Page Forty Nine

39 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Forty Nine

Tundaga wannan ranar natashi daga Kanwar Yaya Lamido nakoma budurwar sa a FGC Azare dankuwa bayajin kunyar fada akoina cewa ni budurwarsa ce yanzu hakanan bayajin kunyar nuna irin sonda yakemin gaban kowa. Dayawa sukan tambayeni "Daman Sir Isma'il Cousin Brother dinki ne" dankuwa dayawan su sunyi tunanin blood Brother nane,da maganar soyayyar tamu ta bazu ne yasa sukemin irin wannan tambayar. nidai amsar guda dayace nake basu kullum "Eh". In class yakeyi mana toh rabi da kwatan Period dinshi se ankira sunana acikin koyarwan,komai yayi bayani seya kalleni yace "Nanaana kingane?" In example ze bayar Kuma akwai suna aciki toh tabbas "Naanaa" zaisaka. In laifin daya daga cikin Yan ajinmu tayi mishi kosukayi mishi sukaje bada hakuri ko neman tafiya toh maganar dayace "kuje kusamu Nanaa intace tayafe nima nayafe muku" harta seniors dinmu da yake musu koyarwa insukayi laifi abundayake musu kenan...

Sukam cewa yake suje sunemo ni indai naje yakalli kyakyawar fuskata ma anwuce gun. wataran kuma yace sesun sani nayi mishi letter me dadi sannan za'a yafe musu. Haka zakaga seniors sunzo ajinmu nemana helter skelter,tun Ina Jin dar dar akan zasuna ramawa a hostel harma nazo nasaki jikina dankuwa Yaya Lamido acikin wasa da raha yakeyi musu abun wanda suma suka dauki hakan amatsayin wasan,hakan seyasa nasakeyin mutane suke kuma yina hakanan wadanda basu sanni ada bama sukazo suka sanni.

Shakuwa sosaine yashiga tsakanina da Yaya Lamido dankuwa zaman mintuna kalilan zakayi dani kagane cewa shidin wani mutum ne dayake da matukar muhimmanci acikin rayuwata. bana maganar minti biyar batareda nasako sunanshi cikin hirar tawaba,sau tari idan na damu Aziza da hirar Yaya Lamido dayake nafi zama da'ita fiyeda kowa takancemin "Rukayya nikam narasa keda Yaya Lamido waye yafi son wani acikin ku" and I'll just laugh,se ince "we love each other equally,yanda nikesonshi haka shima yake Sona".

Abunda yake Kara burge mutane da soyayyata da Yaya Lamido,Koda sau daya tarayyana dashi baitaba affecting karatuna ba dankuwa he's never for once yashiga abunda zaishiga karatuna. Yanda muka saba haduwa ada toh haka yanzunma yake,kawaidai sunan relationship dinne tacanza wanda shima shikadai yacanza ma abun suna tundadai hirar damukeyi dinma duk kamar nada dinne,yakandai rubuta min love letters masu dadi yabani once in a blue moon haka yakuma ce inyi masa reply wanda senaci uwar wuya sannan nakesamu inhado kalamai inyi inbashi,wataran kuma Aziza nike roka tarubutamin dayake she's good at writing love massages haka. He's always been my source of motivation,Koda yaushe karamin karfin gwiwa yakeyi akan karatuna badai yaragemin ba hakanan shima yana maida hankali sosai wurin fita field dinsu every weekend.

Ayanzu yakoyi abubuwa da dama akan field work,sau tari inyadawo daga field yanamin hira seyace "Nanaa ashe haka Geology takeda dadi bantaba saniba?" dariya nakeyi duk sanda naji yafadi haka se ince "Haba Yaya Lamido?" Seyace "Wallahi kuwa,it's very interesting and worth learning. the more I get to know about It the more it makes me want to explore the world" senayi dariya ince "Nima shi zan karanta toh Yaya Lamido. Kaga semuyi exploring world din tare" yana dariya yace "Wayaga Mr and Mrs Geologists. sure indai kinaso I'll surely workhard inkaiki geological terrains masu kyau around the globe" bakaramin dadi kalaman sa sukayi min ba,cikin farin ciki nace "Allah yabaka iko" Yaya Lamido yace "Amin".

Kusan zamu fara exams Yaya Lamido yazomin da wata magana data kadamin yan hanjina,ranar Friday ne dadare bayan muntaso daga night prep bazan taba mantawa ba. As usual abakin masallaci nasameshi zaune yana jirana bayan mungaisa yabani ledar tsiren dayamin alkawarin siyomin tunda rana inda muka dan shiga taba hira. bamu wani Jima tsayeba sega kiran Umma yashigo wayarsa,dagawa yayi suka gaisa, yabani muka gaisa da'ita harma muka danyi hira dasu Yaya Jidda kafin namayar masa da wayar suka cigaba da magana da Umma. Magana sukeyi akan kawo tambayar aure dakuma kaiwa dukda bangane inda maganar tasu ta dosaba I was very excited to know auren wanene za'ayi acikin kannensa lokacin don haka seda nabari yagama wayar sannan najeshi da tambayar "auren wa za'ayi Yaya Lamido?" rike haba yayi a lokacin in a playful manner yace "toh iya gulma har kunnenki yajiyomiki maganar me mukeyi?" Yar dariya nayi sannan natura baki gaba cikin sigar shagwaba nace "Eh mana, kafada min auren waye za'ayi don Allah?" Yaya Lamido girgiza Kai yayi yana murmushi sannan yace "toh da surprise nayi niyar yimiiki inmunkoma gida anma tunda kin damu infada barina fada Miki" cikeda kaguwa nace "fadamin toh" dan furzar da iska Yaya Lamido yayi sannan yace "Maganar auren Basma danawa mukeyi da Umma" Sanda yakira sunan Yaya Basma I was more than happy,infact I wanted to dance anma kanshi dayakira immediately after sunan Yaya Basman ne makes me curious, Cikeda mamaki nace "Aurenka Kuma?" Dankuwa nadauka mistake yayi gurin fada anma da mamakina seya gyadamin kai,with a smile on his face yace "Koh bazaki aureni bane Nanaaa?" cikin sauri nace "Zan aureke mana Yaya anma ai maganar danaji kunayi da Umma kwanannan fah za'ayi auren,nikuma I'm still young,makaranta nikeyi Sena Gama zamuyi aure"

QADRWhere stories live. Discover now