Page Twenty Four

45 2 1
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad*

Page Twenty Four

Banɗakin dakenan cikin parlourn nashiga nakama ruwa sannan naɗauro alwala nafito nakoma nan main parlour natada sallah. Har na idar da sallar bantashi daga position ɗinda nakeba addu'o'i nakeyi ma kaina,al'ummar musulmi baki ɗaya dakuma addu'ar Allah yasa Baba is in a better place dankuwa bazanmanta ba akwai ranar dayashigo ɗakina agida yasameni na'idar da sallah Ina addu'a a fili,seyaji ma nidashi nakeyi ma addu'ar shine yazaunar dani yacemin inzanyi addu'a Ina haɗawa da duka al'ummar musulmi baki ɗaya.

I should never pray for myself alone,I should pray for everyone for Allah yafi karban addu'a irin wannan cikin gaggawa.

Kofar ɗakin sashin Aunty naji an buɗe wanda hakan yasani juyawa nakalli direction ɗin gurin senaga ashe Yaya Siyama ce tafito kanta sanye da hijabi sekuma sleeping wears na riga da wando dake jikinta. Haɗa idanu mukayi wanda hakan yasani gaisarda ita batareda na shirya ba.

Nace "Ina kwana Yaya Siyama" ɗauke kanta tayi daga gareni sannan tace "Lafiya" tayi wucewarta. Harta Isa kofar fita ta backdoor sekuma tajuyo takalleni adakile tace "Ke biyoni!" gyaɗa matakai nayi ahankali sannan natashi nabi bayanta.

Sanda nafita backdoor ɗin tana cikin kitchen danhaka nanufi kitchen ɗin nima. Acan cikin store nasameta tana ɗiban Irish potatoe cikin wani try da alamadai pealing ɗinsu za'ayi. Abakin kofar store ɗin natsaya tareda faɗin "Yaya Siyama gani" batareda ta kalleni ba tanuna min wani daro sannan tace "ɗauki rubber nan kije waje akwai tap kitari ruwa rabi seki dawo ki ɗauki wuƙa kijirani a varender ɗin kofar kitchen ɗinnan" cewa nayi "toh" sannan naɗauki wuƙan da tanuna min nafice a kitchen ɗin nayi duk abunda tasakani sannan nazauna zaman jiranta.

Banjima zaune kan varendern ba segata tafito. Dire tray ɗin potatoes ɗin tayi gabana sannan tazauna itama tana faɗin kisaka hannu muyi pealing dankalinnan.

gyaɗa mata kaina nayi ahankali sannan naɗauki wuƙan dana ɗauko a kitchen ɗazu dan itama already tataho da nata. Tunda nake ban taɓa firan dankaliba arayuwata hakanan ban taɓa ganin anayi agabana ba so ban iyaba anma ko karen haukane yacijeni bazan iya buɗan baki incema Yaya Siyama ban iyaba danhaka sekawai naɗauki dankalin ahannuna sannan nashiga kallon yanda take ferewan nima nafarayi ahankali. Sede duk yanda naso Kar inci jikin dankalin seda nadinga ci gakuma wukar tayimin katuwa ahannuna.

Yankewa kuwa seda nayanke hannuna yafi sau biyar anma ko sannu batacemin ba barema insa ran zatace inbari kawai kuma tanaganin sanda nake yankewan dankuwa kowani yankewa nayi sena danyi ƙara Ina washhh Allah na! anma abanza. Ahaka muka gama firar dankalin hannnuna duk tafaɗi sukemin. Ɗaukan daron Dankalin tayi sannan tadubeni tace "jeki haɗa min wuta kafin inwanke dankalinnan" idanuna cikeda kwallah na gyaɗa mata kai dukda shiɗinma ban iyaba sannan tawuce tanufi bakin tap tabarni zaune gurin Ina kallon yanda na yayyanke fingers ɗina.

Sa bayan hannuna nayi nagoge kwallar dasuka zubomin sannan nakalli direction ɗinda murhun yake ayayinda itace,matches da ledoji ke ajiye gefe guda. ƙarasawa nayi kusa da murhun sannan nashiga jera itatuwan ciki kamar yanda naga su Yaddiko Rahane sukeyi in naje hutu a Babban buli. Bayan nagama jera itatuwan sena saka ledoji da fasassun robobi asaman itacen sannan naɗauko ashana nashiga kyartawa dukda kuwa yanda yatsuna ke min radaɗi amma seyaki kamawa.

Matches yafi ashirin na kunna suna mutuwa sabida iskan da akeyi agurin gakuma gari yafara haske daman. Yaya Siyama data gama wanke dankalin ne tadawo taga abunda nakeyi rai bace tace "bakida hankaline kike ta ɓata ashana haka?" Kamar zan saki kuka nace "Inna kunna mutuwa sukeyi" harara ta watsamin sannan cikin tsawa tace "tashi dalllahhhh! daman ansabar miki dajin daɗi Ina zakisan yanda ake kyarta ashana?" Komawa baya nayi dasauri Ina miƙamata kwalin matches ɗin,wabcewa tayi ahannuna sannan tashiga nuna ni da yatsa tace "toh barikiji ingaya miki! nanba gidanku baneba kuma nan ba gurinda zakizo kinawa mutane kasalanci baneba. Inzaki zage ki koyi aiki gwanda kizage kikoya dankuwa babu jakinki a gidan nan kinajinah!" gyaɗa mata kai nayi Ina hayewa sannan tanuna daron dankali tace "sekije kifara yanka dankalin ai kafin inhura wutan" sonake incemata bazan iyaba shima anma ina tsoron outcome don haka shima dena gyaɗa mata kai kawai sannan na ƙarasa inda rubber ɗin Dankalin yake. Inasaka hannuna acikin daron naji wani irin radaɗi ya ziyarceni lokaci guda sakamakon ruwan daya shiga wounds ɗinda ke hannuna. Aibansan sanda nacire hannuna daga cikin ruwan ba Ina kallon Yaya Siyama. Hararar da ta watsamin ne yasani sake maida hannunawana cikin daron batareda nashiryaba.

QADRWhere stories live. Discover now