Page Two - The visitors/Earth enthusiasts

613 42 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert* 💞

*Zeeneert*@wattpad

*Two - The Visitors/ Earth enthusiasts*

Free page

Washegari talata itace ranar dabazan taba mantawa acikin tarihin rayuwata ba. Rana ta goma sha daya ga watan september. ranar da wani namiji bayan mahaifina yashigo cikin rayuwa ta and wannan shine mafarin dukwani abu dake kunshe cikin tarihin rayuwata dake cikeda abubuwan al'ajabi kala kala. Lol,I don't know where you all first meet your soulmate but inna fada muku nawa zakusha dariya.

Daman a al'ardar garin Babban Buli duk safiya yara kaman mu sukan fita karkashin wata bishiyar kuka suyi surfen hatsin da iyayensu zasuyi abinci dashi ranan kafin akai injin nika. Toyau haka ta kasance,ni,Hari, Bulo,Mairo,Kwaidum dakuma Yar kanwar mamana Indo data tashi gaban Gogede duk muna nan karkashin wannan bishiyar kukar harma dawasu Yan matan ana surfe,except ni daban iyaba Indo ce keyimana namu.

Kowa da turmin sa da tabaryarsa yayinda suke surfen atare suna waka cikin yaren fillanci,inkaga yanda suke daga tabaryan atare suna mayarwa cikin turmin sesun baka sha'awa inda nikuma nake zaune kan wani dutsi dabayida tsayi sosai se fadi ina kallonsu ina dariya tareda tayasu yin wakar cikeda nishadi. Bamu ankara ba kawai mukaga Kwaidum ta zare idanu tareda sakin ihun "Gujjjoh!(Barayi!!!)" ta fillanci kafin tasaki tabaryar hannunta taruga aguje tayi hanyar gida,sauran ma dasuka ga mutanen dake tahowan suka kwasa da gudu suna ihun "Gujjo gujjo! Gujjo en(ga bayari ga barayi! ga barayi!)" dafari bakaramin tsorata nayiba nima anma dana juya naga mutanen dasuke kira da barayin sena saki dariya harda kwanciya ina riƙe cikina dankuwa abun da su Harin sukayi bakaramin dariya yabani ba ahaka har waɗanda ake ƙira da barayin suka karaso inda nake,sunkai su takwas wanda duk maza ne se mace daya kyakyawa da'ita dukda kuwa ba musulma baceba.

Dukansu suna sanye da riga da wando na jeans sekuma rigar leda koriya da'akayimata ratsin kalan ruwan toka dake sanye saman T-shirt ɗin kowannensu(Reflective jacket) yayinda kawunansu kesanye da irin hulunan kwanon nan(helmet) danake yawan ganin masu aikin kwalta nasakawa hakanan kafafunsu nasanye da irin canvas din da muke amfani dashi amakaranta duk ranar sports dukdama na kafarsu dana gani yamin kyau alokacin sosai bansani ba kodan suɗin sunsa different colours da designs ne? Inda mukuma a makaranta simple white canvas kawai ake bari musaka.

Dukkaninsu akwai wata igiya dake makale awuyansu wanda igiyan naɗauke da wani farin abu mekaman shape ɗin agogon bango dan harcikin abun akwai rubutu irin wanda nake gani a agogon parlourn gidan mu. kowa nadauke da school bag abayansa sekuma wasunsu dake riƙe da guduma,wani first aid box,wani tape dadai sauransu.

A iya sanina masu sharan titi kowani farkon wata da masu aikin kwalta dakuma masuyi ma yara allurar polio kaɗai nasan suna saka irin waɗannan riga da hulan amma sauran abubuwan danike gani tattare dasu bana tunanin nasansu,first aid box ɗin da nagani hannun ɗaya daga cikinsu ne yasa lokaci guda nayanke shawarar cewa sudin masu allurar polio ne,dariya nakuma saki ina tuno yanda su Hari suka kwasa aguje.

Daya daga cikinsu ne yazo ya tsuguna gabana tareda zubamin idanu yana mamakin yanda nike dariya kamar wata tababbiya yayinda macen dake tareda su tazo tazauna gefena tana sauke ajiyar zuciya inda naji wani daga cikin wadanda ke tsayen yana cemata "Zamafa baikamasu ba they've a long way to go" anma hakan baisa tatashi ba.

Dakyar na tsagaita dariyar danakeyi ganin yanda suka zubamin idanu dukansu, barinma wanda ke tsugune gabana. As soon as danabar dariyar nagaban nawa yace "meya hanaki guduwa? ko ke sharifiyace baki tsoron musace ki?" se kawai nasake kwashewa da dariya inda fararen hakwarana tas suka bayyana cikeda yarinta nace "guduwa kuma? niba baƙauya bace ba ai nasanku" kallona yatsaya yi daga sama har kasa wanda inada tabbacin kayan jikina sun tabbatar masa maganar danayi yanzu donkuwa riga da skirt na English wears da Baba yasayamin kwanakine jikina.

QADRWhere stories live. Discover now