Page 59

84 5 0
                                    

Page 59

"Dama akwai abinda nake son fada miki game da mai martaba,zan ari bakinshi ne in ci masa albasa" cikin rashin fahimta shukra take kallonta,karkata kai queen haneefah tayi
"Ko baki san da cewar mai martaba ya fada soyayyarki ba?" Zaro ido shukra tayi tare da girgiza kai tace
"Your majesty! Dn Allah kar kice haka"
"Shukra kenan! Ki saurareni da kyau kiji me zan fada miki! Ba komai ne yafi damuna ba face ina tunanin kinqi bashi dama ne saboda ni,amma bana son kiyi haka! Idan har soyayyar mai martaba zata baki farin ciki to ya zama dole ki karbeta"
Shukra har zabura take tace
"Your majesty..."
"A'ah shukra,ni kaina akwai lokuta da dama da naso ace na zama cikakkiyar mace a rayuwarshi ba wai sunan sarauniya kawai ba,amma a yanzu bana jin haka domin na dade da fahimtar cewa babu wajen zamana a cikin zuciyarsa! Kuma ba kowa bane yake da mallakin zuciyarsa face ke! Shukra! Saboda haka ya zama dole na fada miki ki fara shirin kasancewa da shi"
"Your majesty! Hakan ba zai taba yiwuwa ba,Ni wacece da na isa aikata hakan?darajata bata kai haka ba your majesty" Shukra ta fada cikin rawar murya
"A'ah hakan ba gaskiya bane shukra! Domin mai martaba ya dade da daga darajarki,ya dade da mayar dake ishashshiyar da zata mallaki zuciyarsa" Sunkuyar da kai shukra tayi cikin rashin sanin abin cewa
"Saboda haka kada ki qara bata lokaci,ki karbi soyayyar mai martaba cikin farin ciki da aminci,kuma kema ki bashi taki soyayyar........Wannan shine roqona a gareki a matsayin sarauniyar wannan qasar" ta qarasa maganar da murmushi akan fuskarta amma kuma tana hawaye,shukra ma hawayen takeyi kanta a qasa domin maganar tayi mata nauyi sosai,sanyin da jikinta yayi ne yasa ta kasa zuwa tribunal kawai ta dawo gidan da take,ai kuwa tana shigowa taci karo dashi
"Tsaya ke! Ke wai meyasa bakya jin magana ne? Ko dai kawai an haifeki ne domin ki dinga daga min hankali? Ba nace kada kije ko'ina ba?" Murmushin yaqe tayi
"Cheo-nah! Yaushe kazo nan din?" Hararar wasa yayi mata
"Yaya ba zanzo ba? Ko kina tunanin ba zan san cewar kin fita yawo neman magana ba? Yanzu kuma kinji tsoro ne saboda na kamaki dumu dumu ko?"
Rusunar da kanta tayi
"Ba haka bane! Ka gafarceni your majesty,Na san fitar tawa akwai hatsari amma akwai inda ya kamata naje ne"
Jinjina kai yayi
"Ai ke dama ba za'a taba gaya miki magana kiji ba,ba kya tsoron komai! ai nine shashashan ma da nayi tunanin zaki zauna kibi duk abinda aka ce miki a gidan nan" ya fada yana kallon can gefe
"Ba haka bane your majesty!" Ta fada kamar zatayi kuka,kallonta yayi
"Ba komai! Manta kawai tunda yau kin tsallake wata masifar sanadiyyar rashin yi min biyayya,shikenan kinga yanzu ba zan ma iya cewa lallai sai kinji maganata ba!"
"Your majesty me kake nufi da hakan?"
Qin fada mata yayi,ya wayance da maganar kawai,fita sukai suka shiga cikin gari tare zuwa inda suka saba zuwa shan shayi.

Chief Suh ne da abdullahi a zaune,chief Suh yace
"Akwai abinda mai martaba ya bani umarnin sanar dakai! Sun fita tare da Shukra zuwa shan iska amma akwai abu mai muhimmanci a matsayinka na yayanta,yana son ka kalli abin a matsayin kariya ga rayuwarta ne...."
Bayani yayi masa sosai abdullahi ya fahimta,hada kai sukai domin fara shirye shiryen abinda yake gabansu.

Suna hirar su cikin nishadi suna ta dariya,shukra ce ta tsaya da dariyar
"Your majesty! Akwai abinda nake son sanar da kai" kallonta yayi tare da yi mata alamar tayi magana
"Na san abinda ya faru yau!" Zaro ido yayi yana kallonta
"Ina son na koma cikin masarauta domin na cigaba da aikina" girgiza kai yayi
"A'ah ke bakya tsoron abinda zasu iya yi miki? Bayan zaki koma ne a matsayin palace maid wacce bata da wani qarfi ko iko?" Girgiza kai tayi
"Ni ai yanzu bana jin tsoron kowa! Na san zaka kareni! Kuma kaima kana nan a cikin palace din" girgiza kai yayi
"A'ah shukra"
"Ni dai bana jin tsoro! Ina da mai martaba a tare dani waye ya isa yayi min barazana?"
Dariya ta bashi yadda tayi maganar,sai ya danyi murmushi
"Ka taimaka ka bani izinin komawa palace don in taimaka maka ta hanyar da bata fi qarfina ba"
"Saboda ni kika ce?"
"Ehh ina son na koma office of investigation domin na taimakawa palace maids da bayi marasa gata irina,kuma zanyi hakan ne saboda kai! Tunda ina tare da kai babu wanda ya isa ya taba ni" haka dai tai ta masa dadin baki saboda ya yadda,Ajiyar zuciya ya sauke
"To naji! Zaki koma amma tunda kince zakiyi komai saboda ni ne,to nima akwai abinda nake son yi saboda ke! Ina fatan an bani izini"
"Menene shi?"
"Abinda zai sa na iya baki kariyar da ya kamata" ba tare da ta nemi qarin bayani ba kawai ta bashi izini.

Bayan ya raka ta gida shima ya koma palace,takalmin da yasa akayi mata ya dauko yana dubawa,shafa takalman yakeyi chief eunuch ya sanar masa da cewar chief secretary ya qaraso,shigowa yayi ya tsaya tare da rusunawa
"Gobe da safe! Ina neman dukkan ministoci da hakimai a fada" Umarnin da ya bayar kawai kenan,ba tare da ya bashi damar yin tambaya ba,rusunawa yayi
"Yea cheo-na!" Yace sannan ya fita.

Waahegari da safe chief eunuch ya shigo cikin gidan da shukra take cikin tsananin farin ciki,a garden din da ta saba zama ya sameta,rusunar da kanshi yayi a gabanta sannan yace mata
"Mai martaa yayi umarnin komawarki cikin masarauta yanzu-yanzun nan"
Cike da murna tace
"Da gaske? Zan koma yanzu?" Kai ya daga mata tare da nuna mata wasu kwalaye guda biyu,hannu ta miqa zata karba ya hana ta
"Ki nuna min inda zan kai in ajiye miki su" dakinta ta nuna masa,ya shiga gaba ita tana baya,wajen zama ta nuna masa tare da zama itama ta bude babban kwalin,ido ta zaro ganin abinda yake ciki,ta dago ta kalle shi tace
"Ni? Menene wannan chief eunuch?"
"Kyauta ce daga mai martaba! Kayan sawarki ne idan zaki koma cikin masarauta" a tsorace ta kalle shi
"Amma ai ba zan iya saka wannan kayan ba,wannan ai alkyabbar..." kasa qarasawa tayi kawai ta saki baki,shi kuwa yaga ba huruminsa bane yi mata bayani hakan yasa ya tashi ya fita ya barta cikin rashin fahimta.

Sameer ne ya taho da gudu yana qwalawa manager kira
"Yallabai! Yallabai!! Shukra ta dawo! Ta dawo!!" Manager da yake kallon yadda fuskar sameer take a yamutse yace masa
"Ina tausayin yarinyar nan! Yanzu tana ji tana gani ta tunkari mutuwarta da kanta?" Yarfe hannu sameer yayi
"Yallabai ba ma wannan ba fa! Ka san abin mamakin da na gani? Ka san wane kaya ne a jikinta?" Runtse ido manager yayi
"Yagaggun kaya ta saka ko? Da sarqa aka daure ta?"
"A'ah a'ah ba haka ba,kayanta.... Kayanta..." murde masa kunne manager yayi
"Fadi mana! Fada min me kayanta sukai?" Kunnen nasa ya riqe da yake masa zafi,manager yana sakin kunnen nasa ya ce masa
"Ai na fasa fada maka ma!" Juyawa yayi yayi tafiyarsa,manager yana ta qwala masa kira amma inaaa! Yayi nisa.

Dukkan hakimai sun taru a fada,mai martaba yana zaune kan dragon throne dinsa sai muzurai yake yana kallonsu daya bayan daya
"Naji abinda kuka ce! Na yadda ku binciki palace maid Shukra Malak" kallon kallo suka fara yi cikin mamaki,wasu suka fara qus qus
"Amma sai dai akwai wani abu da ya kamata ku sani" ya fada yana qirqirar murmushi,dukkansu kallonshi sukeyi suji me zai fada
"Ina son in sanar daku cewar a halin yanzu Shukra ba lady investigator bace" hakiman kudu murna suka fara yi jin abinda mai martaba ya fada,kenan ya cireta daga lady investigator saboda wataqila shima yanzu yana kokonto akanta kenan,da murmushi ministan tribunal yace
"Your majesty me kake nufi da a yanzu ita ba lady investigator bace?" Fuskarsa a cukule yace
"Daga yanzu,zaku dauki palace maid din da kuka sani Shukra Malak a matsayin special court lady wacce take da alaqa da sarkin qasar ku!"
Gaba daya bakinsu mutuwa yayi,da qyar ministan tribunal ya iya cewa
"Alaqa da sarki kuma? Me kenan?"
Idon jameel yayi wuri wuri shima,haka sauran hakiman kudu,yayinda hakiman arewa mamaki ne ya cika su qwarai.

Ta shirya tsaf cikin kayan da aka kawo mata,tana fitowa ta tarar da palanquin mai matuqar kyau da ado,sai mazan da zasu dauketa a ciki,sai mata palace maids guda 6,chief eunuch shima yana wajen yana jiranta tare da wasu eunuchs din guda biyu,sai tawagar abdullahi kuma da zasuyi mata rakiya.

Alhamdulillah
End of part 3
Part 4 will be THE ROYAL CONSORT.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now