Page Eighteen

56 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Eighteen

***
Lamiɗo da Hafiz isan yanma sukayi Gombe. Napep ɗaya suka shigo wanda seda akayi droping Hafiz sannan aka karasa da Lamiɗo bakin masarautar.

Koda ya'isa gidansu sama sama suka gaisa da kannen nasa sannan yawuce ɗakinsa. Umma kam dama baisameta a gida ba,wai tashiga gidan Galadima dubiya karamin Ɗan su ya karya kafarsa awurin wasan kwallo.

Se dare suka samu zama dukansu inda Umma ta tambayi Lamiɗo koya samu yaje gidansu Rukayyan inda atake yasanar da'ita komai dakuma abubuwan dasuka faru a Bauchin.

Umma cikeda tausayin Rukayya tace "Allah Sarki ashe rashin lafiyar mahaifinta ne yahanata kiranka" Lamiɗo yace "Eh wallahi Umma"

Umma tace "Toh Allah yabashi lafiya yasa kaffara ne. Inadai kasamu ka karbi number tasa?kaga in ankwan biyu seka kira kaji yanayin jikin nasa" Umma takarashe maganar ayayinda tamaida hankalinta baki ɗaya kan Lamiɗon.

Lamiɗo ahankali yace "ban karba ba Umma" cikeda mamaki Umma tace "Akan wani dalili?" Lamiɗo yace "Babantan was in a state dabazai yuyu ince yabani numbersa ba" Umma tace "Toh ai shikenan. Kama kanka" Lamiɗo dai murmushi kawai yayi hakanan har ranshi yanason yacema Umma seya koma sake duba mahaifin Rukayyan zai karbi number anma yasan this's not the right time. Ba lallai ta amince ba dan haka yaja bakinshi yayi shiru with a plan daga baya zaisan yanda zaiyi yayi approaching ɗinta da maganar.

Salma dake kwance jikin Umma tana kallon Hausa film tashiga tambayar Lamiɗo koyabama Rukayya ribom ɗinda tabayar akai mata.

Wara idanu yayi danshi seda tayi maganar ma sannan yatuna tabashi wani abu wai shi sako sannan yace "wallahi namanta Salma. I put it inside my pocket shadaf namanta inbata. Anma kiyi hakuri next time insha Allahu innaje zanbata" Lamiɗo yakarashe maganar ayayinda yake satan kallon Umma and her expression alone gives him an answer.

***
Washegari Koda Rukayya tafarka thesame thing tayi tayi dayake Allah yataimaka Kawu Sani da Fahad na gurin sunzo dubata atake Kawu Sanin yatura Fahad yaje yanemo likita.

Fahad gyaɗa kai yayi sannan yafice a ɗakin don yin abunda mahaifin nasa yasakashi. Baijima da fitaba segashi sundawo da likitan. ƙarasawa jikin gadon likitan yayi sannan yashiga tambayarsu abunda Rukayyan tayi tayi, Gwaggo Suwaiba ne tamishi bayanin yanda sukayi da Nurse ɗinda ta duba Rukayya a daren jiya dakuma alluran baccin datayi mata.

Gyaɗa kai likitan yayi cikeda gamsuwa,sannan yashiga taɓa pulse ɗin Rukayyan,yayi wasu gwaje gwajen sa sannan yayi rubutu jikin paper yamika ma Kawu Sani dake tsaye kusada shi yace "kusamo waɗannan prescriptions ɗin semuyi mata amfani dasu muga abunda Allah zaiyi"

Kawu Sani karban papern yayi yana fadin "thank you Doctor" likitan yace "bakomai kawai in ankawo kuyimin magana Ina office ɗina" Kawu Sani yace "toh" ayayinda likitan yafice a ɗakin. kallon bangaren da Fahad ke tsaye yayi folding hannunsa a kirji yana kallon karfen gadon da Rukayya ke kwance Kawu Sani yayi sannan yace "Fahad" cikin sauri Fahad yaɗago dakansa yana kallon mahaifin nasa sannan ahankali yace "Na'am Abba" Kawu Sani yashiga miƙa masa Papern hannunsa yace "Get this drugs from the pharmacy now please" Fahad karasawa yayi inda mahaifin nasa yake sannan yasaka hannu yakarbi papern yana faɗin "toh" sannan yajuya yafita dasauri.

Sanda Fahad yadawo straight office ɗin likitan yajeshi,yanuna masa prescriptions ɗinda yasiyo sannan suka nufi ɗakin da aka kwantar da Rukayyan tare. Nan likitan yakarasa dakansa yamata alluran sannan yadubi Kawu Sani yace "zuwa bakwai na dare zata tashi insha Allahu daganan kuma se afara bata drugs ɗin though I'll come back myself and see her condition kafin mufara administering mata drugs ɗin" Kawu Sani yace "toh shikenan. Allah yakaimu lokacin Doctor" Doctor yace "Amin" kafin yamusu sallama yafita.

QADRWhere stories live. Discover now