Page Twenty Five

45 4 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad*

Page Twenty Five

Sashinta nawuce dukda kuwa Ina fargaban shiga tace nashigo mata da warin jiki toh anma yazanyi? Inada wanda zeje yakaimin sakon ne? And moreover inbankai sakon bama wani laifin zai zama shiyasa gwanda nakai ɗin kawai inyaso se inyi enduring koma me zatacemin. A nan parlour inda nabarsu ɗazu nasamesu,a bakin kofa na rakube kamar wata munafuka zuciyata na bugu sannan nace "Ummi nagama wanke wanken" yitayi kamar batajini ba harsaida na maimaita kalamaina sannan akafule tace "Naji" alamun na dameta.

Juyawa nayi zanbar ɗakin naji cikin tsawa tace "nace miki kitafi ne?" tsayawa nayi cikin sauri tareda juyowa ina kallonta sannan nace "A'a" harara ta watsamin sannan tanunani da ɗan yatsa sannan tace "nangaba inkikazo gurina ban sallameki ba kika yarda kika tafi sabamiki zanyi kinajina?" gyaɗa matakai nayi ahankali sannan nasauke kaina ƙasa ina zullumin miye dalilin dayasa ta tsaidani ɗin?"

Senaji tace "kiyanka min albasa guda huɗu manya yanzu zan fito nima" cewa nayi "toh" anma memakon intafi sena cigaba da tsayuwa anan ɗin tunda banji ta ambaci intafi ba. Nafi mintuna uku ina tsaye sekuma naga tadawo da dubanta gareni Rai bace tace "tsayuwar me kikeyi Kuma?" Cikin sauri nace "babu" sannan najuya nayi ficewana inajinta tanata zagina waini mahaukaciyar wace garice tasani aiki natsaya Ina kallonta kamar wata tsohuwar mayyah!

Dukyanda naso inyi resisting tears ɗina kasawa nayi haka nafita backyard ɗin na nufi kitchen harna isa bakin kofar kitchen sena tuna banyi sallan la'asar ba. seda naje na sakeyin alwala nayi sallah sannan naɗauko albasa da wuƙa nafara barewa. Nagama bare albasan kenan na wanko zanyanka sega Ummi tafito.

Kallon cikin rubbern da albasan yake ciki tashigayi baki sake sannan rai bace tace "Baki yanka albasan ba haryanzu?" Atsorace nace "yanzu zanyanka" kamar zata dukeni tace "mekikeyi tun ɗazu baki yanka ba? zaman me kikeyi?" Murya na rawa nace "Seda nayi sallah sannan nafara bare albasan" Ummi tace "yanzudai inyi ta zaman jiranki kenan? Sallan la'asar ɗin tun yaushe akayishi? Kumama in banda gulma da tsugudidi keɗin harnawa kike dahar kika fara sallah?" Jin kalamanta dole seda na ɗago na kalleta in shock anma ganin irin kallon datake watsamin yasani saurin sake maida kaina ƙasa ina mamakin wannan ɗin wace irin matace? Ina shekara goma sha biyu anma tanacemin harnawa nake dazan damu dan banyi sallahba? Sekuma natuno yanda su Yaya Aisha sallah bata dame suba kwata kwata. Most at times tarukut salat sukeyi sabida jarabar son kallon da insun zauna agaban TV baswason tashi harsai sunga an ɗauke wuta ko in an kashe generator Itama kuma uwartasu sebata damu data tsawatar musu ba. wani sa'in ma harda ita akeyin hakan. wani lokacin kuma in sukaga dama ma bazasuyin ba,in lokacin yin sallar tawuce shikenan baza'ayitaba.

Wataran baza'ayi sallar asubahi ba za'ayi azahar,ayi la'asar ayi maghrib akiyin isha'i.

Inajinta tagama kashemin warning akan batason inahada aikinta dawani abuna,bazata hananiyin sallah ba anma inyishi a lokacin daya dace basai tazo tana sani aikiba infara bata excuses. nidai bance mata komai ba dukda kuwa ɗazunma ai aikintan ne yahanani yin sallar akan lokaci. Haka nakarasa yankan albasan ayayinda itakuma ta hura wuta ta ɗaura ruwan tuwo.

Bayan nagama cemata nayi nagama inda tanuna wata leather dake ajiye bakin varendern kitchen ɗin tace namane in ɗauki karamar tukunya inje inwanke matashi inkawo. Sanda nawanko Naman nakawo harta hura ɗayan murhun danhaka setace indaura,na ɗaura,tace inmiko mata albasan dana yanka shima tasaka wanda zai Isa sannan taturani kitchen in ɗauko mata su Maggi,onga dadai sauran spices nayin miya duk naje na ɗauko nakawo inda daganan kuma tacemin in ɗauki ɗayan leathern dake ajiye abakin varendern kubewa ne aciki inje inwankeshi inyanka mata.

QADRWhere stories live. Discover now