Page 43

68 5 2
                                    

Page 43

Qarasowar su wajen mai martaba suka tarar da chief secretary yana yiwa mai martaba bayani kamar haka
"ya kasance kamar al'ada ce a royal treasury,basa barin wani yayi musu AUDIT (dudduba abubuwan ko kudaden da suke shiga suke fita a tabbatar komai yayi balancing) saboda kasancewar wajen yana qarqarshin ikon eunuchs ne" kauda kai mai martaba yayi
"Al'ada ko? Kawai dai suna amfani da qarfin iko ne,kasancewar sune suke kula da dukiyar masarauta,amma menene ya kawo matsalar tun farko?" Qara rusunar da kai chief secretary yayi
"Naji ance wata yarinya ce a cikin ladies investigators ta samu wasu 'yan matsaloli game da dukiyar masarauta" mai martaba ne ya juya ga chief steward,a cikin harshe mai kaushi ya fara yi masa fada
"A kan wane dalili ne zakuyi amfani da royal guards saboda matsalar ka ta kanka? Kawai saboda wani dalili na son zuciyar ka? Baka ganin abin naka ya tafi da nisa,zaqewar taka tayi yawa chief steward?" Rusunawa yayi da sauri yace
"Ka gafarceni your majesty! Amma lady investigators din ne suka tunzura ni sosai" da qarfi mai martaba yace
"Suka tunzura ka? Kana nufin saboda sun dage akan sai sunbi dokar masaruta?" Muryarsa ce ta fara rawa,ganin yadda ran mai martaba ya baci sosai,kanshi a qasa yace
"Your majesty! Ka gafarceni!"
"Royal treasury waje ne da dukkan dukuyar masarauta take,ya kanata ace kun zama abin koyi da wasu,amma kuka jawo min wannan abin kunyan?"
"Ka gafarceni your majesty! Nayi ba dai-dai ba" dauke kanshi yayi zuwa kan nadeeyah,cikin sanyin murya yace mata
"Kece lady nadeeyah ta office of investigation?" Rusunar da kanta tayi a tare da cewa
"Yeah cheo-na!" Murmushi yayi
"Na san ba abu ne mai sauqi ba karya tsohuwar al'ada da aka saba da ita,office of investigation kunyi matuqar qoqari,ina son ki bani bayanin duk yadda abin ya faru dalla-dalla kafin na san hukuncin da zan yanke"

A sukwane ya shigo quaters din consort jaleela,itama ganinshi a haka ta san ba lapia,cikin tsoro tace masa
"Kana nufin za'a iya samun matsala kenan?"
"Ban san yadda akayi ba,amma wannan yarinyar tana qoqarin bamu matsala a royal treasury,kuma hakan zai bamu gagarumar matsala" zaro ido tayi waje,domin yanzu bata son jin sunan matsala har sa an nada ta sarauniyar joshun,jaleel ne ya fara yi mata bayani
"A qoqarin sauke sarauniya haneefah,mun nemi kudi masu tarin yawa daga royal treasury,kuma wannan audit din zai iya bayyana komai your highness!"
"Me kace?"
"Ni ban taba tunanin hakan zai faru ba,ya akayi wannan yarinyar ta shiga royal treasury ne ma?"
"Ni na saka a kaita!" Da mamaki yake kallonta
"Saboda ina son ta bar masarautar nan,shiyasa aka kaita can domin ban san akwai wani abu da ya shafemu a can ba"
"Your highness! Lallai mun jawo wa kanmu matsala babba"

"Kina nufin da wannan kudin akayi amfani wajen sauke queen haneefah?" Shukra ce ta jinjina kai tace
"Haka nake nufi,shiyasa nake da buqatar da qara dudduba record dinsu,da abinda na samu anan,zamuyi amfani da dayar hujjar da muke da ita mu wanke laifin queen haneefah!" Afrah itama jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace
"Inda ace zanu samu hakan..."
"Ai hakan ma zamuyi,kuma yanzu da maganar taje wajen mai martaba,na tabbata zai yi mana abinda ya kamata"

Dawowar nadeeyah kenan daga grand palace duk ta wuce su suna tsaye ta shige office,Basma,shukra da Afarh ne suka biyota office din,basma ta fara cewa
"Nadeeyah kin dawo daga grand palace? Ya kuka yi da mai martaba?" Banza tayi musu,kuma bata dago ido ta kallesu ba,sai da Afrah ta sake magana,ita kuwa shukra ma jikinta yayi sanyi da yanayin nadeeyah
"Sai dai fa mu haqura da AUDIT dinnan!" Dukkansu zaro ido sukayi cike da mamakin kalamanta,shukra ce tace
"Me yasa haka?"
"Umarnin mai martaba ne! Yace bamuyi laifi ba don mu dage a kan aikin mu,amma zaiyi wahala a karya al'adar da aka dade ana kanta,sai dai wani lokacin kuma!"
"Mai martaba ne ya fadi hakan da kanshi?" Shukra ta tambaya
"Ehh haka yace" nadeeyah ta bata amsa,dukkansu shiru sukayi cikin rashin jin dadin hakan.

"Kana nufin mai martaba ya bi bayan Royal treasury?" Cikin farin ciki jaleel yace
"Haka ne your highness! Ai dama na san zaiyi hakan,tunda magana akeyi akan masu kula da dukiyar masarauta,mai martaba bazai bari wani abu ya faru ba" dan gajeren tunani consort jaleela ta shiga
"Ai kada ki damu your highness! Babu wata matsala a yanzu kam" jaleel ya jaddada mata,yayinda ita kuma tana jin akwai wani abu ba daidai ba,meyasa mai martaba zai hana investigators aikinsu,sai dai idan yana da wata manufar amma tunaninta ya kasa bata dalili.

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now