Page four - A little Agreement

483 43 0
                                    

🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Four - A little Agreement*

Ahanyar komawa na nahadu da Indo ashe batama tafi kai niqan ba tukunnan kuma ganin najima bandawo ba yasa Yadikko Rahane tace mata tabiyo bayana. tambayana inda natsaya tashigayi ayayinda take kokarin karban kwanon kandilon dake kaina.

Harna buɗi baki zanfaɗa mata inda natsaya sekuma natuno da alkawarin danayi wa Lamiɗo wanda hakan yasani saurin canza maganar,nace mata gajiya nayi shiyasa na tsaya hutawa.

Indo tace "Sannu. shiyasa akace karkije sabida bazaki iyaba" kyabe baki nayi sannan nace "toba gashi yanzu nataho ba" Indo tafiya tafarayi tana faɗin "anma ai seda kika bata lokaci,danine naje diban kandilon nan da tuni ankusa gama girkin nan" ahankali nace "kiyi hakuri toh" juyowa Indo tayi tabar tafiyan datakeyi,tatsaya tana jiran in isota mutafi tare fuskarta ɗauke da murmushi. haka muka kama hannun juna muka karasa gida,tana ajiye kwanon kandilon ta ɗauki buhun hatsin tafice daniyar kai niqa inda nikuma nawuce ɗakin Gogode inajin haushin surutun dana tsayayi da Lamiɗo harna manta inada niyar ciran kanya ahanyar dawowa na.

Kwaɗon Rama akayi da rana se kunun hatsi da aka dama,har kofar Gogode Yadikko Rahane takawo mana abincinmu ganin Indo har lokacin bata dawo daga niqa ba,nice nasauko daga kan babban gadon Gogode nakarbi kwaryar kunun da akushin da akasaka mana kwaɗon ramar naje na ajiye inda muke ajiye abinci duk sanda aka kawo.

Gogode dayanzu ta'idar da sallan azahar tadubi Yadikko Rahane dake tsugune jikin kofar ɗakin tashiga tambayarta ko ankai ma Lamiɗo abinci. Yadikko Rahane tace "ba'akaiba babu ɗan aikene daman ina jiran Indo tadawo seta kayi mishi,gashi Itama haryanzu shiru" tunkan Gogode tayi magana nayi saurin cewa "kawo abincin inkai mishi Yadikko" Yadikko Rahane tace "A'a kibarshi kawai namasan Indon takusa dawowa yanzu" tura baki gaba nayi cikin sigar shagwaba nace "Allah zankai Yadikko Rahane" Gogode dake kan darduma tana wurudi haryanzu tace "kinsan inda yakene?" cikin sauri nace "Eh Gogode. ɗazu damuna dawowa daga surfe naganshi abakin masallaci" Gogode tace "toh kikayi mishi anma kidawo dawuri kici abincin kema" marairaice fuska nayi sannan nace "Inna kai mai abincin  zan karasa gidansu Kwaiɗum ingaida Innarta" Gogode tace "abincin kuma fah?" nace "banajin yunwa Gogode am, In na dawo zanci" Gogede tace "toh sekin dawo kikuma gaidamin innar Kwaiɗum ɗin" cikeda murna natashi nazari hulana nasaka kafin nabi bayan Yadikko Rahane naɗauki abincin. a kofarsu nasamu Ƴar karamar kwaryar dazan ɗebo kanya ciki kafin nafice agidan.

Daman nibawai gidansu Kwaiɗum din nakeda niyar zuwaba,niyana danakaimai abincin inwuce ciro kanya. bansame shi abakin masallaci ba hakanan ina mamakin ya akayi baidawo ba bayan yasan Baffanaina zuwa wannan lokacin suna gida kuma insunga bayanan  zasu gane ciwon kafar karya yayi. dawannan tunanin natafi karkarshin bishiyar mangaron dana barshi ɗazu, tundaga nesa nahangoshi kwance ƙarƙashin bishiyar yana baccinshi hankali kwance. karasawa nayi na ajiye kwanon agefenshi kafin nazauna kusa dashi nashiga tabashi ahankali inatashin shi harsaida yabuɗe idanunsa dasuka canza launi alamun yajima yana bacci kenan.

Cewa nayi "katashi ga abinci ance inkawo maka daga gida" wartsake idanunsa yayi sosai kafin yatashi yazauna yashiga karema yanayin filin gurin kallon yace "badai azahar tayiba?" nace masa "anjima dayin sallah gashi su Baffa harsun daddawo gida,sanda nawuto masallaci ma suna sallah" afurgice yadafe kirjinshi sannan yace "nashigesu Yar birni. yanzu yazanyi? asirina zai tonu" yanda yayi maganar seda yabani dariya.

Cikeda yarinta nace "toh kakoma da rarrafe kawai. sekacemusu da rarrafe kaje yawo"  dariya yama yarintata sannan yace "banshirya kurkurje kafana akan karyaba Yar birni" cikeda curiosity nace "toh haka zaka koma suganka?" bude jakarsa yayi yaciro bottle din ruwa,yashiga cire socks ɗin kafarsa kafin yafara alwala cikin nutsuwa Ina kallonshi harya gama,yaciro sallaya a jakarsa yashimfida yatada sallah.

QADRWhere stories live. Discover now