Page Ten

362 40 1
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert* @wattpad

*Page Ten*

Kallona Yaya Salim yayi cikeda tausayawa kumanasan kobai faɗa ba nasan yayi regretting kawoni cikin gidansu,haka yafice a parlourn jiki sanyaye yarage dagani se Zunnurain. ayanzu narage sautin kukan nawa anma still anajin yanda nake shesheka Ina shikewa.
Yaya Zunurain dake kallon wakar da akeyi a Zeeaflam kafin afara film cikeda takaicin sautin kukana dake hanasa Jin abunda akeyi cikin tsawa yace "Ke!!!!" afirgice naɗago Ina kallonsa yace "Wallahi inbaki bar kukan nanba zanyi wulli dake waje intattakaki inyaso kije ki jona mahaifin naki a asibiti kuyita jinya kinajina?" irin seriousness ɗinda ke kan fuskarsa dakuma yanda yake zaremin idanu yasani saurin hadiye kukana,nadaina sauke ajiyar zuciyar danakeyi ɗinma ina gyaɗa masakai ahankali. Batunyau nasan waye Yaya Zunnurain ba,shike bin bayan Yaya Salim,he's 18years kuma yana ss3 yanzu haka. shi mutum ne meshegen neman tsokana hakanan yanada mugunta sosai dankuwa zakiga zaizauna yayi wasa da yaro anma kana kawo masa wargi zai daga hannu yabugi banza shiyasa ma kowa shakkunsa yakeyi agidan. duk wasan daza'ayi toh bawanda zaiyi gigin yimasa raini. bansake wani kwakkwaran motsiba bare ƙara harsu Yaya Salim suka dawo wanda alokacinne kuma Ummi tafito daga ɗaki cikin shirinta na alfarma tace "yauwa kundawo koh?" Yaya Salim dako zama bekai gayiba yace "Eh mundawo Ummi" Ummi tadubi su Zaheera daketa cin magani suna kallon TV already har anyi nisa a film ɗinda sukeson kallon Ummi tace "Aikuma bazama zakuyiba tashi zakuyi kuje kuhaɗa alalan ku kullah seku hura wuta biyu, ɗaya na kunu ɗaya kuma na alalan asamu yadafu kowa yaci tunda gashi har azahar takusa" Zaheera kaman zatayi kuka tace "Ummi wainikam bazakuma Abba maganar neman me aikin baneba dan Allah?mun wahala abaya yanzuma kuma da hutu yazo semuyita wahala fisabilillahi?" Ummi tatabe baki sannan tace "yace bayaso inkuma mundage toh shibada yawun bakinshiba kuma bazai biyaba tunda gamu da dirka dirkan yan mata agida bazai biya wasu daga waje suzo suna mana aikiba" Ummi tacigaba "ni tsabar takaicima bankuma cemasa komaiba, Safiya (kishiyar Ummi) cema tayi kokarin nuna mishi aida kun koma makaranta babu masu tayamu aikin,lokacin hutune kawai kukenan tunda boarding kuke shine yace "Da dabaisamu kudinba ya mukeyi?Ina hakuri mukeyi muyi aikin dakanmu? toyanzu ma mucigaba dayi kamar da. so inma zaku cirema ranku maganar me aiki gwandama kucire ma ranku kuzage damtse kuyi aiki dandai ni ba aiki nakeyiba bare kusa ran zannemi me aiki tadingayimin Ina biyanta dangwanda Safiya tana business,ita zata iya" Aisha tace "anmadai Abba bekyauta manaba gaskiya. shikenan mutum bazai huta da wahalaba?" Zunnurain yace "mu tun muna yara muke ganin jarabawa,yakasa kulawa damu yanda yadace, kuɗinsa duk a karatunsa yake karewa amma haka muka dinga hakuri. yanzu kuma damuka sa ran jin daɗin ma yana neman yayi depriving ɗinmu" Ummi tace "iyi anma ai ya'iya yima dangin baɗale,tunda gashi shine biyan kuɗin ɗakin Umar,shine biyan kuɗin magani,shine biyan dukwasu expenses da ake kashewa a asibitin nan" Zunnurai yace "hmmm. Bayan shikuma Uncle Umar ɗin sanda yake da lafiyar ma ko tsinke betaba kawomana gidannan ba" wani irin tsawa Yaya Salim yama Zunnurain yace "will you keep quiet my friend! kaidin harnawa kake dazaka tsaya kana questioning decision na Abba? harnawa kake dazaka tsaya kana korafi dan Abba yana taimakon Yan uwansa?" Ummi daranta yagama baci ganin yanda yaya salim ɗin ke hayayyakowa harkaman zaidaki Zunnurain ɗin yasata cewa "Auuu dan ya faɗi gaskiya shine zaka wani hayayyako masa? toh ai bashi kaɗai yayi magana ba hardani. nima seka hayayyakomin. Kuma ai ba karya mukayi ba,begama cida na gidaba yaje yake gwaninta ana waje" Yaya Salim raibace yace "Ummi you're putting this children on the wrong track. menene Abba bayayi agidannan?abincine baitaba kawowa daidai gwargwadoba ko school fees ɗinmu ne baitaba biya akan kariba? Kokuma other needs ɗinmu daya zamanto necessary ne baitaba yimana ba?" Ummi tasaki baki tana kallonshi tace "au yanzukuma wa'azi zakayi min kenan?" Yaya Salim yace "ba wa'azi bane Umma aigaskiyane" Ummi tace "toh bana son gaskiyan karike abunka. Kuma katashi muje ka ajiyeni agidan Hajiya larai. yau sunan yarta tahaihu tana taro acan" Yaya Salim daranshi haryanzu bace yake yace "Ummi Abba fah najiranmu a asibiti zai wuce office" Ummi tace "Dan haka sebaza amin nawa uzurin ba kenan koh?" Yaya Salim yace "nibahaka nake nufiba Ummi" Ummi tace "toh muje maza" kallona yayi yace "tashi mutafi Rukayya, Inna ajiyeta semu wuce asibitin" cikin sauri Ummi tace "baka isaba kuma. wallahi bazan shiga mota ɗaya da kazamar yarinyarnan ba,kalan tasa kamshin turaren danakeyi ya dumulmuye yakoma warin jikinta. Muje inka ajiyeni kadawo ka ɗauke ta,indan tanine ma kabata kuɗi tahau adaidaita" Yaya Salim kasa cewa komai yayi se fita dayayi a parlourn ayayinda Ummi tajuyo tana kallon su Zaheera daharlokacin basu tashi sunje sun fara aikin alalar datasasu ba tace "Wai nikam bazaku tashi kuje kuyi aikin dana saka ku baneba?" Aisha tashiga noƙe noƙe tana bata rai tace "zamu tashidai Ummi" Ummi tace "toh kutashi yanzunnan kufita kuyi. Ke Zaheerea ki bubbuga waken kafin kigama Aisha tahura icce a ɗaura kunu seku hada alalan ku kukkula aleda shima a ɗaura awuta"

QADRजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें