Page Twenty Seven

40 3 0
                                    


🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Twenty Seven

Harara Ummi ta watsamin bayan Yaya Salim yafita daga parlourn sannan tanunani da yatsa daya tace "wallahi inbaki tattare kayanki kinfice a parlourn nan ba koh yanzunnan zanzo in tattaka ki dagake har kayan naki! Munafukar yarinya kawai" jikina na ɓari nacire kan iron ɗin daga jikin socket sannan nakashe socket ɗin nashiga tattara kayana cikin sauri. Sanda nagama tattare kayan hartayi shigewarta ciki wanda hakan yasani zuwa na ajiye akwatin kusa da akwatina na kayan gida dankuwa banason shiga ɗakin su Yaya Siyama suyimin korafin natashe su suna bacci tunda dare yayi sosai. kitchen nawuce nayi kwanciyana kamar yanda nasaba kullum. Najima ina tunane tunane kafin nasamu bacci yaɗauke ni.

Washegari dasafe seda nagama duka ayyukana dasuka zamemin daily routine ɗina sannan nashiga wanka dayake Yaya Fahad cemana yayi karfe goman safe zamu kama hanyar Azare. Aikuwa karfe goma dot segashi yashigo sashin namu. Nidaman a main parlour yasameni zaune nagama shirina danhaka seya wuce ciki don ƙiran Sadiya. Baiwani Jima acikiba sega su sunfito shida Yaya Siyama niqi niqi da kayan Sadiya ayayinda Sadiyan ke biye dasu abaya bayanta goye da class bag ɗinta.

Ganin sunfito yasa nima natashi naɗauki class bag ɗina na goya abayana sannan na daga akwatina nashiga ja nabisu abaya.

Afilin gidan mukayi kicibis da Yaya Salim karban akwati na yayi cikin sauri yana faɗin "Rukayya akwatinnan yayi miki nauyi ai ina zaki iya jansa?" murmushi kawai nayi sannan nace "Ina kwana Yaya Salim" shima murmushin yakeyi yace "lafiya Lau Rukyn Abba! Yau sai kwanan gadon karfe koh?" gyaɗa masakai kawai nayi ayayinda muka ƙarasa jikin motar yasaka akwatin nawa cikin boot kafin yajada baya yana karkaɗe hannayensa. Matrasses dinmu, blanket, pillow dadai sauransu daman tunjiya akasaka su acikin mota.

Yaya Fahad dake riƙe da murfin boot ɗinne yadubeni sannan yace "iya kacin kayan naki kenan?" gyaɗa masakai nayi ahankali sannan yarufe boot ɗin motar yanufi drivers seat batareda yakuma bi takaina ba. Dafari harda Ghana must go Aunty tasayamin kamar na Sadiya anma raguwar provision ɗina a ƴan kwanakinnan yasa akwatin yayi ƙasa kuma dayake akwatin babbane sekawai nasaka komai da komaina aciki dukdama na nade Ghana must go ɗin nasaka shi cikin akwatin shima.
Books ɗina kuwa duk suna cikin katuwar classbag ɗinda ke goye a bayana. Yaya Salim ne yabuɗe min gidan baya na motar yace inshiga ayayinda Sadiya tun tuni tashige gidan gaba suna yar hirarrakinsu tareda Yaya Siyama dake tsaye kusa da windown gidan gaban wanda duk shawarwarine yake bata gameda rayuwar boarding. bayan yagama mata se Yahadamu duka yayi mana nasa nasihan kafin yakoma ta barin da Yaya Fahad yake zaune yace "Toh Bro yanzu Inka tafi se yaushe Kuma?" murmushi Yaya Fahad yayi sannan ahankali yace "Only God knows" Yar dariya Yaya Salim yayi sannan yace "Wai me inyamurennan suke bakane? Anya Inna gama nawa karatun bazanje nan inyi service ba nima kuwa? Inje Inga yanayin rayuwarsu?" Murmushi Yaya Fahad yyi sannan yace "Kaje wallahi! befi experience ba ai and you'll get to know different people from different cultures in your country" jinjina kai Yaya Salim yayi sannan yace "You're right! baridai musamu mu gurgurda mugama jami'ar semuga abunda Allah zaiyi" Yaya Fahad yace "Allah yabaku sa'a" Yaya Salim yace "Amin" sannan yadan sauke ajiyar zuciya yace "anmadai bayau zaka wuce Imo bakoh?"  Yaya Fahad yace "Yeah zankwana a Abuja gidan Uncle Bakoh (Yayan Aunty) inyaso gobe dasafe se inkama hanya" Yaya Salim yace "okay fine! Safe journey Bro" Yaya Fahad yace "Thank you" sannan Yaya Salim yazuro dakansa cikin motar sosai yana dubanmu yace "Ƴan makaranta kundai ji abubuwan dana faɗa muku ko?" gyaɗa kai mukayi duka atare sannan yace "toh Allah yabada sa'a" mukace "Amin" kafin yaja da baya inda Yaya Fahad yaja motar mukabar harabar gidan.

Su Mariya basusamu sunyi sallama da Sadiya ba sabida suna islamiya muka tafi dankuwa bazance hardaniba tunda magana ta arziki bata taɓa haɗani dasu ba sede na cin fuska da cin mutunci. Sadiyar ma bawani jituwa sukeyi ba dansau tari nakanji suna faɗa anma dai hakan bawai yana nufin baswa son junansu baneba! Yes they argue and fight but that doesn't change the love they have for each other. Makaranta tare suke zuwa kuma har faɗa Sadiyan takan shigar musu idan sunnemo tsokanan wasu.

QADRWhere stories live. Discover now