PROLOGUE - A glimpse from the present

2.4K 106 8
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Bismillahir rahmanir rahim. In the name of Allah,the most gracious and the most merciful.

*PROLOGUE _ A glimpse from the present*

APRIL,2018

Dakine madaidaici dake daukeda katuwar katifa shimfide kasa se wardrobe irin na katakonnan dake manne jikin gini ta gefe daya. daga daya bangaren kuma akwatuna ne guda uku inda aka jerasu daya kan daya,daga gefen akwatunan kuwa handouts da notebooks ne jere neatly gwanin ban sha'awa sekuma yar madaidaiciyar madubi da'aka manna da gum jikin bango. tsananin ringing din da wayarta keyi ne yasata tashi daga nannauyar baccin datakeyi hakanan cikin magagin bacci tadaga wayar tana kokarin wartsake idanunta don ganin wanene wannan me shegen kiran kamar wani kayan jaraba,ganin sunan Habiba datayi jikin screen din wayarne yasata tashi zaune kafin ta daga call din cikin sauri ganin kiran yakusa tsinkewa,tunkanma tayi magana taji Habiba daga daya bangaren tana fadin "wai lafiyar ki kuwa Rukayya? Inata kiranki bakya dauka. ina kika jefarda wayartaki ne wai?" hamma budurwar da aka kira Rukayya tasaki tana lumlumshe idanu alamun baccin begama isantaba kafin akasalance tace "Habiba am bacci nikeyi sanda kikayita kira,banmasan kinyita kira ba sabida seyanzu naji ringing din wayar.

Daga daya bangaren cikeda mamaki Habiba tace "bacci fa kikace?" Rukayya tace "Eh bacci nikeyi,akwai laifine aciki? naga yau ba makaranta public holiday ne".

Habiba da haryanzu take cikeda mamaki tace "wai bakiga text dina bane jiya da daddare?" cikeda rashin damuwa Rukayya tace "bangani ba Habiba,nayi bacci dawuri ai" Habiba tace "lallai kam toh wallahi kitashi kishirya kishigo school yanzu yanzunnan muyi submitting assignment din Dr. Isma'il dan yace 10:00am dot yakeson kowa yakawo,dukwanda baizoba kuma bazai karba ba sannan zero zaisaka mai batareda yadamu ba".

Aitunda Habiba ta ambaci Dr. Isma'il Rukayya taji dukwani guntun baccin da yake idanunta sun wartsake,ta dafe kirji tace "nashiga uku, Habiba wallahi banga text dinki ba anma ganinan zuwa kuma dan Allah kujirani muje in group" Habiba tace "kidai yi sauri kizo. Inbakizoba yariga ki zuwa submitting zamuje muyi gamunan zaune duk jiransa mukeyi yazo,kindai san halinshi" daganan Habiba ta kashe wayar dif. Rukayya daketa faman yimata magiyar tadai jirata suje taren taji takatse call din,duban wayar tayi kafin tayi wurgi da'ita kan gado sannan tadubi wall clock din dake manne jikin bangon dakin 9:48am,wani irin dukan uku uku zuciyarta yashigayi,yanzu tayaya zata isa BUK kafin goma?kafin tafita daga layinsu tasamu titin samun abun hawama aikine barekuma inta isa school dinma dole tayi traking zuwa department din wanda shima wani nisanne.

Ganin tsayuwar da takeyidin wani bata lokacin ne yasata karasawa jikin wardrobe dinta tabude tadauko wata doguwar riga ta atamfa tasaka cikin sauri batareda tacire riga da gajeren wandon baccin dake jikinta ba. bandaki tashige cikin sauri ta kuskure bakinta tareda dan watsa ruwa afuskarta sannan tafito tadauko hijabinta tasaka,ta rataya jakarta na makaranta datake da tabbacin assignment din naciki sannan tadauki niqabinta dake kan akwatunan dake jere gurin tatsaya gaban yar karamar mirrorn dake manne jikin bangon dakin tana daurawa.

A parlour tasamu *Sajeed* yaron dabazai wuce shekaru takwas zuwa taraba yana kwance gaban TV yana kallon cartoon tace "Sajeed my boy?" cikin sauri yadago yana kallonta sannan yace "Aunty Ina zakije? bayau ba makaranta ba?" Kaman me shirin sakin kuka tace "Sajeed assignment zanje submitting,be a good boy,banda barna and kazo karufe kofa inna fita sannan dukwanda ya kwankwasa kofar karka bude seka tambaya wayene kaji?" Yace "Toh Mummy" kafin yatashi yabi bayanta don rufe kofar wanda alokacin ita harta fice daga gidan.

Sanda ta'isa bakin titi tasamu abun hawa 9:54am,tabbas duk saurinta tasan bazata isa kafin 10:00am ba,ga nisa,ga hold-ups din garin kano gakuma traking din dazatayi inta isa makarantar ma wani abune. Fatan ta daya Allah yasa shi malamin karya isa makarantar dawuri.

QADRWhere stories live. Discover now