Page Twenty Six

38 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Twenty Six

Kallon envelope ɗin hannuna Kawu Sani yayi sannan yace "menene acikin envelope ɗin kuma Daughter?" ahankali nace "credentials ɗina ne naɗauka bansani ba ko za'a bukata" jinjina kai yayi sannan yace "kinko yi dabara abunda nazo intuna miki kenan" murmushi kawaii nayi batareda nace komai ba.

Yace "Toh mikomin credentials ɗin ingani" mika masa nayi inagani yabuɗe yaciro su duka yana duddubawa harya gama yamaidomin da abuna sannan yadubi Yaya Fahad yace "Son se tafiya koh?" Ahankali Yaya Fahad yace "Eh Abba" Kawu Sani yace "toh muje kukama hanya nima se in wuce office" tashi Yaya Fahad yayi yana faɗin "toh" kafin yanufi kofar sashin Aunty Yana faɗin "Bari muyi sallama da Aunty"

Bejima cikin sashin Auntyn ba segasu sunfito tare da Aunty.

Gaidata nayi ta amsa min fuska sake sannan tagaida Kawu Sani inda daganan kuma muka fice dukanmu. harjikin mota Yaya Salim ya rakamu shida Kawu Sani Aunty kuma daman tundaga bakin kofar fita a main parlour tayimana Allah yakiyaye hanya takoma cikin gida abinta.

Bayan munshiga motar tada injin motar Yaya Fahad yayi still Kawu Sani da Yaya Salim na tsaye daga gaban motan suna kallonmu.

Yaya Salim ganin Yaya Fahad yatada motar seyadubeni yace "Toh Ruky Best of luck kinji?" Yar murmushi nasaki sannan nace "thank you" Kawu Sani yace "makesure you compose yourself kafin kishiga test din kinji Daughter?" Shima gyada mishi kai nayi sannan nace "toh" kafin yadubi Yaya Fahad yace "Fahad Drive carefully karkaje kana gudu a babban titi fah" Yaya Fahad yace "insha Allah Abba" sannan yayi reverse aka bude masa gate mukabar gida. gaban wani restaurant dake nan cikin garin Bauchi Yaya Fahad yayi parking sannan yadubeni yace "Sauko kibiyoni" zuciyata fal take da mamakinsa anma sena boye mamakina nakama handle ɗin motan nabude nafita danshi already haryafice a motar jirana yakeyi infita yasama motar key.

Shine agaba inabinshi abaya har muka Shiga restaurant ɗin. Table me kujeru guda biyu yasamu yaja kujera ɗaya yazauna inda yanuna min ɗayan yace in zauna nima. ɗaya daga cikin ma aikatan restaurant dince tazo tayi mana sannu dazuwa sannan tashiga tambayar Yaya Fahad abunda za'a kawo mana.

Seyace mata meda me suke dashi on ground cikin sauri tashiga lissafamasa harta gama nidai idanuna nakan table ɗin feeling uncomfortable.

Kawai sejinayi ya jefomin tambaya "what would you like to eat?" dagowa nayi cikin sauri don son in tabbatar dani yake kobada ni ba senaga ni ɗin yake kallo. Maida kaina nayi kasa dasauri sannan ahankali nace "Anything"
Kawai senaji shima yanace ma waitress ɗin "just bring anything for her" murmushi waitress ɗin tayi sannan tadawo da dubanta gareni tace "toh akawo miki chips, plantain and egg?" Gyaɗa mata kai kawai nayi sannan nace "toh" murmushi tayi sannan tasake maida dubanta ga Yaya Fahad tace "what of you Sir? meza'a kawo maka?" Yaya Fahad yace "No I'm okay kikawo Mata natan dai"

Waitress ɗin nakawo min abincin senaga yatashi yafita wanda hakan yasa naci abincina comfortably dukda Ina mamakin ya akayi Yaya Fahad yasan banci abinci ba tundadai ai yasan anyi breakfast agida kuma harkai musu nasu nayi sashin su.

Wata zuciyar kuma seta shiga rayamin kodai Kawu Sani ne yabashi kuɗi yace mutsaya a hanya inci abinci? Take Kuma ɗaya part ɗin zuciyartawa tayi dismissing wannan tunanin danbaiyi making sense bama kwata kwata. Dama adawowa ne yasayamin abinci se ince wannan Kawu Sanin ne yace yasaya min anma ayanzu kam nasan a assumption ɗin Kawu Sani nayi breakfast agida tunda basanin abubuwan da iyalin sa keyimin yayi ba. Hakadai nakarasa cinye abincina still Ina mamakin canzawar Yaya Fahad ɗin. I just can't believe it tunda banasuba ganin yanama kowa haka ba anma sena bar abuna acikina ni kaɗai. Bansan ya akayi yasan nagama cin abincin ba kawai seganinshi nayi yashigo entrance ɗin restaurant ɗin bayan nakai last spoon ɗin abinci bakina.

QADRWhere stories live. Discover now