Page 40

66 4 0
                                    

Page 40

Shukra da gudunta ta tafi grand palace amma guards suka hana ta shiga,zama tayi a wajen har dare ya qara yi sosai,chief eunuch ne yazo wucewa,da hanzari ta tashi ta tare shi,sai da ta gaishe shi sannan ta fada masa tana son ganin mai martaba,amma shima ya bata amsa da cewar ba zai yiwu ba domin mai martaba yace babu wanda zai gani a cikin daren nan,suna cikin haka tana qoqarin roqon shi ko zai taimaka ya kaiwa mai martaba takaddun da ta kawo,sai ga IG,sai da ya gaishe da chief eunuch sannan yazo kusa da shukra daidai kunnenta yace
"Ki dakata haka! Kada ki aikata abinda kike qoqarin yi,gobe da safe kizo ki sameni a office" juyawa yayi ya tafi,yayinda itama cikin sanyin jiki ta tafi daki domin ta kwanta,idonta a bushe har gari ya waye,cikin shirin ta na uniform din lady investigator ta shirya tare da zuwa office din IG,tattaunawa suka farayi yana fada mata dalilin da ya sa ya dakatar da ita daga nunawa mai martaba wanan hujjar,cikin rashin fahimta tace masa
"Yallabai kana nufin na boye wannan hujjar kenan? Bayan za'a sauke queen haneefah ba'a kan qa'ida ba?" Jinjina kai yayi
"Ehh haka nake nufi domin yanzu mun riga mun makaro,kuma sannan a halin yanzu bangaren arewa sun riga sun rasa qarfin ikon su"
Girgiza kai tayi
"Amma yallabai zamu binne hujjar da muke da ita ne domin tsoron bangarencin kudu? Ko domin bangarencin arewa sun rasa qarfin iko?" Jinjina kai yayi
"Ehh haka nake nufi,domin a cikin wannan lokacin,hakiman kudu ba zasu taba bari a yi wani sabon bincike ba,kuma hakan zai sa suyi mana abinda ba zamu qara cigaba da abinda muka saka a gaba ba,tunda yanzu suna ganin sun samu nasara,mu qyale su da nasarar su,mu kuma muna qara bincike a qarqashin qasa ba tare da hankalinsu ya kawo hakan ba" hawaye ne ya zubo akan fuskar shukra
"Shikenan yallabai,haqiqa qarfin iko abin tsoro ne,amma bana tunanin qarfin iko zaifi qarfin gaskiya"
"Maganarki haka take shukra,qarfin gaskiya yafi qarfin iko,amma kuma qarfin iko yana iya danne gaskiya duk da ita gaskiyar bata bata,komai daren dadewa zata fito,ina son kiyi haquri a wannan lokacin domin mu samu dama ta gaba"

A durqushe take a gaban queen haneefah tana ta kuka,murmushi queen haneefah tayi
"Shukra! Ki daina kuka,kin fi kyau idan kina murmushi,kuma bana son na tafi na barki kina kuka! Ai zaki yi min murmushi kafin na tafi ko?" Dago kai shukra tayi fuskarta duk ta baci da hawaye,amma ta kasa cewa komai,murmushi queen haneefah ta qara yi mata
"Kiyi haquri,abinda IG ya fada miki nima shi nake son na fada miki,kiyi haquri a wannan lokacin,zuwa nan gaba zamu fi samun nasara sosai,domin a halin yanzu babu duk wata yarda da take tsakanina da mai martaba,ya riga ya sare da al'amari na,hakan ne zaisa ba zai dauki hakan da wani muhimmanci ba,amma na tabbata ba zasu tsaya a haka ba,dole nan gaba zasuyi abinda zai fito da halinsu qarara" sunkuyar da kai shukra tayi gaba daya tausayin queen haneefah ya lullube ta
"Kiyi haquri shukra! Ki daure a wannan lokacin saboda ni! Kiyi min alqawarin ba zaki sa damuwa a ranki ba,kiyi min alqawari!" Hannu shukra ta saka ta goge hawayen fuskarta,tare da kallon queen haneefah
"Your majesty! Ke zan bawa haquri,kiyi haquri! Amma ba zaki jira har lokaci mai tsayi ba,nayi miki alqawari" murmushi queen haneefa tayi
"Nagode shukra,sannan kuma ina son ki kula min sosai da mai martaba,na san yafi kowa shiga tashin hankali da rudani,ki kula min dashi sosai,ki dawo masa da farin ciki da walwalar sa,na bar mai martaba a hannunki shukra!" Kukan su suka cigaba dayi sosai,a lokacin sai wata shaquwa ta shiga tsakanin su kamar kusancin da yake tsakaninsu ya dade sosai.

Washegari da safe chief secretary da sauran sakatarorin masarauta suka zo da saqon tsige queen haneefah har cikin quaters dinta,a zaune take a gaban chief secretary kamar mai zaman sallah,yayinda shi kuma ya fara karanto takardar da take hannun sa kamar haka:

A yau,biyu ga watan mayu (may) 1689.
Queen haneefah zata zamo mara muqami,kuma mutum kamar kowa.
Za'a karbi Kambun sarautar ta,da matsayinta daga gareta.
Kuma anyi mata umarnin barin cikin masarautar nan a nan take.
Hear and obey.

Runtse ido tayi jin yadda kalaman tsige ta daga dukkan wata matsayi da alfarma da take da ita,kuma zata tafi wani qauye inda sarki ya zabar mata domin ta zauna,kuma babu abinda zai qara kawo ta cikin garin ma balle kuma masarauta,miqa hannunta tayi ta karbi takaddar,a can gefe kuma chief maid dinta ce ta dauko crown dinta da stamp dinta akan tray ta miqawa lady sumayya,sai nadeeyah da basma da suka taho zuwa inda queen take zaune a qasa da hawaye a fuskar su,suka fara zare kayan ado da kwalliyar da suke cikin gashin ta,sai da suka gama cirewa kaf suka dora akan wani tray cikin muryar kuka suka ce
"Ki gafarce mu your majesty!" Sannan suka matsa suka koma inda sauran mutanen suke a tsaye,tashi tayi ta shiga cikin dakinta tare da cire duk kayan alfarma da alkyabbar ta ta sarauta mai zanen dragon,haka ta saka fararen kaya gaba daya,sai chief maid dinta da wata maid din guda daya da zasu bita suma da suka cire uniform dinsu,da hawaye akan fuskar su dukkansu suka fito,jerin hakimai manya da qanana na bangaren arewa duk sun durqushe a gaban quaters dinta suna kukan tafiyar ta,domin tafiyarta daidai yake da faduwar qarfin ikon mulkin su,haka ta qarasa har inda abin da za'a dauke ta a ciki yake (palanquin wani abu ne da sukeyin shi na katako,kamar minbarin maulidi amma a rufe yake ruf,ba'a gane waye a ciki,sai a samu maza majiya qarfi su daga sukai mutum inda zaije,ana amfani dashi ne ga mata 'ya'yan manyan mutane tunda su bazasu hau doki ba,kuma babu mota) maids din guda biyu suka bude mata qofar abin ta shiga sannan suka rufe,mazan suka dauka suka fara tafiya,ta baya suka zagaya suka bar quaters din nata,suka fita daga cikin masarautar sannan suka dauki hanyar qauyen da zata zauna.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now