Page Thirty Four

43 4 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty Four

Cikin sati biyu muka gama jarabawar mu kuma kamar yau Friday mungama jarabawa washegari Saturday ne visiting day. Yawanci bazuwa ma ɗalibai wannan visit ɗin za'ayiba,muma kuma baza'azo mana daga gida ba hakama Aziza kasancewar sati guda yarage mana mutafi gida hutu First Term. Lamiɗo ne nake ganin tsanmanin zuwansa dayake wancan visit ɗin yacemin zaizo insha Allah.

Tunkan mugama Exams nasanar da Aziza cewa Lamiɗo zaizo kuma zata rakani gurinshi muje sugaisa kuma atake dana faɗa mata ta amince. ranar Friday bayan antaso daga sallar juma'a muka ɗauki kayan mu mukaje laundry muka gogeshi tsaf sannan muka dawo nan kwanana muka kafa babin hira nida ita,munaji Ƴan ɗakinmu na hirar za'ayi filmshow dadare washegari Saturday kuma ayi social night a social Hall ɗin makarantar anma kwata kwata mubamu da interest ɗin zuwa dankuwa yawanci programs ɗinnan zuwa ake a haɗu da Boys ɗin makaranta ayita haukan banza dana wofi. mundaice zamuyi attending other activities daza'ayi cikin sati mai zuwa during the day,irinsu Games,press club day,RedCross club day,debate competition da speech daza'ayi insha Allahu.

Washegari Saturday tun bayan inspection muka shirya muna jiran azo acemana Lamiɗo yazo shi anma shiru babushi babu labarin shi har azahar wanda hakan yasamu deciding cire kayan mu mu'ajiye inyaso dayazo mwa saka mutafi. Banwani ɗaga hankalina ba na rashin ganinshi dawuri tunda last time ma bayan la'asar yazo. Aikuwa yauɗinma hakan tafaru,harmunyi bacci muntashi munyo alwala zamuyi sallan la'asar kenan sega wata Yarinya tazo nemana,ita tasanar dani Yayana yana jirana a visiting ground ɗin makarantar. Cikeda zumuɗi nace mata "toh mungode gamunan zuwa" Aziza dakejinmu murmushi tayi sannan tace "ai danaga yanma yafarayima harna cire rai dazuwansa" Ƴar dariya nayi sannan nace "Nikam bancire Raiba dayake last time ma dayazo bayan la'asar ya'iso makarantar nan" Sena ɗauki housewears ɗinmu dake ajiye namika ma Aziza nata bakinnan yaƙi rufuwa tsabar farin cikin nace "karbi kisaka muyi sallah muje dawuri kada yayi ta jiranmu"

Cikeda zolaya Aziza tace "aikuma Yaya Lamiɗo yazo baza'asamu kanki ba" ina dariya nace "Kedai bari" ayayinda nake saka uniform ɗina. Cikin mintuna goma shabiyar mukayi sallah muka ƙarasa shirinmu sannan muka fita visiting ground kuma ban manta ɗaukan gift ɗinda aka baniba as the 2nd position na ajinmu. Acan school garden inda na haɗu dashi last visiting muka samo shi,yauma yayi gayu yayi kyau sosai abunsa,wani sa'in har mamakin yanda Lamiɗo ya'iya dressing nakeyi. Walau kananun Kaya yasaka walau manya yasaka duk amsar jikinsa sukeyi sukara masa kyau da kamala,tunda nasanshi dede darana ɗaya ban taɓa ganinshi a hargitseba,he always looks good and so presenting koda kuwa sanda muke zuwa field trip tareda shine.

Yau ƙananum kaya yasaka saɓanin last visit daya saka manyan kaya. yau banyi ihun murnar ganinshi ba anmadai har na Isa gareshi bakina kasa rufuwa yayi.

Shine cikeda zolaya yace "Ƴar Birni Mobbu honduko ( Yar Birni rufe bakin)" sekawai nakwashe da dariya Ina kokarin rufe bakina nace "Ina wuni Yaya Lamiɗo" playfully yace "Bazan amsa gaisuwar taki ba tunda ajiyeni kikayi inajiranki kamar gawan shanu" dariya nakuma yi sannan nace "Kai Yaya Lamiɗo bamufa wani jimaba anasanar damu mukayi sallahn la'asar muka fito kuma aikai ka Shanyamu,tunsafe muka shirya muna zaman jiranka" wara idanu yayi sannan yace "haba?" Ina murmushi nace "Allah kuwa" seya kama kunnuwansa cikin sigan bada hakuri yace "I'm sorry Dearest Sis. I had to finish some work acikin Bauchi kafin nakaraso nan" cikin sauri nasa hannu nacire hannun sa daya kama kunnuwansa dashi Ina murmurshi nace "Laaa bakomai ainasan ba lallai kazo dawuri ba daman tunda wancan karanma iyarhaka kazo, zumuɗin ganinka ne yasani shiryawa dawuri" fuskar Lamiɗon kaɗai zaka gani kagane ba ƙaramin daɗi kalamaina sukayi masaba.

Seya sa hannu a kan kirjinsa yana smiling,funily  yace "Lord!!! My heart will explode. ashedai haka nikeda importance har ana zumuɗin ganina" dagani har Aziza dariya mukeyi masa ganin abunda yayi.

QADRWhere stories live. Discover now