Page Thirteen- Flashback 2

368 32 1
                                    


🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Thirteen - Flashback 2*

Amina tana isa unguwarsu gidansu Hafiz tama mai machine kwatance yakaita. Tajima agidan suna hira da mahaifiyar Hafiz ɗin harsaida taga shabiyu takusa,su Lamiɗon sunkusa dawowa daga makaranta gashi batayi lunch ba sannan tamata sallama tatafi bayan tabar mata sallahu in Hafiz ya dawo daga makaranta yazo gida tana nemanshi don Allah.

Lamiɗo tunda yadawo daga makaranta yaga canji agurin Ummarsa. she's been acting weirdly kuma babu irin tambayar duniyar nan dabaiyi mataba amma ko cikanka batace mai ba wanda hakan yatabbatar mai dacewa fushin dashi akeyi bada kowaba tunda gashi tana harkokin gabanta da sauran Ƴaƴanta. ba ƙaramin damuwa yashiga ba hakanan abincin da tasa Basma takawomai ɗakin shi ma kinci yayi sabida kwata kwata ji yayi bashida appetite ɗin kuma. In akwai abunda yatsana aduniyar nan damuwar Umma da tashin hankalinta,in akwai abunda yake hanashi sukuni kwata kwata aduniyar nan toh yaga Ummarsa bata walwala dan gaba ɗaya se shima yaji duniyar tadainayi masa daɗi. koda ukun rana tayi daƙyar yashirya yatafi Islamiya bayan yabi ta ɗakinta yamata sallamarda batako kalleshi ba bare yasa ran zata amsa.

Dayanma dasuka taso daga Islamiya Hafiz yace masa suje gidansu tare anma se Lamiɗon yace masa shiba gida zashiba,zeje gidan kawar Umma Hajiya Safiya yagaisheta ne sunkwana biyu basu gaisa ba. Hafiz yace masa "Toshikenan nidai gidanku zani kafin inwuce gida sabida ɗazu Ummar ka tazo gida tabar ma Umma na sallahu wai tana son ganina inna dawo daga makaranta" Lamiɗo da harya fara raba hanya da Hafiz yayi sauri yadawo yace "Ummana taje gidanku nemanka kace?" Hafiz yace "Eh hakadai Umma tacemin ɗazu dana koma gida bayan munrabu a school. Shine tace Inna taso a Islamiya nabi ta gidan naku inji menene" cikeda damuwa Lamiɗo yace "Ta tabbata nayi laifin kenan,ta tabbata fushin da Umma keyi dani sabida wani laifi danayine danikaina bansanshi ba" Hafiz yace "kayi mata wani abunne kafin katafi school?" Lamiɗo yace "haraam. wallahi lafiya lafiya muka rabu yauda safe,she even escorted us to the gate harsaida school bus yazo ya ɗaukemu sannan takoma gida" Hafiz yace "Ikon Allah. toh dai kayi kokari katuna kasan fushin Uwa ba abun wasa bane" Lamiɗo yace "I've been thinking all day anma ni nakasa tuna menayi mata Hafiz,tunda nadawo na tadda condition ɗinta ko abinci kasaci nayi,bakaga a Islamiya yau seda Mallam yamin gyaraba da ina bada hadda? Wallahi I was just not in my right senses. anmadai yanzu mujemu gidan nizan tsaya ta window inji me Umman zatace maka kaga daganan zansan laifin danayi mata se inbata hakuri" Hafiz yace "A'a Lamiɗo kasandai babu kyau laɓe,mudaije kajirani a ɗakinka ko awaje Inna fito zanfaɗa maka yanda mukayi da'ita insha Allahu" Lamiɗo yace "zandai jiraka awajen dan intaga Ina cikin gida zata iya fasa yimaka maganar" Hafiz yace "toshikenan. Kafasa zuwa gidan Mama Safiyan kenan?" Lamiɗo yace "Kaiii kyaleta. daman nakwana biyu banje nagaisheta bane and nasan kona koma gidan yau I'll just make the atmosphere worst for Umma shiyasa nayi deciding najecan anma yanzu zuwa inji laifin danayi a gida inkuma bada hakurin laifin yafimin mahimmanci akan zuwa gidan Mama Safiyan,insha Allahu gobe zanje mata"

Hafiz yayi murmushi yace "toshikenan" inda daganan suka jera suka tafi gidansu Lamiɗon dake cikin masarautar. awajen gidan Lamiɗo yasamu wani dakali yazauna inda yakeda tabbacin ko Ummarsa taleko bazata ganshi ba sannan yacema Hafiz ɗin yashiga shiyana jiransa agurin.

Hafiz sallama yayi a kofar parlournsu Lamiɗo inda Basma da batajima dashigowa daga Islamiyaba ta amsamai danko shiga cikin gida batayiba tukunnan. ƙarasawa yayi cikin parlourn ayayinda Basmah ke faɗin "A'aaa Yaya Hafiz kaine daman?" Yace "wallahi nine Basma" Basma tace "Ina wuni?" Hafiz yace "lafiya Lau. Ya karatu inafatandai yau bakisha bulalan hadda ba?" Hafiz yakarashe maganar cikeda zolaya Basma tace "aiyanzu nadage sosai bana bari ayimin dukan bada hadda danaga Uwar bari" Hafiz na dariya yace "toh Allah yabada sa'a" Basma tace "Amin" ananne Kuma suka jiyo muryar Umma daga ciki tana tambayar wayene yazo inda Basma tashige cikin tanacemata Hafiz ne yazo.

QADRWhere stories live. Discover now