Page Twenty Three

31 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad*

Page Twenty Three

Aunty ne tafara shigowa parlourn sannan Ummi. Ƙarara naga mamakin gani na a fuskar Aunty sanda tashigo parlourn anma se tayi ƙoƙari ta ɓoye mamakin nata takaraso cikin parlourn tasamu guri tazauna saɓanin Ummi da data shigo ta ganni seda taja tunga tatsaya tana kallo na baki sake,harsaida Kawu Sani yamata magana sannan takaraso cikin parlourn itama tasamu guri tazauna.

Gaida Kawu Sanin sukayi duka tareda yimashi sannu da dawowa ya amsa sannan yashiga tambayar Aunty hidimar biki inda ananne nagane inda tajeta ɗazun. ashe bikin cousin ɗinta data taso agaban kishiyar Inna(mahaifiyar Aunty) akeyi yauɗin. Sena fara mamakin miyasa Siyama da Sadiya basuje suba despite being bikin Ƴar uwar mahaifiyarsu. Anma ganin banida amsar dazan bama tambayar tawa yasani kawarda zancen araina tahanyar saka ma raina cewa kilan sunada ƙwaƙwaran daliline shiyasa basu je can ɗinba.

Inanan zaune gefen Kawu Sani yafara yi masu magana akaina.

Yace "Daman nataraku ne duka dan insanar daku cewa Rukayya daga yau tareda mu zatana zama insha Allah" saurin katseshi Ummi tayi tunma kafin yakarasa musu bayani.

Tace "kaman yaya zata zauna anan? Ba agidan idriss kace zata zauna ba?" tabbas Kawu Sani yaji haushin tambayar Ummin anma seya ɓoye bacin ran nasa yace "mun canza shawara. Anan zata zauna damu kamar yanda nafaɗa" dan aganinshi bai kamata yazauna yanayi masu bayanin abubuwan da su Kawu idrissan sukayiba. Wannan ɗin tsakaninsu ne su kaɗai and moreover bai tabbatar da cewa idrissa bayason riƙe Rukayya ba haryanzu sannan yanada yaƙinin koda wasa ƴaƴanshi mazan bazasu taɓa faɗama iyayen su Mata ba.

Salim bazai taɓa fadaba sabida sanin halin mahaifiyar sa dakuma irin ƙin Rukayya datakeyi ayayinda Fahad Kuma daman shi ba mutum bane dayake shiga shirgin da banasa ba. Auntyma kuma bazata taɓa tambayarsa ba dankuwa halinsu ɗaya da ɗan nata. Harkokin gabanta kawai takeyi babu ruwanta da shiga harkan wani.

Tunbayan da Kawu Sani yabama Ummi amsa taɗauke kanta daga gareshi takai wani barin rai bace tanata wani kumbura fuska ita adole bahaka tasoba kuma sotake tayi magana anma tasani koda wasa tace zata sake furta wani kalma toh lallai Kawu Sanin ɓata mata rai zaiyi akan wata ballagaza Rukayya shiyasa taja bakinta tayi shiru tareda zubama sarautar Allah idanu.

Kawu Sani yace musu "Rukayya Ƴa ce agareni dankuwa abunda yayi mahaifinta shiyayi ni sabida haka nake neman alfarmar agurin ku. kuma kuɗauke ta kamar Ƴar cikin ku,ku riƙeta amana,kubata kulawa kamar yanda zaku bama Ƴaƴanku na cikin ku sekuga Allah yabaku lada. besides,Ɗana kowane. You never know wanda zai amfaneka in the future" gyaɗa kai Aunty tayi ahankali batareda tace komaiba.

Haka yacigaba dayi musu nasiha akan falalar dake cikin riƙe maraya kafin daga ƙarshe yamusu bayanin makaranta dayasa Yaya Fahad yanema min. Ananne naji yana faɗin tunda ma akwai yayun mu acan baya tunanin zamu samu matsala acan and then I realized ashe su Yaya zaheera duk sunyi resuming school ne shiyasa bangansuba. Yaya Siyama kuwa tagama secondary school daman,kusan tare suka gama da Yaya Zunnurain dan kusan sa'anni ne. wata uku kawai tabama Yaya Zunnurain ɗin"

Sallamarmu yayi daga karshe inda ni, Yaya Salim da Yaya Fahad muka fice a parlourn muka barshi da matayensa guda biyun dukda kuwa girkin Aunty ne yauɗin. Nafidai tunanin akwai abunda zasu tattauna a tsakaninsu ne shiyasa Ummin bata fito ba.
Muna fita a parlourn Yaya Fahad yayi wucewarsa boys quarters ayayinda Yaya Salim yatsaya mukayi sallama sannan shima yabi bayansa.

Tafiya nadingayi inajin yanda cool breeze ɗin filin gidan ke ratsa kowani ɓangare na jikina ayayinda araina nakejin inama inada kwanciyar hankali. Inama ina cikin farin ciki? da senafi jin daɗin whether ɗinnan,dahar guri zannema inzauna Ina shaƙar wannan iskan me tsananin daɗin Ina feeling happiness ɗina tareda tuno memories na farin cikin rayuwata.

QADRWhere stories live. Discover now