Page Twenty One

45 5 0
                                    

  🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad*

Page Twenty One

Harsuka isa gida Kawu Adamu ne kaɗai keta surutanshi acikin motar dankuwa Kawu idrissa gaba ɗaya yayi nisa acikin duniyar tunani. A garrage ɗin gidan Kawu Adamu yayi parking motar sannan suka fito bakidayansu,kasancewar dare ne Kuma har goma tawuce yasa basu tsaya wani dogon surutai ba sukayi ma juna sallama ayayinda kowannensu yawuce sashinsa.

A parlour Kawu idrissa ya tarda wasu daga cikin yaransa suna kallo ayayinda wasu daga cikin su most especially yan pici picin duk sunyi bacci anan parlourn suma,da alamadai suna cikin kallone baccin yayi awun gaba dasu.

Waɗanda idanunsu biyu harlokacin suna ganin yashigo parlourn duk suka gaidashi tareda yi masa sannu da zuwa ayayinda ɗaya daga cikin yara mazan yazo yakarbi babban rigarsa da eyes glasses ɗinsa daya riƙo a hannu suka shige ciki. Maman Rabi'u koda yaran suka sanar da'ita dawowan Baban nasu bataje yimasa sannu da zuwa ba harsaida ta tabbatar tashigar da kananun yaranta ɗaki tasakasu sukayi fitsari suka kwanta sannan tafito takora Samarin boys quarters wurin Ƴan uwansu maza inda matan kuma tace suma suwuce ɗaki su kwanta dare yayi. dukda cewa Maman Rabi'u macece me son abun duniya dakuma ruling mijin somehow,hakan besa tayi wasa wurin bama yaranta tarbiya mekyau ba,they always respect their elders hakanan duk abunda taɗaura su akai shi sukeyi. Tsaye take akansu sosai wurin ganin they always behave wanda wannan na ɗaya daga cikin abunda yasa Kawu idrissa kesonta dakuma kaunarta daga ita har Ƴaƴan nasu.

Sanda tashiga ɗakin haryayi shirin kwanciya shikam, ƙarasawa tayi bakin gadon tazauna tareda faɗin "Sannu da dawowa Baban Rabi'u" Kawu idrissa yamikar da kafafunsa sosai akan gadonsa sannan yace "Yauwa sannu" tace "Yau naga baku dawo dawuri ba harma nayita ƙiran layinka inji ko lafiya bansameka ba" murmushin yaƙe Kawu idrissa yayi sannan yace "Munacan gidan rasuwar ne ana tattaunawa kan batun inda Rukayya zata zauna seyanzu muka gama shine muka taho gida" aitunda Maman Rabi'u taji an anbaci sunan Rukayya kuma hankalinta yakoma kan maganar dungurugun tace "toh yanzun yakuka kare?wace magana kuka tsaida?" Kawu idrissa yace "suka tsaida dai danni kwata kwata tunfarima ƙin ɗaukan shawarata akayi dana bada shawara" kwafa Maman Rabi'u tayi sannan tace "Sani ne dawannan aikin koh?" Cikin sauri Kawu idrissa yace  "Aikuwa kamar kinsani. Shine yafara magana ma" Maman Rabi'u takyabe baki sannan tace "nasan za'a rina ai. wato shi yanaganin yayi kuɗi yanason yanuna yafi kowa sanin yakamata. Toh yanzun mekuka yanke? Shiɗin meyace daman?"

Ɗan numfasawa Kawu idrissa yayi sannan yabata labarin duk yanda sukayi acan gidan rasuwar kafin daga karshe yafaɗa mata cewa sunyanke hukunci Rukayya zata zauna agidan sa. aiko ko rufe baki bekai gayiba Maman Rabi'u ta katseshi tahanyar cewa "Waaaa? Rukayyan ne zata zauna agidannan?toh wallahi bazata sabuba Baban Rabi'u! kakuwa san mehakan ke nufi?" Girgiza matakai yayi alamar A'a sannan tace "indai Rukayya zata zauna agidannan toh tabbas burin mu bazai taɓa cika ba danbayan fitar ka dasafe Hajiya Jummai tazo munjemu wurin boka kuma nafaɗa mishi komai and he told me bamatsala komai zaitafi yanda akeso anma karmu yadda mubarta agidanmu,inda so samune ma karmu zauna da ita agari ɗaya inbahaka ba akwai consequences. Dan akwai wanda already yana cikin rayuwarta yanzu haka and he can go to any length for her happiness,he's her soulmate,bashida burin daya wuce yafaranta mata hakanan babu abunda bazai iyayima wanda yace zai kuntata mataba kuma har tambayarshi nayi akan yaron anma seyace min daya duba fuskarshi is not visible hakanan ko iskanunshi sun kasa gane wanene shi. Kuma mahaifiyar sa a tsaye take wurin yimasa addu'a bare suce zasu iyayi masa wani abu shiyasama abunda bazai yuyu ba kar afarashi Baban Rabi'u" Kawu idrissa yace "ikon Allah toh wanene wannan yaron haka damu bamu sanshi ba?" Maman Rabi'u tace "Nima bansaniba Baban Rabi'u kuma in akwai wanda yakamata yasani aikune tunda kukuke ganin yarinyar kullum" Kawu idrissa yace "nidai ban taɓa cin karo da wani yaro daban dasunan yazo ganin Umar tahanyar Rukayya ba. Kuma shi bokan bece miki acikin dangi yaron yakeba?" Girgiza kai Maman Rabi'u tayi sannan tace "be faɗamin ba gaskiya" Kawu idrissa yace "toh shikenan zantambayi Adamu inji koyasan yaron" Maman Rabi'u tace "nifah duk wannan baya gabana Baban Rabi'u. damuwana shine asan yanda za'ayi acanza maganar Rukayya zatazo gidannan. kanadai gani tun ba'aje ko'ina ba har kaninka yafara nuna shine sama dakai sabida yafi ka kuɗi. Wai dan feleke da bushewar idanu har Sani ne zaka kawo shawara yace naka baiyiba nashine dede" ajiyar zuciya Kawu idrissa yayi sannan yace "toh yanzudai miye abunyi dan na riga na amince musu kan zanrike Rukayyan kuma gobe zanje in ɗauketa" Maman Rabi'u tace "kawai goben karkajeka,kosun kiraka kada ka daga" Kawu idrissa yace "ai wannan kuma ba solution baneba dan kobanjeba za'a iya kawota har gida" Maman Rabi'u tace "kadaiyi musu hakan insun kawota gidan seka fito barau barau kanuna kaifa bakason riketa sannan kaja Adamu kutafi kasuwa gobe kokaturashi Giyaɗe yimaka wani aiki yanda bazaisan me ake cikiba danshikam uban Ƴan tausayine yanzu seya ɓata mana budget bayan kuma kuɗin nan harda shi zai amfana in akasamu cigaban tunda kominku tare yake" Kawu idrissa yace "toh shikenan hakan za'ayi. Kawai ma zanturashi Kano sarin kaya gobe"

QADRWhere stories live. Discover now