Page 10

73 5 0
                                    

Page 10

A bangaren shukrah kuwa shaquwa mai qarfi ce ta shiga tsakanin ta da mai martaba ba tare da ta san shi ne ba,yana jin dadin yadda take nuna yarintar ta da kuma yadda a karo na farko wani mutum a garin yana masa magana kai tsaye a matsayin ba kowa ba,domin shi tun daga haihuwarsa har girmansa ya zama sarki girmamawa ce tsakanin shi da kowa a qasar ko da kuwa shekarun mutum sunkai 100 ne,hakan yasa yake jin kamar wani 'yanci ya samu wanda da bashi da shi. Hakanan manager da sameer suma lokaci zuwa lokaci suna haduwa da mai martaba a wajen masarauta,su zauna suyi hira,su sha shayi tare ayi wasa da dariya.

Chief maid din lady jalila ce tare da wasu maids din suka shigo bureu of music,wajen manager suka nufa tare da isar masa da saqon lady jalila,shukra tana bakin rijiya tana hada kayan wanki zata fara wankesu maids din suka iso tare da manager,manager ne ya kalleta sannan ya kalli chief maid din tare da cewa

"Wannan itace yarinyar da ake magana,amma dai ba wani laifin tayi ba ko my lady?" Ya tambayeta fuskarsa da dan alamun damuwa,murmushi chief maid din jalila tayi

"Ahh babu komai,ba laifi tayi ba akwai wani abu da zata yiwa her ladyship ne"

Boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da maida kallonshi inda shukra take tsugunne,tare da zuba musu ido cikin rashin fahimtar inda zancensu ya dosa,yanayin ta ya karanta kafin ya bude baki yace mata

"lady jalilah ce take nemanki" zare ido tayi cikin kaduwa tace

"Lad....ladyyy jalilah kuma? Me nayi?"

Murmushi yayi mata tare da cewa

"Babu abinda kikai mata,amma dai ki tashi kije ko ma menene zaki ji" jikinta a sanyaye ta miqe tare da nufar dakin da take kwana,farar takaddar da take da zanen butterfly dinta ta dauko tare da budewa,runtse ido tayi tare da fadin

"Allah ka taimakeni yau idan na shiga cikin masarauta yau na gamu da court lady din da nake nema"

Saurin miqewa tayi tare da mayar da takaddar ta ajiye a inda ta dauko ta,fitowa tayi inda maids din lady jalilah suke suka tafi tare har quaters din ta.

Daga Shigowar shukrah ta sauke idonta akan lady jalila ta gane ta,farin ciki ne ya lullube ta cikin ranta take cewa

"Ina da tabbacin wannan itace court lady din da nake nema,kuma daga kayan da suke jikinta sun tabbatar mata cewar SPECIAL COURT LADY ce,Wato Matar mai martaba mai mataki na hudu,idan ma ba ita bace toh kamar tayi yawa,duk da shekara bakwai kenan....." kafin ta qarasa tunanin ta muryar chief maid din lady jalila ta katse ta

"Me kike yi a tsaye,greet her ladyship!"

Daidai lokacin itama jalila ta dawo daga nata tunanin,wanda bata san dalilin da ya sa tunanin ya fado mata a daidai wannan lokacin ba,tunanin ta kuwa bai wuce wani mutum da ta taba haduwa dashi har ya fada mata abinda yake daga mata hankali duk lokacin da ta tuno shi,a hankali ta furta

"Kamar yadda yace duk irin daukakar da zan samu tabbas ni zan zamo inuwar ta (shadow)"

Diriricewa shukra tayi tare da rusunawa sosai tamkar zata kai qasa

"Barka da hutawa My lady!"

Murmushi jalila tayi tare da cewa

"Zaki iya zama" a inda take tsaye kawai ta nade qafarta ta zauna a qasa tare da tunanin dalilin kiranta da kuma ta inda zata fara tambayar lady jalila maganar keyholder dinta,muryar lady jalila taji

"Shukrah ko? Na san zakiyi mamakin dalilin da ya sa na kira ki nan" ta dan nisa,ba tare da shukra tace komai ba ta ci gaba

"Na ji qoqarin da kikayi wajen gano gaskiya akan sharrin da aka so a qulla min,na kuma gode sosai,shiyasa na kiraki domin na nuna miki godiyata sosai,kunya ta bawa shukra yadda tayi maganar cikin sanyi da kuma tsantsar nuna ainihin karamcin da take dashi,murmushi shukra tayi

"Ba komai My lady! Ba sai kin gode min ba,ai ban cancanci duk irin wannan ba"

Murmushi mai sauti jaleela tayi

"ke kuwa kika cancanci har abinda yafi haka,duk da kina matsayin baiwa amma qwaqwalwarki bata bayi bace,saboda haka kada ki qasqantar da kanki,ta yiwu nan gaba ki iya zama abar alfahari a cikin al'umma,shawarata a gareki shine kada ki taba jin ba zaki iya cimma komai ba saboda kina kallonki a wani qasqantaccen matsayi,qoqari da qwazo suna kai mutum inda bai taba zato ba"

Jinjina kai shukra tayi,tayi matuqar jin dadin abinda jalila ta fada mata,chief maid ce tayi mata magana ta tashi ta biyo bayanta suka fito,a sannan ne ta bata aiki na musamman wanda jaleela bata san dashi ba domin umarni ne daga haj jameela mahaifiyar jaleela.





Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now