Page Eight - Shocking news

338 33 9
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Eight - Shocking News*

***

Baffa iddi yace "toshikenan se akaitan kawai" Gogode tace "hakan kam dazaifi. Ko gobe dasafema seka haɗa ta dasu Rahane sukaita taga yanayin jikinnashi daganan ma kaga su Rahanen swa dubashi. Baffa yace "toh Allah yakaimu" kafin yatashi yakoma kofarsu.

Tun a daren ranan bayan nadawo daga dandali Gogode tacemin gobe intashi da sassafe zamuje cikin gari taredasu Yadikko Rahane, daɗi kamar nayi yaya dankuwa tunda tafaɗa min nasama raina indai nashiga garin Bauchi gobe babu abunda zaihana ni zuwa gida ingano Baba kafin mudawo dukda kuwa ɗazu nama Gogode alƙawarin zama se hutuna yaƙare anma ai yanzu ita tace inshirya zamuje gari,kuma indai har zanje gari mezai hanani zuwa gurin Baba? tunda dalili yakaini. Tun adaren naciro kayan dazan saka na ajiyeshi saman akwatin Gogode kafin nakwanta bacci. washegari dawuri natashi nashirya kamar yanda su Yadikko Rahane suka tashi dawuri suma,takwas nayi mukatafi batareda nasan takamaimai inda zamujeba tsabar zumuɗin ance za'aje gari dani,nidai damuwana inje Inga Baba ba inda zasuje bane damuwata. Seda naga taxi driver na ƙoƙarin shiga general hospital na Bauchi sannan nafara tunanin "Daman asibiti zamuje? Toh waye babu lafiya?" and then my heart starts beating without a reason. Sonake intambaya waye babu lafiya anma bakina yayi nauyi,nauyin da nikaina bazan iyacewa ga dalilinsaba.

Ahakadai mai taxi ɗin yasamu guri yayi parking su Yadikko Rahane suka biyashi kuɗinshi sannan muka fara takawa cikin harabar asibitin. Mutane natakai kawo wanda kallo ɗaya zakayima kowannensu kasan ba daɗi yakawosu asibitin ba,jinyace takawosu danwasu zakaga tafiyarma daƙyar sukeyinta,wasu kuma turasu akema akan sickbay,wasu kuma gashidai suna tafiyar lafiya Lau amma kallo ɗaya zakayi musu kagane basuda isasshen lafiya. kawai kwantar dasune ciwon baiyiba,wasu kumada taimakon yan uwansu masu lafiya suke iya takawa. naga mata masu ciki,naga masu ciwon kafa,naga masu zazzabi,naga waɗanda sukayi accident(hatsari) dadai sauransu kuma duk seda suka bani tausayin dan by just a mere look zakagane how much they're suffering dukdama wasu sunfi wasu shan wahala and even though I was very young,deep down in my heart I sympathize with them. It was my first time going to the hospital dannidai bantaba rashin lafiyar datasa aka kwantar daniba,inkaga nayi zazzabi toh baiwuce kwana daya biyuba na warke sekuma mura dayazamo usual ciwona barinma lokacin sanyi,inada pneumonia dukdama baya tashi sosai sabida Baba namatukar ƙoƙari gurin ganin nakiyaye duk abubuwan dazai iyasawa yatashi.

Tafiya mukadinga yi harmuka isa wani ward,gaida security ɗin gurin Yadikko Deejah tayi sannan tashiga tambayarshi ɗakin da ake ajiye marasa lafiya awannan ward ɗin,kwatance yamana sannan muka mishi godiya muka shige cikin ward ɗin,a kofar dakin daya kwatanta mana muka tsaya. Yadikko Rahane tafara shiga sannan Yadikko Deejah tabi bayanta seni dake biye dasu abaya, ɗakine babba dayakeda tsayi sosai ga kuma gadaje sunfi dayawa,tundaga bakin kofa naga nake ganin duka gadajen ɗakin are all occupied by male patients wanda hakan yasa bugun zuciyana yatsananta batareda nasan dalili ba.

A gaban wani gado naga su Yaddiko Rahane sun tsaya wanda hakan yasani tsayawan nima. kallon Kawu Hassan autan mazan gidansu Baba nayi zaune kan wata yar gujera wanda hakan yasani mamakin meyakawo shi asibiti kuma?waye ba Lafiya? sede tunma kafin nasamu damar tambayar wadanda nikejin zasubani amsa yanda yadace naji Yadikko Rahane nafaɗin "Mallam Umaru yajikin?" and if I'm right that's the only name da mutanen Babban buli ke ƙiran mahaifina dashi,afirgice na ƙarasa kusa dasu,nature Yadikko Rahane gefe ina kallon mutumin dake kwance kan sickbay ɗin helplessly. Babana ne,the only Father that everyone could ever ask for,mahaifina abunsona,mahaifina abun alfaharina,mahaifina danake ganin babu kamarshi acikin rayuta. Shine kwance agadon asibiti duk yatsomare,yayi wani iri,kallo ɗaya nayi mashi nasan yana tsananin shan wahala.

QADRWhere stories live. Discover now