Page Twenty Two

37 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad*

Page Twenty Two

Rukayya nafita a parlourn Maman Rabi'u takaraso cikin parlourn tasamu ɗaya daga cikin kujerun parlourn tazauna sannan tadubi su Salim da gaba ɗaya yanayinsu yagama nuna ransu a bace yake da abunda tayima Rukayyan. Anma se hakan baidametaba danko su ɗinma she's ready to hurt them indai akan batun Rukayya tazauna agidannan ne toh Babu wanda bazata iya bata ma raiba.

Salim ne kaɗai ya iya yagaida ta fuska ɗauke da ɗan fara'a dukda kuwa ransa a matukar bace yake inda Fahad kuwa ko kallon inda take yagaidata amma sebata amsaba,shima kuma sebe damuba dankuwa inda sabo yasaba darashin amsa gaisuwartasa. danne danne yakoma yi cikin wayar sa pretending as if bemasan abunda yake faruwa a parlourn ba anma dazaka buɗe zuciyarsa kagani kokuma ka kalli fuskarsa closely dole zaka gane ransa a matukar bace yake.

Maman Rabi'u ko kaɗan batayi danasanin rashin amsa gaisuwar Fahad daba tayiba hasalima baya gabanta kamar yanda mahaifiyarsa bata gabanta. Koda can dasuke zaune gida ɗaya daman Ummi ce mutumiyarta dayake halinsu yazo ɗaya. Kwata kwata baswa jituwa da Aunty dukda kuwa she was the first wife. Ita tafara sani kafin Ummi anma dayake da'ita tayi kishin balbalinta shiyasa nasu baizo ɗaya ba,acewarta Aunty macece me shegen girman kai danuna tafi kowa shiyasa basu taɓa shiriba take kuma jin haushinta shiyasa Ummi nashigowa gidan tayi sauri suka haɗe kai suka zama kawaye suna harkokinsu tare suka juyama Auntyn baya.

Amsa gaisuwar Salim Maman Rabi'u tayi Jin yagaidata sannan ta tambayesa lafiyan kannensa sa da Umminsa inda yace duk lafiya Lau suke kafin kuma parlourn yaɗan ɗauki shiru nawasu daƙiƙu.

Salim Jin shirun yayi yawa gashi Allah Allah yake ya'isa gida sabida gajiyar daya kwaso a hanya dakuma dokin ganin iyayensa da su Zunnurain yasashi fara yunkurin tashi tsaye yana cewa "toh Aunty. Muzamu wuce gida,daman munkawo Rukayya ne" Maman Rabi'u zabura tayi kamarma tunda can batasan da zancen kawo Rukayya gidan ba.

Tace "wace Rukayyan? kuma awani gidan zata zauna?" Salim komawa yayi yazauna Jin abunda Maman Rabi'u tace cikeda mamankin ta,yes yaji haushin abunda tayi yanzu sannan yasan Rukayya ba ƙaramin wahala zatasha ba inzata zauna agidan anma bai taɓa tsanmanin Maman Rabi'u zatayi questioning ɗinsa akan hukuncin iyayen nasuba,atunaninsa tariga da takwana da sanin hakan anma Jin abunda tace yasashi cewa "Su Abba ne suka yanke shawarar tazauna anan" dankuwa dukda Fahad befito yafaɗa masa ba hakanan besan yasukayiba, he's very sure wannan ɗin decision ɗin iyayensune.

Maman Rabi'u tace "Cabdi jam! Toh nidai bansan da zancennan ba kuma Baban Rabi'u besanar dani ba inaganindai mahaifinka ne ya yanke shawarar sa shikaɗai shiyasa yace akawota nan" ahankali Salim yace "inaganin hakanne toh" Fahad dake zaune gefe yanajinsu tundazu yadago kansa yadubi both Salim da Maman Rabi'un sannan yace "it was not his decision. dukansu suka yanke shawarar Rukayya tazauna agidannan and even Kawu idrissa knows about it. Infact he was suppose to pick her up from her Home rashin zuwansa ne yasa su Gwaggo Suwaiba sukace inkawotanan bayan na ajiyesu a tasha"

Maman Rabi'u data zubama Fahad idanu tun sanda yafara magana tanajin kaman taje tarufeshi da duka tace "komadai yasukayi can musu,atsakaninsu nidai babu ruwana tunda maigidana baisanar daniba sannan inbanda rashin adalci da rashin tausayi yakamata ace Rukayya tazauna agidannan nema? muma yaushe muka gama jida kanmu da namu ƴaƴan dahar za'ace za'akaro mana wani nauyin? Toh nidai ba'a gidanaba,kujecan kunema mata wani matsugunin anma banan ba. Shiɗinma inaga kawai kawaici yayi ma iyayen naku da akace yaɗauketa amatsayinshi na Babba anma ai Inza'a duba matsayi da status dakuma capability na mutum mahaifinnakune yakamata yariƙe Rukayya ba Baban Rabi'u ba,inkuma yaga shima bazai iyaba seya maida ta Giyaɗe wurin kakanninta ba shikenan ba? Anma se azo ace za'a ɗaurama wasu wahalanta bayan ubanta dayake raye babu wanda yataimaka ma inbanda kanshi da Ƴar sa daya sani"

QADRWhere stories live. Discover now