Page Nine - Shocking News 2

336 37 3
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert* @wattpad

*Page Nine - Shocking News 2*

Free page

Haka suka karbo robar da za'a dibi jinin Baba suka kaima Nurse on duty yazo yaɗiba sannan akamayar lab ɗin don carrying test ɗin inda akace daga baya aje akarbi report. Kawu Sani yabar Yaya Salim da Kawu Hassan tareda ni inda yace mana zeje yadawo. ashe zuwa yayi ya sille Ƴan uwan nasa kan abunda sukayi. A makeken shagonsu dake makare da atamfofi,laces,shaddodi kala kala,kayan yara da manya dadai sauransu yasamesu. gakuma customers daketa kai kawo cikin shagon suna sayan kaya. Kawu Sani bayan sungaisa dasauran yaran shagon yaceda Yaya idrissa yanason magana dasu shida Kawu Adamu wanda hakan yasasu shigewa can cikin store room ɗinsu suka kebe.

Magana yayi musu akan abunda sukayi anma memakon sununa regret ɗinsu sesuka daura ma Kawu Hassan laifi suka ce su bece musu komaiba,basu saniba.

Ran Kawu Sani baci yayi sosai dan yasan Hassan bazai taba yimasu sharri ba yace "Koh Hassan bai faɗa muku ba aganina yakamata ace kunayi kuna leka likitan kuna tambayarsa update gameda rashin lafiyar Umar ɗin. Kai koma bakujeba kwa tambayi shi Hassan ɗin me likitan yace anma cikinku babu wanda yataba tambayarsa bayan kunsan baiyi karatun dazai fahimci mema akecikiba ko anmai bayani,likitan ma baku taba nemansaba kwata kwata danyace Hassan kaɗai yasani" Kawu Sani yace "Why? sokuke kucemin aikinku yafi lafiyar Umar komi? couldn't you take few hours out of your work hours for your Brother? haba haba! kunbani mamaki wallahi" Kawu Sani yakarashe maganar cikeda disappointment.
Kawu idrissa dayake ganin Kawu Sanin raini yakeson yimai ba gyaraba yace "ya isheka Sani! ya'isa haka! karka faɗa mana maganar banza. duk zuwan damu keyi muna dubashi baka ganiba? Duk bata kuɗin transport da kuɗin mai ɗinda akayi akan iyalanmu dasukaje dubashi baka ganiba?sayan maganin danayi yauda safe nakawo shima duk baka ganiba se little mistakes ɗinmu koh? toh kai meya hanaka zuwa dakaga kafi kowa sonshi? yanda kakeson aikin ka haka mukeson namu muma hakanan yanda kakeson ciyarda iyalinka dede gwargwado haka muma mukeso muyi shiyasa muke faɗi tashi" cikeda bacin rai Kawu Sani yace "miye amfanin zuwanku dana iyalan naku tunda ba abunda yadace kukeyi ba? Kuma a shagon naku mekukeyi inbanda zama? ba yaranku ke aikin ba?" wannan Karan Kawu Adamu ne yayi magana yace "Dan yaranmu ke aiki se akace bazamuyi supervision ba?" Kawu Sani yace "gaskiya ce dai guda ɗaya kuma bakwa sonta sannan inason kusani rayuwarnan bakomai bane acikinta,inmutum yace zaisa hassada da kyashi aransa toh he'll never succeed. Kuma in mutum yayi mai kyau zai gani a kwaryar sa,inbakayi maikyau dinbama duka mutum zai gani a kwaryarsa" daganan yajuya yafita rai bace yana mamakinsu. Atunaninshi dukda suɗin se ahankali bazasu taba yin abunda sukayi yanzunba,aganinshi rashin lafiya tafi gaban komai,aganinshi ko makiyinka ne indai akazo tafarkin jinya dole ya sarara maka anma segashi nashi Ƴan uwan sunbashi mamaki lokaci guda,suncanza mai view dinshi gameda Ƴan uwan taka lokaci guda.

Dayanman ranar Gogode takoma Babban buli inda tayi tayi inbita anma naqi nace nida Baba zanzauna kuma har lokacin banbar zubda hawayeba hakanan naqi sakin hannun Baba koda kuwa na minti ɗaya ne. Da dare Kawu Hassan yafita yasiyo mana Koko da kosai yadawo,sanda yamin tayi kinci nayi nace naqoshi hakanan inaganinshi yazauna yaci abincin iyacinshi harsaida yakoshi sannan ya ajiyemin sauran.

Dana tambayeshi na Baba fah secemin yayi "ai anasamai drip bayama iya tashi bare ya iya cin abinci" wasu irin dummammun hawaye sukabi kan kuncina Ina tuno yanda Baba baya wasa da abinci,yana bama abinci ultimate respect,duk inda time ɗin three square meals ɗinnan sukayi zaibar komi yakeyi yadawo gida muci abinci,wataran innaki ci yayita lallashina yana rokona inci bayason ulcer takamani. Toh gashidai yauga abincin kuma lokacin cinta yayi anma babu halin tashi yaci.

Karfe takwas Yaya Salim yashigo ɗakin hannunshi riqe da ledan take awayn abinci dana fruits yasamu guri yazauna yana tambayar Kawu Hassan jikin Baba.

Kawu Hassan yace masa "Dasauki alhamdulillah" kafin yadubeni cikeda tausayawa yace "Rukayya kukan nandai bazaki barshi ba? do you want to hurt yourself by crying?" Jijjiga masakai nayi ahankali,daman tuncan shi mutumina ne akaf gidansu. bamusaba ba ko ada damuke gida ɗaya sabida boarding school yayi,hutu kawai muke haɗuwa shima ba sosai ba. Toh yanzu ma dayake jami'a bamu saba ba bakuma mutaba zama munyi hirar datakai na minti goma ba anma duksanda naje gidan indai yananan yaganni kuma toh zamu gaisa yatambayeni Baba fuska daukeda fara'a unlike the others shiyasa nake ganin darajarsa da girmansa sosai. Sauran Ƴan gidan kuwa,wasunsu inna samu hararama ingode Allah hakanan wasunsu ma ko kallo ban ishesuba,wasunsu kuma tsangwama da habaici kokuma azageni directly babu yanda na'iya. Shikaɗai yafita zakka, shikaɗai yake ganina da idon mutunci mugaisa lafiya lafiya.

QADRWhere stories live. Discover now