Page Eleven - Meet The Kwami's

348 29 0
                                    

🌹 _*QADR*_ 🌹

( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page Eleven - Meet the Kwami's*

Muryar Umma dasuka ji daga ɗakinta tana faɗan dariyar mesukeyi dabasu koma bacci ba har lokacin yasata saurin saka hannu abakinta tana kokarin boye dariyartata. shima Lamiɗon arude ƙasa ƙasa yace "kirufan asiri kirage muryarki kartasan nashigo gidannan bayan nacemata TDB zanyi a school sabida jarabawar gobe" Jidda ahankali tace "toh. yauwa nikam mema yadawo dakai Yaya? bakace a makaranta zaka kwana ba kanada exams biyu gobe?" tabe baki yayi sannan yace "kema kinsan duk burgane kawai,wallahi namaje nakasa karatun,gyangyadi nadingayi kaina yana rawa su Hafiz natamin dariya shine kawai nabaro school ɗin daniyar dawowa gida sena  haɗu da wani friend ɗina a hanya yajani muka tafi gidan kallo shinefa seyanzu muka taso" Jidda cikeda damuwa tace "tou yazakayi da jarabawan goben Yaya?" dariya Lamiɗo yayi sannan yace "sekace bakisanni ba. aigefen mayencan Auwal kawai zanzauna in dabsa,yana rubutawa Ina kwashewa a booklet dina indai ba akawo mana jahilin invigilator ba" Jiddah tace "toh Allah yasa kada akawodin" shafa kan Jidda Lamiɗo yayi yana girgizawa playfully yace "Amin ya Allah Kanwata" Jidda cikeda son jin karashen labarin yanda akasan Lamiɗo yashigo tace "Amma ya akayi suka ganka yau Yaya? Da inkashigo basutaba kamakaba,ya akayi yau sukasan kashigo?" Lamiɗo yace "kaddara" yana dariya ƙasa ƙasa kafin yashiga bata labarin yanda akayi dakuma ɗauke drum ɗinda yasaba biyowa takai da akayi tanata dariya ƙasa ƙasa dukdan karsu janyo Umma tace "ni babu abunda yafi bani dariya ma irin bangaje wazirin da kayi. wallahi dayaganka sekayi sati agidan yari" Lamiɗo na dariya yace "indai wannan mugun ne for sure zanfi satima" yakarashe maganar ayayinda suka kwashe da dariya atare sekuma suka sa hannu suna rufe bakinsu tunawa dasukayi basuson Umma tajisu.

Ahankali Lamiɗo yace "niyanzu damuwana ma baiwuce hanani holewan daza'ayi kwana biyuba sabida na tabbata yanzu zasu fara saka idanu,so I've to stop being late outside" Jiddah tace "gaskiya kam. suma gulmansu yayi yawa wallahi,gida babba irin wannan damutane da dama nada uzurirrikansu suce duk inda sha ɗaya yayi babu wanda zaishigo" Lamiɗo yace "swayi sugama ma mukam ai munada wasu kofofin tunda gashi muna shigowa" sannan yakarada "ke tashi kije kikwanta insamu in danyi bacci,da asuba zan fice please karki faɗama kowa agida nakwana,just pretend as if bamuma haɗu ba kinsan Basma da gulma" Jidda tayi dariya tana ware hannaye sannan tace "wa! ni in faɗa. aibanma ganka ba Yaya a school kace zaka kwana Kuma se gobe after exams zaka dawo" Lamiɗo na murmushi yace "Thank you fav Sis, shiyasa nace sonki" Jidda tace "I love you too Yaya. anma maganar bribe dinfa?" Tayi maganar tana kashe masa ido ɗaya tana dariya sannan takara da "Yaya kasandai gwamnati tahana aikin banza koh?" take Lamiɗo ya tsuke fuska yace "Wani bribe kuma Jidda? yau ai bake Kika buɗemin window ba abuɗe nasame sa" Jidda tasaki baki tana kallonshi sannan tace "Yaya asirifa zanrufa maka nigaskiya abiyani ko inje infadama Umma yanzu" Jiddah takarashe maganar tana kokarin tashi daga zaunen da take. Cikin sauri Lamiɗo yajanyo hannunta takoma tazauna yace "Ke! bakida hankali koh?" Jiddah tamika masa hannun tana tura baki sannan tace "Toh bribe me" tuni Lamiɗo yakoma lallashi yace "Haba Darling Sisi kiyi hakuri mana,kinsandai bamwa ƴar haka dakekoh?" Jiddah tatura bakigaba tace "toh nidai ka bani awarar kawai se infasa faɗa. Allah yunwa nikeji banci komai bafah tun abincin rana sabida tuwo da miyar kuka akayi da darennan" Lamiɗo yace "Allah bansiyoba kiyi hakuri se gobe sabida daman bamuyi dake zandawo gidaba" Jiddah tace "anma doubling za'amin Koh?" yayi Ƴar dariya sannan yace "naji za'amiki tripling ma inkinaso" dariya Jiddan ma tayi sannan tatashi tamishi saida safe kafin tafice a ɗakin cikin sanɗa dankar kowa yaji motsinta.

Tashi Lamiɗo yayi yaje yasa makulli akofar yarufe taciki kafin yadawo yakwanta yalumshe idanunsa yana murmushi with zero worries har bacci yayi awun gaba dashi. Washegari kuwa yanaji ankira sallan assalatu yatashi yasauya T~shirt ɗinsa sabida tsaro sannan yabuɗe class bag ɗinsa yasaka T-shirt ɗinda yacire ɗin aciki sabida inya tashi dawowa dole yamayar da'ita jikinsa sabida kar Umma tayi zargin yazo gida sannan yakarasa jikin windown ɗakinsa yafice cikin sanɗa dan bayason koda buɗe kofar banda kine bare mistakenly Umma tajuyo motsinsa danyasan by now tanacan tana ibada adakinta kamar yanda tasaba kullum. A masallacn masarautar yayi alwala sannan yashige masallaci yaɗauko alqur'ani yafara karatu kafin lokacin sallah yakusa yayi raka'atainul fajir.

QADRWhere stories live. Discover now