Page Forty Four

34 4 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Forty Four

***
Yaya Lamido ranar Sunday dinda yace zaidawo yadawo makarantar tamu kuma adaren ranar seda yanemeni yabani tsarabana,tsarabar da seda aka kawomin nakowa kamar yanda na bukata. Yaya Auwal ma yabani nashi playfully yana fadin "gashi dukdama dai tsarabar dole akasani nayi" nidai dariya kawai nayi sannan nayi masa godiya.

Tun matsalar damuka samu dashi mukayi resolving bamu sake samun wani matsalar ba. infact wani irin sabo da shakuwa ne yasake shiga tsakaninmu,babu wanda baisan Yaya Lamido Yayana bane awannan lokacin dan kullum semun hadu,either during break kokuma after night prep kafin muwuce hostel hakanan babu ruwanshi gaban kowa nunawa yakeyi I'm very special to him wanda hakan yasa ko seniors shakkun tabani sukeyi kosakani aiki. Barinma wadanda suka samu labarin abunda akayima su Yaya Aisha. masu crushing akanshi kuwa shisshigemin sukeyi suna Jana ajiki anma duk abanza dan gabadaya baswa gabanshi.

Akwai lokacin da wata Sister Kaltum ta dameni kan insama Mata number shi dannikaina ban rike ba tunda ba wayane daniba banikuma da wanda zaibani wayarsa inkira sa koda ina gidane,a Babban buline kawai zan iya kira da wayan Buba shima kuma already yanada number wayartasa saved acikin wayarsa,Inna tashi kira kawai searching sunanshi zanyi inkira. Alokacin da Sister Kaltum tadameni da batun Yaya lamido cemata nayi yanada budurwa anma dukda haka seta dage sena samo mata number nasa.

Yakan bani wayarsa inyi game inmun hadu,most especially during the weekend inyashigo  dadare anma banason in dauki contact dinshi without his knowledge shiyasa nayi deciding in tambayar mata anawa wautan.

Yaya Lamido baya taba shiga abunda zaiyi affecting karatuna. Kamar during prep inyazo sede kawai mugaisa yawuce hakanan during classes ma inba sako zaibani ba banma cika ganinsa ba. Zuwa dayakeyi during break kullum farkon zuwanshi makarantar tun bayan abunda yahada munnan yazo yadaina zuwa. In kaganshi during break a ajinmu toh ranar munyi class dashine Tuesdays and Fridays kenan. In yagama mana lesson toseya jira munyi hira kafin yatafi,sauran ranaku kuma sede muhadu after evening prep ko night prep kokuma insuke on duty na zuwa hall muhadu in an tashi ko kafin ashiga.

Yau Wednesday kuma anatashi daga night prep nasabi jakana nafita a ajinmu kasancewar nasan Yaya Lamido nacan gurin masallaci yana jirana. Sonake inje inbashi sakon Sister Kaltum kamar yanda nayi mata alkawari ranar shiyasa ma bantsaya jiran Aziza ba,nace tasamoni acan kawai semu wuce hostel tare.

Yana ganin nakusa isowa gunshi Ina murmushi shima yataho muka hadu a hanya,yace "Nana murmushin yau dinnan na menene haka?" Yar dariya nayi sannan nace "Babu" Yaya Lamido yamin kallo a darare sannan yace "Anya kuwa? Anya bawani abu muka samu ba" Ina dariya nace "Allah bakomai Yaya lamido" Yaya lamido yace "Toh ya karatu? Hope you had a good time reading?" Gyada masakai nayi ahankali sannan nace "Yau banga kazo patrol night prep ba" dan yatsina fuska yayi sannan yace "wallahi kuwa. I'm having headache tun rana yanzuma nafito ne sabida banason kizo kiyita jirana" sad face nayi take Jin yace bayida lafiya sannan ahankali nace "Sorry. Allah ubangiji yakara sauki,Aida kayi zamanka" playfully yace "Na'isa? Inyi kwanciyana gobe inji ance gaki a gadon asibiti?" Tura baki nayi gaba tareda sakin dariya sannan nace "Banasooo Yaya Lamido" yana dariyar shima yace "Aigaskiya nafada. I don't want to cause you any problem Kuma"....

Jinjinakai nayi cikeda gamsuwa sannan nace "toh ka wuce kawai nima zantafi Hostel" folding hannayensa yayi a kirji sannan yashiga girgizamin kai kamar wani karamin yaro, sincerely yace "Bangaji da hira dakeba. Innatafi yanzu I'll miss you soon,gwanda mucigaba da hirar lokaci yasake tafiya ynda I'll get to see you tomorrow dawuri" blushing nayi sannan nace "Toh inkaje kakira Aunty Maimunatu kuyi hira you'll not miss me" sake girgizamin kai yayi sannan yace "aike zanyi missing ba itaba,so Kona kirata tunanin ki bazai bar rainaba" tura baki nayi gaba sannan nace "toh yaza'ayi?" yayi Yar dariya yace "mucigaba da tsayuwa for a little longer tunda students ma basu gama tafiya hostel ba yet" Gyada masakai nayi ahankali sannan nanufi dakalin masallacin nazauna Ina fadin "muzauna anan kada kagaji da tsayuwa" zuwa yayi yajona ni muka zauna sannan mukayi shiru nadan wasu dakiku babu maicewa komai,se wulgawan student dasuke tafiya damukeyi. Mu muna ganinsu anma su inba mutum ya lura ba bazai hangomuba.

QADRWhere stories live. Discover now