Page 14

55 5 0
                                    

Page 14

Duk tsawon lokacin da suka dauka a qarshe dai aka gama yiwa lady jalila tambayoyi,afrah ce ta kalli lady jalila cikin girmamawa tare da cewa

"My lady zan aika a kirawo maids dinki su raka ki quaters dinki" lady jalila ta miqe tsaye ba tare da ta kalli afrah ba tace

"A ah ki barshi,na san guda biyu suna jirana a waje,zamu tafi tare da su" tana magana tana takawa zuwa hanyar waje.



A daidai wannan lokacin an birkita ko ina a cikin quaters din lady jalila ba tare da saninta ba,ladies investigators ne masu pink din kaya ko ina a cikin quaters din suna ta bincike bincike,wata murya ce mai tashi tace

"Ga shi nan na samo" dukkansu suka dakata da abinda sukeyi tare da mayar da hankalinsu inda maganar take fitowa,wata yarinya ce lady investigator Sameerah,Basma ce ta qaraso inda take da sauri,sameerah ta rusunar da kanta tare da miqawa basma abinda ta samo,hakan yasa suka bar binciken tunda sun samu abinda suke nema. Maids din lady jalila suna ta kuka saboda qarshen wulaqancin da akai wa uwar dakinsu na binciken rashin mutunci,kuma gashi ance an samo abinda suke da yaqinin babu shi a cikin quaters din,tabbas wani makircin ne ake qoqarin qulla mata.





Fitowar lady jalila daga office din ta kalli gefenta da dayan gefen taga babu qyallin maids dinta ko daya,cike da mamaki a fili tace

"Me hakan yake nufi? Ya kamata ace suna jira na a nan,ko meyasa suka tafi?" Kafin ta gama tunanin abinda ya faru ta jiyo muryar lady sumayya tana cewa

"Ni nace su tafi su barki,domin da yiwuwar ba zaki tafi a daren nan ba" ta fada idonta cikin idon lady jalila,mamakin hakan ne ya cika jalila ta ce

"How dare you " cikin zare ido ta cigaba

"Ki dinga kallon cikin idona kina min magana babu ladabi?" lady sumayya ta dan saukar da idonta qasa ba tare da tace komai ba,shiru ne ya ratsa tsakani suna tsaye sai ga investigators basma da Aliya sun taho da faranti da bowl a kai,bowl din kuma pinellia ce da aka samo a quaters din jalila a cikin ta,suna zuwa daidai inda chief madam sumayya take suka tsaya da farantin a hannunsu,sumayya ta kalli jalila tare da cewa

"Wannan shine sakamakon binciken da akayi a quaters dinki kuma an samu pinellia da aka sawa queen haneefah a cikin tonic dinta har ya zama mai cutarwa"

Cikin firgici lady jalila take bin sumayya da kallo,daga bisani ta mayar da kallonta kan basma da aliya ba tare da tace komai ba,nan take zuciyarta ta bata anyi amfani da miqa kanta da tayi an qulla mata wani makircin,chief sumayya ce tace

"My lady zaki iya komawa ciki,domin yanzu you are under arrest da samun cikakkiyar hujjar qoqarin halaka uwar qasarmu,queen haneefa" idon jalila ne ya cicciko da ruwa,ta juya ta koma cikin office din,kan kujerar da ta tashi ta koma ta zauna,itama sumayya ta shigo ta zauna a wacce take fuskantar jalila,cike da rashin ladabi tace

"Muna tuhumarki da qoqarin halaka queen haneefah,ko zaki fada mana dalilin da ya sa kikai yunqurin aikata haka?"

Jalila idonta cike da ruwan da bata basu damar zubowa ta kalli sumayya

"Ban san abinda kike fada ba,domin babu abinda kuke fada a cikin quaters dina,ban san abinda kuke cewa ba,sharri ake son ayi min"

Ta qarasa maganar cikin murya mai rauni

"Amma ga abinda aka samo a quaters dinki,wannan ma kadai ya isa hujjar abinda muke tuhumar ki dashi" sumayya ta fada tana nuna mata bowl din da aka zuba ganyen pinellia a ciki,jalila ce ta zare ido tare da cewa

"Ki iya bakinki,ki san da wa kike magana cikin rashin da'a"

Cike da tsiwa sumayya tace

"Ke zaki iya bakinki saboda kina nan ne a matsayin mai laifi"

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now