Page Thirty One

48 3 0
                                    

🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

Page Thirty One

Ba ƙaramin rudewa Yaya Lamiɗo yayi da Jin kukana ba hakanan cikin tashin hankali yashiga rarrashina tahanyar soothing bayana yana faɗin "It's okay! Stop crying please. I'm here. I'm here with you Nanaa...!" and this words makes me cry even more dukdama kukan na farin cikine,kukan cewa nidinma ashe inada wani haryanzu a doron ƙasa dazai faɗamin wannan kalamai masu daɗin.

Sedana gama kukana nakoma ina sauke ajiyar zuciya sannan Yaya Lamiɗo yaɗago dani daga jikinsa yana kallona da idanunsa dasukayi jazir suka canza launi lokaci guda. Manyan yatsunsa yasaka a both cheeks ɗina ya gogemin hawayena tareda faɗin "Toh Ƴar birni kukan ya isa hakanan. Koso kike har in tafi inyita aikin rarrashin kuka batareda munyi hira ba?" cikin sauri na girgiza masakaina ina murmushi jin sunan daya kirani dashi yau sannan nace "A'a" seyaja hannuna muka ƙarasa kusa da wani fancy chair dake kusa damu yazaunar dani sannan yazauna agefena shima.

Cikeda curiosity nace "Ya'akayi kasan makarantar mu? kuma ya akayi kasan yau visiting day ne?" murmushi yayi sannan yace "Toh uwar tambaya zaki farakoh?" tura baki nayi gaba sannan nace "nidai kafaɗamin please" yace "A'a bazan faɗa ba semun gaisa,inama ko gaisheni bakiyiba" yayi maganar yana ɗan tsuke fuska playfully.

Ƴar dariya nayi ga yanayin dayayi da fuskarsa sannan nasa hannu a bakina Ina faɗin "Aaawww Ina wuni?" danni nama manta kwata kwata bangaishe shiba.

Lamiɗo yace "bazan amsaba tunda seda na roka tukunnan zaki gaidani" pity face nayi sannan nace "kayi hakuri. Allah mantawa nayi" seyasa hannu yaja cheeks ɗina sannan yace "I know,I was just kidding. Toh ya makarantar taku? Hope dai ana karatu sosai? kuma injidai ba'a bullying ɗinku?" yatsina fuska nayi sannan nace "makaranta alhamdulillahi,karatu kuma anayi shima bullying ɗin duka anayi dan seniors ɗinnan babu abunda suka sani se mugunta,sekace susuka biya mana kuɗin makarantar" nayi maganar ina sake yatsina fuska.

Seriously yace "Suwaye da waye suke bullying ɗinki a seniors ɗinnan? Faɗamin sunayensu kokuma kinuna minsu in rama miki yanzunnan" wara idanu nayi ina dariya sannan nace "karama min kuma?" dankwata kwata banɗauki maganar Serious ba.

Yace "Awww baki yarda baneba? Just tell me their names kokuma kinuna minsu inkingansu anywhere around here kiga aiki da cikawa" murmushi nayi sannan nace "bansan sunayensu ba Yaya Lamiɗo hakanan bansan adadinsuba kuma wasuma na manta fuskarsu yanzu" yayi kwafa sannan yace "toshikenan sunci sa'a amma dukranar da kika tuna just let me know kinji?" dariya nayi sannan nace "Toh" sannan nakarada "inasu Umma da Kawata Salma? Ina Yaya Jidda da Yaya Basma?" murmushi yayi yana kallona sannan yace "Baki manta sunansu ba kenan?" gyaɗa masa kai nayi ina lilo da kafana ayayinda nakasa dena murmushi sannan nace "Nina isa inmanta su? Ko  mutum yana manta Ƴan uwansa ne dama?" wara idanu yayi yana mamakin kalamaina.

Tsuke fuska nayi Ina tura baki gaba nace "yakana wara idanu kuma?" Yaya Lamiɗo yace "yanda kikayi maganarne yabani mamaki. Sometimes you speak like an adult" senasake tsuke fuska nace "kenan kana nufin ni jaririya ce?" dariya yayi sosai sannan yace "jaririya kuma? Jarirai ne kaɗai ba adult ba?" tsuke fuska nasakeyi ina pouting bakina nace "Eh mana" yace "A'a Nanaaa! wannan maganar taki akwai sonkai acikinshi" yayi maganar cikeda tsokana wanda hakan yasake hasalani.

Yace "Kefah koh ɗan sweet sixteen ɗin zamaninnsn bakijeba,rabinsa ma bakikai ba anma kikeso akiraki da Adult?"  nace "Eh ɗin,anma ai ni ba Ƴar baby bace dukda bankai wannan shekarunba" dariya yake sosai  yana mamakin rigimana sannan yace "toh naji! Ke ba jaririya bace anmadai that does not mean you're an adult,dukranar da kika zama adult I'll say it to your face proudly insha Allah"

QADRWhere stories live. Discover now