Page Thirty Eight

61 2 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Eight

Amma da mamakina se naga yasake karban cup ɗin ahannuna yacigaba da daurayewa. Yana murmushin danasan baikai har zuciba yace "Nasan kina tsoro kada Ummi tafito taga Ina tayaki aiki ne kokuma su Mariya su fito suganmu suje su faɗa Mata Koh? but believe me Ummi bazata fito yanzuba sabida yau ba girkinta baneba. Su Mariya Kuma incase insun fito I know how to handle them" Jin abunda yace ɗin senaji nazama speechless gaba ɗaya, senaji jikina yayi sanyi saka makon irin tune dayayi using wurin furta kalaman sa. It clearly shows shima bahakan yakesoba.

Sekawai na sunkuya na ɗauki wani cup nafara wankewa ahankali batareda nace masa komai ba. Haka mukayi shiru harna kusan mintiuna goma,inbanda karan kwanuka bbu abunda kakeji. Can senaji ya ƙira sunana.

Ahankali yace "Rukayya" ɗagowa nayi na kalleshi sannan nace "Na'am Yaya Salim" ajiye plate ɗinda yagama daurayewa yayi cikin basket ɗinda muke kifa kwanukan sannan yamaida attention ɗinsa kaina baki ɗaya,cikin sanyayyar murya yace "I'll like to apologise to you on my Mom and siblings behalf akan abunda yafaru jiya. I know you're going through alot because of them anma inason kisan cewa they're not that bad you might think they're. They just've wrong impression about you and your Mother from the very beginning shiyasa" yasauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya sannan yace "Kiyi hakuri dan Allah. Kikuma cigaba da hakuri for insha Allah wataran komi zaizama tarihi" murmushin dayafi kuka ciwo nasakarmasa sannan nace "Bakomai Yaya Salim karka damu. I'm absolutely fine" dukda kuwa araina Ina tunanin yaushe ne ranar dazai zo har komai ya wuce gaba ɗaya,har su Yaya Zaheera sudaina yimin irin tsanar dasukeyi min yanzu? Har komai dayake faruwa acikin Rayuwata yanzu yazama tarihi? Yaushe ne wannan ranar zatazo?

Seya kawar da zancen tahanyar yimin hira yana bani labarin jami'a dakuma irin wahalhalun dasukesha wurin lecturers ɗinsu har muka gama wanke wanken Wanda alokacin kuma har gari yafara haske sosai. kwandon wanke wanken yaɗaukamin yakaimin kitchen ayayinda nabishi da tukwanen dana wanke ahannuna inayi mishi sannu da aiki. Yace "Kimadaina yimin sannu Rukayya! In akwai wanda yakamata ama sannu aikene. Nida ɗauraya kawai nike tayaki" Ƴar dariya nayi sannan nace "toh ai shima aikine" Yaya Salim yace "Aganin kiba anma nidai aguna bawani aikin azo agani baneba" Ƴar dariya nasakeyi sannan nace "Toh na gode" senaga yabata rai lokaci guda,yace "Godiyar ta menene kuma bayan yanzu nagama cewa niba aikin komai namikiba" sekawai na girgizakai in desbelief Ina murmushi batareda nakuma cewa komaiba.

Yananan tsaye kaina harnagama jera tukwanen dana shigo dasu a ma'ajiyinsu sannan natashi tsaye Ina faɗin "Alhamdulillah nagama" Yana kallona yace "Seme zakiyi next?" sincerely nace "Sharan backyard zanyi kafin afara maganar girki" cikin sigar zolaya yace "toh muje intayaki" wara idanuna nayi sannan nace "Medin!!!" yanda nayi maganar a firgice ba ƙaramin dariya yabashiba. Dakyar ya tsagaita dariyar tasa yana faɗin "Rukayya Uwar tsoro. I was just kidding dannasan konace zantayaki dagasken ma bayarda zakiyiba" cikin sauri nace "Bazan yarda bakam Yaya Salim. wanke wanken ma danba yanda na'iya ne yasa nabarka katayani so kayi tafiyarka kaje ka huta. It's still early in the morning" still yana dariya yace "Auuu yanzu kuma korata kikeyi kenan?" Cikin sauri nace "A'a ba korarka nikeyiba nagadai kamar kagajine" seyayi murmushi ayayinda yajuya yana fita a kitchen ɗin yace "Toh Ruky ayi shara lafiya tunda kinki intayaki" Murmushi namasa ayayinda nabishi da idanu Ina faɗin "A huta gajiya".

Seda ya kulemin dagani sannan najuya naɗauki tsintsiyar dazanyi shara dashi nafita a kitchen ɗin nafara sharan Ina mamakin ya akayi su Safiya basu ɗauki hali irinna Kawu Sani dasu Yaya Salim ba. Ina cikin sharan backyard ɗin kuwa sega Mai aikin Aunty tazota, gaisawa mukayi inda take tambayana yaushe muka dawo daga makaranta nace mata jiya.

QADRTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon