Page Fifteen

420 34 4
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Fifteen*

***
Yau tun sassafe Lamiɗo yagama shirinsa cikin shaddarshi milk colour daya sha wanki da guga, Umma ne ta ɗin kamai a sallar azumin daya wucennan shiyasa kallo ɗaya zakayi ma kayan kasan cewa sabone barekuma Lamiɗo da daman baicika sa manyan kayaba,kananun kayane daily dress code ɗinsa inkaga ya saka shadda toh tabbas Friday ne Kuma yauɗinma ya kasance ranar Friday and yasan kilan sallan juma'a na'iya samunsu a can inda zasuje ko ahanyar dawowa shiyasa yayi shirin sa na juma'a baki ɗaya.

Karfe bakwai da yan mintuna Lamiɗo yafito daga ɗakinshi. a parlour yasamu Jidda nata aikin goge gogen Tv da TV stand da alama dai tagama tsaftace parlourn ne takoma kanyin goge goge Kuma.

Tana kallonshi tace "Ina kwana Yaya? badai harka shirya tafiyanba?" Lamiɗo karasowa yayi inda Jiddan ke gogo gogen yace "lafiya Lau Jiddodo. Ina Umma? Yanzu zantafi kinsan yau zamuje mudawo bamwason muyi dare bakwai mukayi zamubar garinnan gashi har bakwai ɗinma ta gota niban bar gida ba. nasan Hafiz nacan yana jirana" Umma dake kitchen tunda tajiyo muryar jidda nama Lamiɗo magana tayi sauri taɗauki cup tashiga zuba masa koko acikin cup ɗin ayayinda tadubi Basma dake harkar suyan kosai tace "kwashe mishi kosan cikin kaskon nan a plate kibani inhaɗa masa da kunun inkayi masa yasamu yaci kafin yatafi inyaso ke kicigaba da ɗana kosan" Basma tace "Toh Umma" ayayinda takarasa inda kwando yake taɗauki plate tashiga kwashe masa kosan.

Sanda kwashewa Umma tariga ta gama haɗa kunun ita take jira daman,sa hannu Umma tayi takarbi plate ɗin sannan tafice a kitchen ɗin. harlokacin Lamiɗo na tsaye kusa da Jidda yana ganin Umma tafito yace "yauwa Umma. Ina kwana?" Umma tace "lafiya Lau Lamiɗo" ayayinda tashiga mikamai cup ɗin koko da plate din kosai tace "karbi kazauna kaci karin kumallon ka ne" Lamiɗo da kamar bazai karba ba sabida bawani yunwa yakejiba anma sanin cewa Umman bazataji daɗi ba yasashi karban abincin yakoma kusa da ɗaya daga cikin Tum tum ɗin parlourn yazauna yana faɗin "Thank you Ummana" Umma tace "Hafiz ɗin gida zaibiyo maka kuwuce ko kai zaka bimashi?" Lamiɗo dahar yafara cin kosai da Kunun yace "nizan bi masa. munyi karfe bakwai zamu haɗu dashi fah gashi har lokaci yawuce" Umma tanufi hanyar ɗakinta tana fadin "sekaci dawuri kada yayita zaman jiranka" Lamiɗo yace "toh Umma".

Umma bata jima dashiga ɗakinta ba ta tafito hannunta rikeda kuɗi,zuwa tayi tazauna gaban Lamiɗo dake cin abinci tamika mishi some portion of the money tace "gawannan kuɗin motarkune kaida Hafiz na zuwa da dawowa" Lamiɗo karba yayi yana murmushi yace "nagode Umma" sauran kuɗin dayake ɗari biyar biyar guda biyu tasake miƙamai yakarba yana sakeyi yimata godiya tace "wannan Kuma kasayama kakarta goro kona ɗari biyar ne sauran canjin kuma kasayama yaran gidan sweet kakai musu tsaraba babu daɗi kujeku hannu rabbana sannan kasake yimasu godiyan kula dakai dasukayi tayi sanda ciwon kafarshi yatashi,kace musu mungode Allah yasaka da alkhairi"

Lamiɗo yace "toh Umma nagode. insha Allah zanyi yanda kikace" seda yacinye kosai da Kunun tas sannan yatashi yaɗauki plate da cup ɗin yakai kitchen yana cema Umma da tun ɗazu takoma kitchen suka cigaba da aiki shizai tafi.

Umma tace "Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya. ka gaggaishesu kuma kutaso dawuri Lamiɗo kada dare yayi muku ahanya" Lamiɗo yace "insha Allahu Umma" harbakin kofar parlour suka rakashi sunayi masa Allah yakare. Salma dayanzu fitowarta daga ɗaki tashinta daga bacci kenan ganin ana raka Lamiɗon yasa cikin sauri takira sunanshi tace "Yaya Lamiɗo" Lamiɗo juyowa yayi yana kallonta dasauri takaraso inda yake tace "Wai har zaka tafi wurin Kawartawa ne?" dariya yayi sannan ya gyaɗa matakai ahankali.

Sa hannu tayi cikin hular dake kanta taciro ruffle ɗinda ta kama gashinta dashi takamo hannunshi tasaka ruffle ɗin a tafin hannunshi tana faɗin "Gashi kakai mata kace mata inagaisheta and I accept her friendship shiyasa naɗauki favorite ruffle ɗina nabaka kabata" Lamiɗo tsugunawa yayi yayi kissing forehead ɗin Salma yana lumshe idanu sannan yace "Ƴar birni na godiya Autar Umma" Jidda da Basma dai basuce komaiba don duk cikinsu basu ɗauki maganar Rukayya dayakeyi musu da mahimmanci ba kamar yanda Umma ma bata ɗauki maganar da mahimmancin ba dukda kuwa irin damuwa dasu da Lamiɗon yanuna Rukayya nayi tana kuma son suzama yayunta. Umma kuwa takyeleshine yayi yanda yaga dama ne tunda yanuna nacinsa akan tafiyar, yaɗage seyaje.

QADRWhere stories live. Discover now