Page Seven - Saying Goodbye

347 34 3
                                    

🌹_*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Seven- Saying Goodbye*

Agarin Babban buli Lamiɗo yace ma mai akori kura yasaukemu inda nina wuce gida shikuma yaje masallaci yayi sallar la'asar sannan yaciro report book ɗin Auwal danashi yashiga copying abubuwan dasukayi a field yau kamar yanda yayi jiya.

Asanda su Uztaz suka iso harya gama copying yaje ciro kanyar dazaiyi guzurinta suka haɗu a hanya. kokulashi basuyiba sukayi wucewarsu shiko dariya yadingayi ƙasa ƙasa yana faɗin "ku kuka sanidai. baku obeyers ba?kuje kuyitayi" seda yajirasu sukayi sallah sannan suka karbi fura da nonon dasukace a ajiye musu nima naɗebo mishi anagida da aka kawo ɗazu dabananan nakai mishi sannan suka wuce bakin hanya dankomawa masaukinsu.

Toh haka muka cigaba da fita field kullum taredasu harmuka kare wannan satin aka shiga wani. kuma kullum inzan fita sena nema mana abunda zamuci acan nida Lamiɗo hakanan indai akazo inda dole hawan dutsi za'ayi to nidashi samun guri zamuyi muzauna su suhau suyi abunda zasuyi susauko mutafi. kuma kullum dayanma inmuntashi komawa gida Lamiɗo yadinga sawa atsaya a hanya ina hutawa kenan. hakanan duk randa Allah yahaɗamu da mai machine ko akori kura tose Lamiɗo ya tarar mana su yaroƙa mana lift zuwa garin Babban Buli nidashi inda su Uztaz kesamo mu anan suhadu da Lamiɗo suwuce gida. Tun su Uztaz na korafi harsuka daina,Hafiz ma yakoma yashiga binmu danshima cewa yayi yagaji gaskiya,kuma yana ganin bati bazai bariba Allah ya gani. Abubuwan dasuke faruwa a field din kuwa Allah yayi yawa dasu, faɗansu dakuma yanda suke samun sabani a tsakaninsu sukuma dawo su shirya bakaramin dariya yake baniba,gashi Lamiɗo is full of jokes shiyasa innacemuku field work ɗinnan is boring to nayi karya,akwai gajiyakam anma inada mai magance min ita sabida tsaye yake akaina,baya taba bari in wahala. Akwai ranar da mukaje wani quadrant naji Auwal da Uztaz nata emphasising minerals ajjejefe sunyi yawa agurin yakamata su faɗa ma Malamansu. da mamaki na natambayi Lamiɗo dake rikeda hannuna nace "meyesa za'a faɗama Malamanku minerals sunyi yawa anan gurin?" take yacemin "Wayasan musune Ƴar birni anma bari intambaya maki Auwal" daganan yadubi Auwal yace "Auwal Ƴar birni na tambaya. wai miyesa zaku faɗa ma samudawan malamankucan minerals sunyi yawa anan" Auwal yayi dariya yace "Malaman namune samudawan Lamiɗo?" Lamiɗo yace "Yoh ba samudawan bane? mutanen da basu da aiki secin teba da doya inba'a haɗa su da samudawa ba dame za'a haɗasu fisabillahi?" Hafiz dake dariya yace "Ga Mr ogwechuku abayanka" aidasauri Lamiɗo yajuya a rikice dariya suka saki dukansu Auwal nafaɗin "ashema duk iskancinka kana tsoronsu" Lamiɗo dake sauke ajiyar zuciyar danbakaramin razana yayiba,yama manta a field suke babuyanda za'ayi yaga malamansu yace "Sufa zasu bani certificate Auwal. dole inruɗe,wallahi duk iskancina Ina tsoronsu danjahilaine,yanzu sesu hana hanani gama wahalalliyar course ɗinsunnan" sudai su Uztaz inbanda dariya babu abunda sukema Lamiɗo kafin daga karshe Auwal yamin bayank yace duk inda kikaga akwai traces na minerals sosai toh it indicate that somewhere around akwai precious stone shiyasa muka damu mufaɗa ma Malamanmu.

Cikeda gamsuwa nace "kamar sumeyene precious stones ɗin?" Auwal dariya yayi yace "something like diamond,gold dadai sauransu" wara idanu nayi cikeda excitement nace "yanzu kenan zamu iyasamun Gold anan?" Auwal yace "probably, somewhere around dukda ba'asan exact gurinba and it can be something else ba gold ɗinba". yace "kuma ko ansamu location ɗin ma cireshi abune mai wahala Ƴar birni,injinan daza'ayi anfani dasu dakuma yanda za'ayi ba abune mesaukiba mumadakikaji muna maganar kawai don Jin daɗin bakinmune, because munsan komun faɗama baza'a ɗau maganar da mahimmanci ba because we're in Nigeria and here in Nigeria mutanenmu basu ɗaukan valuable magana da mahimmanci. basusan darajar da Allah yamanaba,basusan baiwa da albarkatun kasan da Allah yabamu ba. kawai rashin sanin yanda zamuyi dashine yakedamun mu,rashin sanin ciwon kanmu ke damunmu, selfishness darashin kishin kasarmu ke damun mu dakuma rashin leaders na ƙwarai and above all curruption yamana yawa. Malamin mu bejimannanba yake faɗa mana turawa sunzo suncire gold anan Nigeria,hargurin yakaimu yanuna mana,a Inda suka cire gold din anan sukabar injinan dasukayi amfani dashi tsabar sunsan sunsamu abunda yafi wannan injinan daraja,ninkin baninki. we always say munsamu yancin kanmu but somehow, somewhere still mutanennan suna rulling ɗinmu batareda munsani ba" gyada kaina nayi inajin bayanin Auwal kafin daga karshe yayi dariya yace "but we're hoping for a change Ƴar birni. may be wataran kedakanki kikawomana injin cire gold kiciromana kodan su Gogode susamu" yakarashe maganar playfully.

QADRWhere stories live. Discover now