Page Thirty Seven

45 2 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Seven

Bayan fitan Safiya se Aunty tadubeni cikeda tausaya wa tace "Babu dai wanda kika samu matsala dashi a makarantar da aka barki koh?" Gyaɗa matakai nayi ahankali. Tace "toh yanzun kinci abinci ne?" nanma gyaɗa matakai nayi sannan nace "Yaya Fahad yasayamana ahanya" Aunty jinjinakai tayi sannan tace "toh tashi kikai class bag ɗin naki cikin ɗaki sekiyi sallah ki kwanta ki huta Koh?" gyaɗa mata kai nayi sannan natashi ahankali ayayinda nasaci kallon Yaya Fahad dake danne danne cikin wayarsa kafin najuya nayi shigewata ɗaki inaji inama abunnan yatsaya hakanan basai anyi furthering dinshiba because the more su Sadiya will be purnished the more nima nasan zansha wahala arayuwa,toh anma inada bakin cewa kar a hukunta su ɗinne? Banidashi shiyasa nayi tafiyana kamar yanda Auntyn ta umarceni hakanan inaji Sadiya tanata sheshekar kuka anan tsakiyar parlourn

***
Safiya nabarin parlourn Auntyn kuwa straight parlourn Ummi tawuce. Aisha,Zaheera dasu Mariya kaɗai tasamu a parlourn dankuwa Ummi bata jima da shiga yin sallar isha'i ba dan saida takalli wani Series sannan tashiga ciki kuma tunda tashiga bata sake fitowa ba. Su Zaheera naganin Safiya tashigo parlourn daman suka tashi sukayo kanta dan Sule daman yakai musu gulmar yaga sanda Fahad da Rukayya suka shigo dazu suka kuma zo sukaji kukan Sadiya wanda hakan yatada musu hankali yasa su fara tunanin ko asirin su ne ya tonu.

Aisha ne takalli Safiya sannan tace "Ya naganki wani iri? Meyake faruwa newai?" Safiya tace "Hmm atakaice dai yau kashin mu yabushe kawai shine abunda zan iya ce muku. Kuzo Yaya Fahad na kiranmu duka yana parlourn Aunty" a kidime Zaheera tace "Akan wani dalili yakeneman mu?" Safiya tace "sabida yasamu labarin abunda muka ma Rukayya. infact shiyaje ya ɗauko ta ma,tare suka dawo badajimawannan ba" seta juya cikin sauri tana faɗin "nidai kunga tafiyata,zanje inkira Yaya Zunnurain mu haɗu acan parlourn Auntyn kawai kada Yaya Fahad yazo yaci ubana yace nabata masa lokaci" daganan Safiya tayi ficewarta a ɗakin jiki na rawa. Kallon juna Zaheera da Aisha sukayi akidime kafin Zaheera tayi sauri tashige ɗakin Ummi tana kwala mata kira.

Bin bayanta Aishan ma tayi, Ummi dayanzu ta'idar da sallahn tana ƙoƙarin ninke sallaya ahassale takalli Zaheera da Aisha dasuka shigo ɗakin kamar wanda aka jefosu daga sama sannan tace "Wai wannan uban kiran na menene haka sekace bakusan inda nakeba?" Zaheera a rude tace "Ummi Yaya Fahad ne ke kiranmu" harara Ummi ta watsa mata dukda tayi mamakin wai yau Fahad ke kiran kannensa anmaseta ɓoye mamakin nata tace "Daya kirakun kuma se akayi Yaya? Kuje mana kukasani ko tsaraba yayi muku" Aisha kamar zata fashe da kuka tace "Ba tsaraba yamana ba Ummi. Cin ubanmu zaiyi wallahi" wani kallo Ummin tamata sannan tace "Cin ubanku kuma? Akan wani dalili?" Aisha tace "Sabida yasamu labarin anbaro Rukayya a makaranta. Shida kanshi yaje yaɗauko ta" Baki sake Ummi tace "Wace Rukayyan kuma?" dandai ita hartagama lissafinta akan Rukayya, gaba-daya a tunaninta tunda taga dare yayi Rukayya  batadawo ba toh tawuce Babban buli ne Koh Giyaɗe wanda har hakan yasa tariga tagama kissima abunda zata faɗama Kawu Sani inya dawo baisamu Rukayyan agida ba.

Aisha tace "Wallahi kuwa Ummi! Yanzunnan ya Aiko Safiya takiramu kuma daman bayan shiganki ɗaki yin sallah bada jimawa ba Sule yace mana yaga sanda suka shigo ranshi a bace kuma muna parlour ma munji kukan Sadiya daman" Ummi setace "toh shidin waya faɗa mishi?" Zaheera kamar zatayi kuka tace "Oho" se Aisha tace "Hmmmm yawuce Rukayyan ne taje tasamu Uncle Adam tasanar dashi shikuma ya kirashi yafaɗa masa tunda daman abokin sa ne" Zaheera cikin sauri tace "I doubt zata faɗama wani kobakiga irin yanda take tsronmu baneba?" Aisha tace "toh ya akayi yasani inba faɗa ɗin tayiba?" Se Zaheera tace "sede in sun haɗu ne kotaje karban kuɗin mota kan anmantata a school shine shikuma ya kira Yaya Fahad ɗin ya faɗa masa" Aisha tace "toh ya akayi yasan meyafaru har yake neman mu?" Tsaki Zaheera tayi danta fara Jin haushin silly questions ɗin Aishan sannan tace "koma wayene yafaɗa mishi shouldn't matter right now. Damuwar mu ayanzu shine musan yanda zamuyi mufidda kanmu acikin maganarnan" wani kallo Aisha tama Zaheera sannan tace "Ah tunanin ki zamu iya fidda kanmu ne wancan matsoraciyar tana gurin? Ai wallahi tonama kowa asiri Sadiya zatayi I'm very sure about that" cije lebe Zaheera tayi sannan tadubi Ummi with pity face tace "Ummi yanzu yazamuyi don Allah" tsaki Ummi tasaki sannan tace "Yakoh zakuyi dayawuce kuzuba ma sarautar Allah ido. Koh da atunaninku barin shi zanyi ya hukunta ku inyi shiru batareda nace komai ba?toh wallahi yayi karya yakwana da yunwa. Yadaki kannen nasa wannan damuwarsa ne anma kukam bazai taɓa ku inkyaleshi akan wata shegiya Rukayya ba" take se su Zaheera suka fara murmushin Jin daɗi,Ummi tace "Kuyi gaba ganinan biyoku a baya kada ma kuwani tada hankalinku" Ummi ta karashe Maganar ayayinda ta ajiye sallayar datagama ninkewa akan bedside ɗinta sannan tashiga ƙoƙarin cire hijabin dake jikinta zata sauya kayanta.

QADRWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu