Page Forty Two

38 4 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Forty Two

Yana shigowa bezarce ko Ina ba se gaban desk dinmu nida Aziza. Akan desk din Aziza ya ajiye teaching materials dinda yashigo dasu sannan yadubi entire class din yace "Good morning class" da turancinsa da is very clear and fluent sannan ga ascent din fillancinsa daya karama yanayin turancin nasa gardi.

Gabadaya Yan ajin amsawa mukayi da "Morning Sir" kafin Yaya Lamido yace "let me start by introducing myself first" seyadan numfasa kafin yafara introduction din,yace "I'm Isma'il Yusuf Kwami From Gombe state, Kwami local government. I finished all my studies within Gombe state. And Alhamdulillah I'm now fully a graduate in BSC Geology. I'm here for my NYSC program and within my entire NYSC program I'll be taking you guys English Language in the absence of your Teacher. She'll be out of the college for few months due to some personal issues" jinjina kai mukayi duka sannan yakarada "I hope you guys will cooperate with me for a better understanding?" "Yes sir" shine abunda duka Yan ajin muka fada.

Sekuma yace muma muyi introducing kanmu one by one sabida yasan kowa.

Dagakan first row akafara inda kowa zaifadi full name dinsa,state of origin dakuma local government dinsa hakanan he somehow makes the class lively tahanyar tsokanar yaren mutum kokuma inkayi kama da masu yaren ko bakayi kama dasuba. Ahaka har aka iso kan row dinmu wanda mune a seat din gaba nida Aziza dankuwa tun js2 dinmu muka Zama seatmates,ita yafara tambaya tayi introducing din kanta tagama Wanda ni atunanina nice next anma da mamakina senaga sabanin hakan. Tsallake ni Yaya Lamido yayi tahanyar nuna Zuwaira dake bayana.

Binsa nayi da idanu baki sake jin ya tambayi Zuwaira sannan cikin sauri nace "Yaya Lamido ka tsallakeni baka tambayeni ba" ni gabadaya ma na manta position dinsa awannan lokacin dakuma inda muke,naga ana tambayar kowa ankuma tsallakeni shiyasa nayi magana dankuwa har rehearsal din yanda zanyi introduction din nagamayi a Raina. Dariyar danaji wasu daga cikin Yan ajinmu nayine yasani sauri gane baranbaramar danayi, sauri nayi nasa palms dina a bakina Ina wara idanu ayayinda nakalli Yaya Lamido nace "Sorry Sir" anma memakon ya kawar da zancen tahanyar karban tuban nawa seya dubeni with a smile on his face yace "Mezan tambayeki Nanaaa? Is there anything new that I need to know about you?" Shiru nayi bance komai ba,seyayi dariya, yace "I'm asking those that I don't know kekam aisede ma atambayeni Abu game dake" sekuma yamaida hankalinsa gakan Yan ajin.

Yace "Don't mind her. She's my sweet little Sis,nema kawai take tatadamin hankali babu gaira Babu dalili" dariya Yan ajin sukayi inda daganan kuma aka cigaba da introduction din har aka gama. Tambayar mu yayi topic dinda muka tsaya muka fada mishi,seya koma farkon topic din yadan sake briefing dinmu akan topic din kafin yashige next topic dazamuyi maisuna "CLAUSES". Yafara mana introduction kenan lokacin break yayi. Aikuwa yanajin anyi ringing bell yarufe teaching materials dinsa yadubi Yan ajin namu yace "it's time for break,so let's just call it a day" gyadakai mukayi duka inda mukace "Okay Sir" cikeda farin ciki anma memakon yatattari takardunsa yafita yabar ajin sekawai yahau saman desk dina yazauna yana fadin "How do you see me teaching today?" murmushi nasaki sannan nace "Bravo alaik. you did well! Like very very well Yaya lamido. Bantaba tsanmanin you can teach well like this ba" nayi maganar sincerely.

Dariya yasaki Jin abun da nace sannan yadan sassauta muryarsa,in a funny manner yace "Ke karfin haline fah kawai and moreover it's English,naci ubana gurin Aunty chioma dole bazan mantashi ba" dariya nida Aziza mukayi inda Aziza tace "wacece kuma Aunty chioma?" grinning Yaya Lamido yashigayi sannan playfully yace "Aziza yakaman kema kinason kizama Miss curious kamar kawarki neh?" Sekuma yayi sauri ya juya yana karema class din kallo tako Ina,duk yawanci anfita break,mutum dayace a ajin,Itama kuma tanacan baya zaune kan seat dinta wanda hakan yasashi yin kasa da murya yace "warning Zan muku. nasan ku da shegen tambaya,toh wallahi kurufamin asiri kada wataran kujefomin tambayar datafi karfina a ajin ku inkasa amsawa insha kunya" dariya muka saki nida Aziza harda nikam harda rike ciki.

QADRWhere stories live. Discover now