seyayi. Toh anma abunda baiganeba shine shin Lamiɗon ya hakura da zuwa ganin Rukayyan ne kokuwa? Tunda baiga alamar yana making wani effort nasake zuwa Bauchin ba. Seya ɗauki hakan amatsayin ya hakura and then seyaji daɗin hakan dukdama baifito fili yasanar da Lamiɗon ba.

Kwatsam ranar laraba Lamiɗo nadawowa daga companyn dayake IT se Umma tatareshi da labarin abokinshi dayaje yasamu aiki awurinsa last weekend yakirashi awaya ta wayarta dayake layinshi na ciki,wai akwai vacancy nawani aiki if he's interested yaje yasameshi a shago. Take Lamiɗo yace "Umma dakince mishi bazanyiba kawai! Last week ɗinma aidan ina bukatar kuɗin ne shiyasa naje nayi dakoh" tsuke fuska Umma tayi sannan tace "agaba bazaka nemi kuɗi ba kenan kakeson kacemin komi? inma zakaje gwanda kaje kaji wani irin aikine. Aibaifi rage zaman banza ba" ganin Umma tadage se Lamiɗon yace "Toh Umma anjima zanje shagonsu insameshi insha Allah" cikeda farin ciki Umma tace "Allah yakaimu anjiman. Allah kuma yamaka albarka" Lamiɗo yace "Amin ya Allah Ummana" sannan yazauna yana kwala kiran Basma wai tazo tazuba mishi abinci yaci.

Dayanma Lamiɗo na fita straight kasuwa yawuce shagonsu Abdulmalik kuma yayi sa'an samunsa a shagonsu don haka seya bashi hannu sukayi musabaha yakuma gayamasa Umman sa tabasa sakon daya bayar abasa ne shiyasa yazo ganinsa yanzu.

Murmushi Abdulmalik yayi sannan yace "aikine akeneman masuyi shine nace bari in faɗa maka tunda last week naga kazo nema,may be yanzunma kanada bukata" take Lamiɗo yace "A'a Abdulmalik wancan ɗinma dandai Ina bukatar kuɗine alokacin shiyasa nayi amma dai faɗamin,wani irin aikine? may be in iya during my leisure time" se Abdulmalik yace "Aikin transporting kayan abinci ne zuwa other states daga wani campany dakenan garin daman. Suna neman new employees shine nace barina maka magana if you're interested" Lamiɗo Jin an ambaci transportating abinci zuwa wasu states yasashi saurin cewa "wasu states za'ana kaiwa Abdulmalik?" Abdulmalik yace "inaga Kano,Adamawa,Bauchi,Taraba,Yobe, maiduguri dadai sauransu. Kawaidai northern states" Lamiɗo yace "toh amma mutum ɗayane zaiyi aikin kowani state ɗin kokuma assigning mutane akeyi kowani state?" Abdulmalik yace "A'a assigning mutane akeyi,kamar kowani daf guda mutane biyune ake assigning sannan za'a iya basu state biyu ko uku ace sukai" cikin sauri Lamiɗo yace "Zanyi anma fa se in state ɗinda zamuna kaiwa akwai Bauchi aciki" yanda Lamido yayi maganar seda yabama Abdulmalik dariya,yace "Kaikuma Ina ruwanka da state dinda za'aje so far as zakasamu gumin ka?" Ɗan Sosa kai Lamiɗo yayi sannan yace "bazaka gane bane Abdulmalik. Kaidai kawai katambaya min inba'a ɗauki waɗanda zasuna zuwa can ɗinba Zanyi aikin" Abdulmalik yace "toh shikenan zantambaya maka innakoma gida insha Allahu sannan dukyanda mukayi dasu zankiraka infada maka" Lamiɗo yace "a'a karka kirani wayana tasamu matsala acikin wayar Umma nasa simcard ɗina, I'll just come here tomorrow morning inyaso se inji yanda kukayi" Abdulmalik yace "toshikenan Allah yakaimu goben" daganan sukayi sallama Lamiɗo yawuce majalisa ranshi fes yana addu'ar Allah dai yasa adace.

QADRWhere stories live. Discover now