Page 11

66 4 0
                                    

Page 11

Queen dowager ce a kwance a dakinta cikin wata doguwar rigar bacci,gashinta ma a warware,kitse jelar gashin kawai akayi yayinda queen haneefah take zaune da wani baho a gabanta da kuma duster tana tsomawa tana matsewa tare da gogewa queen dowager jiki,dayan bangaren kuma royal doctor ne a tsugunne kanshi a qasa,sai royal nurses guda biyu a bayanshi suma sunyi irin zaman da yayi.

fuskar queen haneefah fal damuwa ta furta

"Sannu maama,Allah ya baki lapia"

Cikin jin jiki dowager tace

"Yauwah sannu queen,nagode da kulawarki,Allah yai miki albarka"

Murmushi queen haneefa tayi duk da damuwar bata bar fuskar ta ba tace

"Ai aiki na ne na kula dake maama,kiyi shiru Allah dai ya baki lapia"

"Ameen ta furta can qasa qasa" tare da lumshe idonta bacci ya dauketa sanadiyyar maganin da aka bata yanzu.



Shukra tana tafe har unguwar da aka kwatanta mata nanne unguwar su lady jalila,tambaya tayi aka nuna mata gidan,da sallamarta ta shiga gidan,wata maid ta tarar a tsakat gidan tana ta kai kawo,jin sallamar shujra yasa ta tsaya don ganin mai shigowar,a hankali shukra take turo kai cikin gidan da ganin maid din ta dan rusunar da kanta kadan tare da cewa

"Barka da warhaka,lady jalila ce ta turo ni" da jin haka maid din murmushi kawai tayi ba tare da ta cewa shukra komai ba ta nufi qofar sitting room haj jameela,jim kadan suka fito tare,shukra da ganin ta ta rusuna tare da cewa

"Barka da war haka,sunana shukra" wani kallon wulaqanci haj jamila ta bita da shi tare da cewa

"Fuskar ki ta nuna min hakan,ba sai kin gabatar da kanki ba"

Nan take shukra ta sha jinin jikinta,haj jamila da maid dinta ne suka fita shukra tabi bayansu har wajen mai magani.

Da zuwansu gidan mai maganin haj jamila ta shiga ciki ta bar shukra da kuma maid dinta a tsakar gida,da shigarta mai maganin ya miqe daga inda yake zaune tare da rusunawa ya gaishe ta

"Barka da zuwa madam"

Ba tare da tace komai ba ta nemi waje ta zauna,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kafin daga bisani tace

"Ina fatan maganin ya kammala ko?" Ta fada tana me dubanshi,gyaran murya yayi

"Ehh ana hadawa amma sai zuwa qarfe takwas na dare zai kammala"

Gyada kai tayi tare da cewa

"Ina tare da yarinyar da zata karba,ka tabbatar ba'a samu wata matsala ba,kuma idan har buqata ta biya kana da kyauta mai tsoka"

Washe baki yayi cike da farin ciki yace

"Ai ba za'a samu matsalar komai ba madam"

Tsam ta miqe ba tare da ta qara ce masa komai ba ta fito inda ta tarar da su shukra,sai da tazo dab da shukra sannan ta rage murya tare da cewa

"Ki jira zuwa qarfe 8 sai ki tafi da saqon,Ki tabbata ba'a samu ko wace irin matsala ba,kuma kada ki bari kowa ya ganki,ina fatan kin fahimta"

Cike da ladabi shukra tace

"Na fahimta madam"

Barin shukra tayi anan suka wuce ita da maid dinta.

Waje shukra ta samu ta zauna domin jiran saqon wani mutum ya shigo karbar magani,har ya karbi maganin shi zai wuce daidai inda take ya yarda qulli daya,shukra ce ta tsugunna tare da dauko qullin tace

"Baka ji ba"

Juyowa yayi ya kalleta tace

"Ka yar da wannan" ta fada tana miqa masa qullin maganin da ya yar a qasa,saurin karba yayi tare da cewa

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now