Page Thirty Nine

47 2 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Nine

Brush da maclean naɗauko a ɗaki sannan nafito naɗauki buta naje nadibo ruwa acikinsa daga randa sannan nazo naɗauki kujera nanufi can kusa da hanyar banɗaki na tsuguna ina brush. Ina cikin yin Brush ɗin Indo tafito daga ɗakin Gogode tana kwala Ƙiran sunana. amsawa nayi ayayinda nujaya Ina kallonta,ɗauke take da kwarya a hannunta wanda inada tabbacin tagama shirin tafiya surfen hatsine.

Dubana tayi sannan tace "Zakije surfene?" girgiza matakaina nayi ahankali ina yatsina fuska danni gaba ɗaya yaujina nake banajin daɗi sabida gobe zankoma cikin gari. Cemin tayi "toh shikenan" sannan tayimin sallama tayi tafiyarta. Bayan nagama brush wanke fuska na nayi nakoma ɗaki gurin Gogode.
Da mamaki tadubeni tace "Daman baki ta fi surfen ba?" gyaɗa matakai nayi ahankali sannan nace "Eh Gogode. Yaukuma naji banason zuwa" jinjinakai tayi sannan tace "Niko harnake cewa dagacan seki wuce gurin Innan Kwaidum tayi miki kitso tunda gobe zakikoma cikin gari" batarai nayi take sannan cikin sauri nace "Bazanyi kitso ba" Gogode tace "Kunada masu kitso a unguwarku kenan?" Senace Mata "Eh". Gaba-daya su Gogode basusan halin danake ciki agidan Kawu Sani ba,infact a tunaninsu ana treating ɗina very well agidan tunda Buba ya taɓa zuwa mungaisa bannuna masa komaiba gakuma dazanzo anhadoni dasu Yaya Zunnurain sunkawoni. Dukda bayan tafiyarsu Gogode tasha tambayana ko akwai matsala anma kullum amsar babu nakebata sabida banason abunda zaitada Mata hankali,most especially awannan shekarun nata. Ranar har azahar babu inda naje ina kwance adaki.

Ƴan gidan kowa yajini shiru seya leko ɗakin Gogoden yana tambaya ko lafiyata Lau inda zance musu kalau nike,kawai dai yauɗin banjin fitowan ne. Wuraren ukun yanma Ina kwance a ɗaki ni kaɗai Ina karanta wani story book danataho dashi acikin kayana naji andoka sallama a sashin Gogode ɗin. Tsayawa nayi da karatun ayayinda na tsurama kofar ɗakin nata idanu dukda akwai labule dan in tabbatar sallamar akayi dagaske kokuma imagination ɗinane. Wani sallamar aka kuma yi wanda Jin kamar nasan me muryar yasani saurin tashi nazauna ina murmushi kamar wanda akamin kyautar kujerar makka,sallaman daya kumayi akaro na ukune yasani fitowa daga kan gadon kaina ko dankwali babu nafito dagudu Ina faɗin "Waalaikumus Salam" ayayinda na daga labulen kofar. Yaya Lamiɗo nahango tsaye jikin katangar data raba sashin Gogode danaso Yaddiko Rahane.

Wani irin lallausar murmushi yasaki sakamakon ganina dayayi sannan cikin sigar zolaya yace "Yakika tsaya kamar statue? Toh ki karaso mugaisa mana. Koh baki farin ciki da ganina ne inkoma" yayi maganar ayayinda yake kokarin juyawa wai zai koma,ai cikin sauri nasaki labulen Gogode nanufesa da ɗan gudu gudu Ina faɗin "Wallahi inayi Yaya Lamiɗo.  mamakin ganinka ne yasani tsayawa guri guda" Yana murmushi tajuyo gareni sannan yace "Miye abun mamakin? Didn't I promise you that I'll surely come and visit you inkukayi hutu?" tura Ƴar karamar bakina nayi gaba sannan nace "You promised to come and danazo ancemin you came last week bananan shiyasa nayi tunanin bazaka sake dawowa ba" seyasa hannu cikin lallausar gashina yadanyi stroking ɗinsa yana fadin "Ai indai banganki ba toh I won't rest until I get to see you" washare bakinayi cikeda Jin daɗi sannan nace "Really?" gyaɗa min kai yayi yana murmushi,senace "Kana  nufin dakazo wannan satin baka sameni ba wani sati ma zaka dawo?" Gyaɗa min kai yakumayi still looking at me while smiling.

Cikeda Jin daɗi nace "What if har hutu ya ƙare banzo Bafah?" Seyasa hannayensa a kirji yayi folding yana kallona,yace "then I'll surely go to your Uncle's House inganki kafin kuyi resuming" bansan sanda nafara blushing ba,nace "Inkuma ba'a barka kashiga ba fah?" Boldly yace "I'll surely find the way no matter how insha Allah" senace "But why will you go to this length kawai danka ganni? Ai akwai komawa makaranta and you promise to always visit lokacin visiting days" Lamiɗo cire hannayensa yayi a kirjinsa ayayinda yamaida su cikin aljihun wandonsa yasauke wani sanyayyar ajiyar zuciya sannan playfully yace "Yarinyar nan you can ask questions for Africa" Ƴar dariya nayi sannan nayi pouting bakina nace "Nidai kafaɗa min don Allah" Kama hannuna yayi muka nufi rumfar Gogode ayayinda yake faɗin "because I've so much to discuss with you dayake ta damuna for months now while kekuma gudun muyi maganar ma kikeyi and secondly nayi miki alkawarin zuwa inganki so I'll make sure nacika wannan alkawarin because I don't like breaking promises,most especially indai akanki ne Nanaaa!" Yakarashe maganar slowly ayayinda yasaki hannuna,yaja kujera yazauna yana faɗin "Tunda ba'acemin inzauna ba ba inzauna dakaina dannagaji da tsayuwa" Ƴar dariya nayi sannan naja ɗayan kujerar nazauna nima Ina faɗin "Ina wuni?" Yaya Lamiɗo yace "Lafiya Lau Ƴar Birni" tura bakina nayi gaba sannan nace "Wai bazaka manta sunan nanba" Ƴar dariya yayi sannan yace "Akan wani dalili zan manta? Kokin tashi daga Ƴar birni kinkoma Ƴar kauyene?" Tura baki nayi gaba sannan nace "Ni ba Ƴar kauye baceba" dariya yayi sosai wannan karan sannan yace "Toh kuma sekice kar acemiki Ƴar Birni?" fuska tsuke nace "Nidai banaso,haka ranar ma kafaɗa agaban Aziza. Allah yataimakeni hankalinta baya kan sunan sosai dayanzu tamaida min suna yakoma Ƴar birni" wannan karan Lamido dariya yake sosai harda riƙe ciki, dakyar ya tsagaita sannan yace "Kice dana kwabsa" hararanshi nayi playfully inabata Rai.

QADRWhere stories live. Discover now