Page 53

76 3 0
                                    

Page 53

Sun ratsa daji suna ta gudu sosai,naseer ne ya fadi a qasa,ta juyo
"Ka tashi mu qara gaba! Mutanen jaleel zasu iya kama mu,ka tashi" huci yake tayi tsabar gajiya yace mata
"Ai sai dai in mutu a nan,amma ba zan qara ko taku daya ba,ki tsaya mu huta mana,don ni gaskiya na gaji" sama ta kalla kamar mai tunani can kuma sai ta qyalqyale da dariya,hararar ta yayi
"Ni kikeyi wa dariya ko?" Girgiza kai tayi
"A'ah kawai abinda kayi ne sai ka tuna min da wani dan sandan sirri dana sani,shima bai iya gudu ba kamar ka"
"Ni ai ba gudun ne ban iya ba,ke dince saurin ki yayi yawa" murmushi tayi
"Amma abin yana damuna idan na tuna cewar registration archive dinnan yana hannun jaleel,na san yanzu ma ya bawa mutanen china sun tafi dashi" ajiyar zuciya ya sauke
"Kinga kenan na ci amanar qasata saboda na tseratar da rayuwar ki" gefe ta kalla
"Hakane! Amma shin rayuwata har takai darajar haka? Ina jin kamar munyi wa qasarmu babban laifi" kallonta yayi
"Ni zanje wani waje,ki tafi inda kukayi magana da sulhee"
"Kai kuma yanzu ina zaka je?"
"Kada ki damu dani! Kije kawai!" Kafin ta qara yi masa wata tambayar ya bar wajen da gudu,hakan yasa bata da wani zabi sai itama ta tafi inda ta nufa.

Jaleel cikin tsananin kidima da tashin hankali,ya rasa inda zaisa rayuwar sa,luqman ne ya qaraso shima baya cikin nutsuwa yace
"Yallabai! Akwai saqo daga masarauta,queen tana buqatar ka a can,yq kamata kayi gaggawar komawa" yana tsaye qiqam ya dayse haqoransa tsabar bacin rai yace
"Yanzu babu sojojin da zamuyi amfani dasu wajen neman shukra da naseer?" Jinjina kai luqman yayi
"Babu yallabai! Dukkansu suna kan umarnin mai martaba ne" girgiza kai jaleel yayi
"Yanzu yadda chief Suh yazo da wannan imperial dispatch seal din,babban hatsari ne mu tunkare shi a cikin garin nan,don idan yace a cire min kai,cire min za'ayi nan take! Domin tamkar umarnin mai martaba ne! Ni zan tafi amma ka tabbatar kun nemo shukra da naseer kun gama min dasu"
"Yes sir" luqman amsa masa.

Sulhee da shukra sai masinjan sulhee tsaye akan jirgin ruwa sai kalle kallen ta inda naseer zai bullo sukeyi,shukra ta kalli sulhee
"Kiyi haquri,na saki barin garin uiju saboda ni!" Girgiza kai tayi
"A'ah ba komai shukriyya,ai na ma fara gajiya da zaman garin" kafin shukra tace wani abu suka hango naseer,yana qarasowa shukra tayi saurin ce masa
"Yauwa,yi sauri ka hawo jirgin mu tafi" girgiza mata kai yayi
"A'ah ni ba inda zani! Ku tafi tare da sulhee" yamutsa fuska shukra tayi,yace
"Kinsan ina nan garin ne a kan umarnin mai martaba,kuma ba zan iya barin nan duk sanda naso ba" jinjina kai tayi,wani abu ya miqo mata a nade a cikin qyalle
"Karbi wannan! Kyauta ce na baki daga wajena" bata karba ba tace masa
"Menene wanan?"
"Wannan shi zai ceci rayuwarki sannan kuma nima shi zai wanke laifina a yafe min kuma mai martaba ya bada umarnin na koma bakin aikina" karba tayi ta riqe amma bata bude ba,kallon rashin fahimta tayi masa,haka ma sulhee
"Wannan original din Registration archive ne!" Naseer ya fada musu,Bude baki sukai ita da sulhee da mamaki tace
"Kenan littafin da ka bawa jaleel..."
"Littafin da ake shigar da shige da ficen jami'an tsaro ne na puongyang,bango kawai na canja musu,da yake shima jaleel din jahili ne baisan yadda littafin yake ba shiyasa bai gane ba" cikin farin ciki shukra tace
"Amma kayi dabara yallabai! Na san idan suka je china suka gane cewar ba'a basu abinda suke buqata ba ba zasu bayar da sahalewar matsayin yarima mai jiran gado ba,kuma hakan zai batawa su jaleel aikinsu" jinjina kai yayi
"Hakane! Ya kamata ku hanzarta ku bar nan,kin san muhimmancin kula da lafiyarta ko? Ki kula da ita sosai dn Allah" ya qarasa maganar yana kallon sulhee,rusunar da kanta tayi alamar taji,shukra ma ta rusunar da kanta sosai can qasa kamar mai tafiya ruku'i tayi masa godiya,yana tsaye har jirgin nasu yayi nisa ya daina ganinsu.

Bayan sun sauka,wani gidan saukar baqi suka nufa a wani qauye da yake bayan gari,kasancewar madam din gidan qawar sulhee ce yasa basu wahala ba,kuma zamansu a wajen ya zama sirri har lokacin da zasu samu yadda zasuyi su shiga cikin garin joshun,don garin a akewaye yake da ganuwa da kuma qofofi guda hudu.

JOSHUN CAPITAL
GRAND PALACE

Chief eunuch ne ya shigo ya sanar da mai martaba zuwan IG,cikin qaguwa da farin ciki mai martaba yace
"Ka shigo dashi"
Yana shigowa mai martaba ya miqe daga inda yake zaune,da murmushi a fuskarsa yace
"Barka da dawowa! Ina shukra? Ka sameta?" Shiru IG yayi tare da sunkuyar da kansa qasa,ya kasa hada ido da mai martaba,ganin yanayinsa yasa murmushin fuskar mai martaba ya ragu
"Kayi min bayani! Ina shukra?" Bai dago kansa ba yace
"Munje har garin,amma kafin mu qarasa yayan queen jaleela wato superidendant of police jaleel ya dauke ta daga inda akayi mata masauki a garin,daga nan kuma babu wanda ya san inda take,kuma akwai shaidun gani da ido a lokacin da ya kamatan" ran mai martaba ne ya baci sosai,yace
"Jaleel kuma? To meyasa zai dauke ta?"
"A tunanina dalilin dai guda daya ne,shine dalilin dai da ya sa ta bace daga masarauta" IG ya bashi amsa,cikin kakkausar murya da take bayyana tsananin bacin ransa yace
"Zan sa a kawo min shi nan yanzun nan yayi min bayanin dalili! Chief eunuch!!" Ya qwalawa chief eunuch kira har wani zabura yakeyi tsananin bacin rai,IG ne ya rusunar da kanshi sosai yace
"Ka gafarceni your majesty! Amma yanzu ba lokacin da ya dace ka tambayi jaleel bane,don idan ka tambayeshi zai baka wani uzurin daban,zai ce maka ya kamata ne saboda laifin qona record room din royal treasury kuma ta gudu kamar yadda suka qulla mata,kuma babu yadda zamuyi da hakan tunda bamu da hujjar da zamu qaryata shi! Yanzu abinda yafi muhimmanci shine mu nemo shukra mu tabbatar ta tsira daga garesu,kuma har lokacin da zamu sameta,kada kayi maganar nan da kowa" jinjina kai mai martaba yayi kawai,ji yake kamar ya kamo jaleel ya sare masa kai yanzu yanzun nan,jinin jikinshi tafarfasa yakeyi tsabar bacin rai,sallama IG yayi masa ya tafi domin dorawa da neman shukra daga inda suka tsaya.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now