Part 1: Introduction

454 23 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤

ROYAL CONSORT
(Historical fiction)

©️ marriam mayshanu.... ✍️

Labarin ROYAL CONSORT labarine irinshi na farko a cikin labaran hausa novel,labari ne na tarihi amma wani bangaren labarin qagagge ne,labarin ya qunshi mulkin mallaka,tsantsar qauna,tasirin qarfin iko,mugunta,rashin adalci,sadaukarwa da sauransu.


❤️ Part 1 : Introduction

Masarauta ce mai fadi da girman gaske,domin zaifi sauqi a kirata da gari guda,masarauta ce mai tarihi da tsari mafi birgewa a yadda suke tafiyar da al'amuran mulki da rayuwar yau da kullum.
Sai dai matsalar guda d'aya ce tak,suna amfani ne irin tsarin nan na mulki da tantancewa tsakanin talaka da mai kud'i,hakan ne yasa kowa yake da kwad'ayin kasancewa a cikin mutane masu alfarma,domin kuwa hakan ne kawai zai iya tseratar da kai da ahalinka daga dukkan wata barazana.
Idan har mutum ya kasance da jinin talaka a jikin sa,to zai zama abin qyama ne a cikin al'umma,kuma ba zai samu sakewa ba sai dai a cikin talakawa 'yan uwansa.
Wani 'bangaren kuma zamu iya cewa duk wanda ya kasance a cikin wad'anda ake mulka to tamkar bawa ne a wajen sarki,domin mulkin mallaka akeyi,laifi kad'an ne ko wanda bai kai ya kawo ba zai iya sawa mutum ya rasa ransa.
Domin kuwa babu gwamnati balle kuma demokrad'iyya,masarauta ce take mulkin kowa da komai,kama daga jami'an tsaro,kotu,haraji,da sauran su.
kasancewar a haka suka tashi sukaga al'ummar su shiyasa basu d'auki hakan a wani nau'i na zalinci ba,sai dai sun yadda da cewar wajibi ne a garesu su yi wa sarki da iyalansa biyayya sau da qafa domin tsira da rayukansu.
Har ila yau a wannan masarauta,doka tana aiki akan kowa komai matsayinsa kuwa,matuqar dai an samu hujjar cewa an aikata laifin to kuwa ba zai tsallake hukunci ba,hakan yasa duk wanda ya aikata wani laifi zaiyi qoqarin ganin ya rufe kuma ya toshe duk wata hanya da za'a samu hujja a kansa.
Masautar tana da FADA guda biyu ne akwai fadar sarki mai martaba wato (Grand palace) inda nan ne sarki yake ganawa da fadawansa,da kuma fadar sarauniya,wannan fadar cikin gida ce da ake kiranta da (inner court) wannan fadar itace qarqashin ikon sarauniya (Queen) wato matar sarki ta farko,itace take mulkin cikin gida (pavillion of women: inda babu wani namiji da yake iya shiga sai da izini) a qarqashinta akwai sauran matan sarki da duk wata 'ya mace da take cikin masaurautar,kama daga bayi (servants) har masu aikace aikacen cikin masarautar (Palace maids) haka nan kuma tana da office din bincike na musamman (office of investigation) wanda shima mata zallah ne a ciki da ake kiransu da (investigator ladies) wanda sunfi ko wacce palace maid matsayi a cikin gida saboda yanayin aikinsu yana buqatar baiwa da ilimi na musamman.
A tsarin wannan masarauta,Matar sarki ta farko ce kawai take da haqqin a kirata da sarauniya (Queen) inda duk wata mata da sarki zai samu bayan nan za'a kirata da (Consort) kuma suma ko wacce da matsayin ta daidai da yadda sarautar ta yazo,hakan yasa ba matsayin su daya da sarauniya ba,zasu kasance ne a qarqashinta kuma masu biyayya a gareta.haka nan kuma sarki yana da damar da zai nemi duk wacce yake so cikin palace maids ya mayar dasu qwarqwara (concubine)domin suna qarqashin ikonsa ne,hakan ne yasa basu da damar da zasu qulla alaqa ta soyayya da wani namiji domin hakan laifi ne mai girma.
Inner court din sarauniya tana da wasu jerin mata da ake kira da (court ladies) wanda su suka hada da sauran matan sarki,qwarqwarorinsa,da kuma palace maids da suke da babban matsayi a masarautar.
A tsarin masarautar duk wani abu da ya shafi inner court to fa sarki bashi da ta cewa a wajen,sarauniya zata sa ayi bincike kuma ta yanke hukunci,kuma idan har sarki yana buqatar wani abu da ya danganci inner court sai dai ya bawa sarauniya shawara ko kuma ya nemi alfarma a wajenta amma ba umarni ba,domin umarnin sarki baya amfani a inner court.
A cikin 'yan matan masarauta akwai biyayya mai qarfin gaske,yadda ko yaya mutum ya fika sai kayi masa biyayya,kuma kaucewa wannan sharadin laifi ne mai girma. Kuma duk wata matar sarki babu wanda ya isa ya kirata da sunanta ko da kuwa iyayenta ne,domin doka zata iya hawa kansu,sai dai da sunansu na girmamawa.
A tsarin magadan sarauta kuwa,'ya'yan sarki maza ana yi musu sarauta kamar yadda yawancin masarautu sukeyi,babban d'a wanda mafi akasari shine yarima mai jiran gado(crown prince) sauran kuma duk wani d'an sarki namiji ana kiransu da (Grand prince)
'Ya'ya mata ma suna da nasu yanayin sarautar saidai babu su a gadon sarauta.
Sarautar crown prince sarauta ce da ake bata matuqar muhimmanci domin a tsarin sarautar daga sarki(His majesty the king)sai mahaifiyar sa (queen dowager) sai sarauniya Her majesty The queen)sai crown prince,duk consorts suna kasancewa qarqashin crown prince ne duk da matan babansa ne domin yafi su kusa da sarauta,akwai biyayya a tsakaninsu ko da kuwa shi crown prince din consort ce mahaifiyarshi ba sarauniya ba.
A tsarin kayan sawa kuwa,sarki,sarauniya,da kuma crown prince suna rufa alkyabba a jikinsu a cikin kowane yanayi a cikin masarauta,kuma alkyabbarsu na d'auke da zanen dragon ne a jiki,wanda babu wanda yake da ikon saka alkyabba mai zanen dragon sai su ukun nan kamar yadda aka qawata karagar mulkin qasar (Royal throne) da wannan zanen dragon 🐉
Hakanan suma consorts da irin nasu design din alkyabbar,a doka su kad'ai suke iya saka alkyabba mai adon zaiba (golden and silver) inda mai adon golden a alkyabbarta tafi mai adon silver matsayi na sarauta,wanda ko wanda bai sansu ba,wannan kayan kawai zai kalla yasan matsayinsu.

Haka nan ko wane matsayi na court ladies akwai irin kayan dasuke amfani da ita,domin tantance kowa da matsayinsa a fadar.
Special court ladies a matsayin matan sarki suke suma domin sun yi daban da sauran court ladies,suna samun matsayin special court ladies ne idan sarkin ya neme su a shimfida hakan yake sawa matsayinsu ya canja a dare guda,ana basu masu aikin su,quaters dinsu daban,da sauran masu yi musu hidima.

Royalty 👸

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now