Page Twenty Eight

34 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Twenty Eight

A previous page nayi mistake! Namanta kwata kwata a weekend aka kaisu Rukayya makaranta and I make the page as if it's during week days. Hope you guys will bear with me? Kudauka kawaicikin sati aka kaisu😁 afuwan please.

Tsugunawa nayi gaban kayan nawa ahankali ina tattabasu sannan nace "wannan ai kayana ne" Aziza dake tsaye akaina tace "Ina daga Admin kuka bayar ashigo muku dashi hostel?" gyaɗa matakai nayi ahankali setace "toh Ina na ɗayar cousin sister ɗin naki? Koh hostel ɗinku ba ɗaya baneba" ahankali nacema Aziza "hostel ɗinmu ɗayane da'ita" cikeda curiosity tace "toh Ina aka kai nata kayan? kodai sunzo sun ɗauka itada Yayunkune?" tashi nayi daga tsugunen danake agaban kayana sannan nakalli Aziza nace "Nima bansani ba Aziza" wani wawan ajiyan zuciya tasauke dukda kuwa tana da tarin tambayoyin datake son tayimin abakinta seta riƙe su aranta tace "toh mushiga ciki muyi tambaya kilan musamu wani da yasan ɗakin da ɗayar Yayarkun take tunda kince itama a hostel ɗinnan take" cewa nayi "toh" sannan muka shiga haraban hostel ɗin.

Wata muka hango zaune akan dakalin dazai sadaka da ɗakunan dake bari gabar dake cikin hostel ɗin kuma daga gani zatayi kusan sa'anni da Yaya Zaheera dan haka semuka ƙarasa inda take zaune muka gaisheta sannan Aziza tashiga tambayarta ko tasan Yaya Zaheera awannan hostel ɗin dayake tun ahanyarmu nashigowa hostel ɗin tatambayeni sunan Yaya Zaheera nafada mata.

Se mukayi sa'a tasanta,tambayar number ɗakin Yaya Zalihan mukayi ta faɗa mana sannan mukayi mata godiya muka tafi.

Ɗakunan dake wannan block ɗin mukayita bi harmuka isa number ɗakin da yarinyar can tabamu sannan mukayi sallama muka shiga. Ɗakin cike yakeda occupants ɗinsa hakanan kowa yana harkokin gabansa da alama ma basumasan da shigowar namu ɗakin ba. Rarraba idanu nashigayi kozanga su Yaya Zaheera anma babu su babu labarinsu.

Aziza ne ta ƙarasa jikin bunk ɗinda ke kusa da inda muke tsaye sannan tayima yarinyar dake kwance kan bunk ɗin sallama suka gaisa sannan tace mata Sister Zaheera muke nema.

Buɗan bakin Yarinyar cewa tayi "Cab Sister Zaheeran nan gaskiya rabona da'ita tun safe anma dai bansani ba kota dawo hostel bayan antashi daga classes dan nima yanzunnan shigowana ɗakin" seta dubi bunk mate ɗinta dake zaune kan up bunk tana ninke inner wears ɗinta tace "Zainab nikam Yaya Zaheera tadawo hostel ne tunbayan da aka tashi daga classes?" Zainab tace "Eh sunzo itada kannenta taɗauki kayanda zatasa na tafiya evening prep sannan suka tafi. wai acan hostel ɗinsu Safiya zata shirya yau" dawo da dubanta tayi garemu sannan tace "toh kunji batanan sede in kudawo anjima" godiya mukayi masu dukansu sannan muka fice a ɗakin.

Aziza dubana tayi sannan tace "Yanzu yaza'ayi? zamu ɗebo kayanki mukawo ɗakin nan ki ajiye kafin sudawo su rakaki abaki ɗakin ne komuje kawai abaki ɗakin kikai kayanki can?" cikin sauri nace "kinsan House captain ɗin namu ne?" girgizamin kai tayi alaman a'a sannan tace "bansanta ba anma damun tambaya za'a faɗa mana ɗakinta ai" senace "toh muje abani ɗakin kawai" dankuwa banason inkawo kayana in ajiye anasu ɗakin yazama abun magana tunda na leka ko'ina a ɗakin banga kayan Sadiya bama.

Komawa ɗakin su Yaya Zaheera Aziza tayi takuma tambayar yanmatan ɗazu ɗakin house captain ɗinmu nan suka faɗa mata sannan muka tafi. bamusha wahalar samun house captain ɗinba dan muna shiga ɗakin damu kayi tambaya aka nuna mana ita. Ƙarasawa mukayi inda take muka gaida ta sannan nace mata ɗaki nazo tabani, I'm a new student.

Wani long note taɗauko ta ajiye kan locker ɗinta sannan tashiga dube dube harta iso wani page kafin tamikamin littafin tamin pointing inda zancika details ɗina sannan tabani pen nacike cikin lokaci kankani namaida mata littafin ta rufe ta ajiye sannan tafito daga corner ɗinta tana faɗin "kubiyoni a baya" room seven takaini tayi introducing ɗina ga yan ɗakin sannan tanuna min bunk ɗinda zan ɗaura katifana akai kafin tayi tafiyar ta.

QADRWhere stories live. Discover now