Page 9

66 4 0
                                    

Page 9

Minister of State affairs ne cikin tsananin tashin hankali yake tahowa quaters din queen dowager,chief maid dinta ce tai masa iso a zabure ya shiga tare da durqusawa ko and rusuna mata baiyi ba alamun gaisuwa
"Minister lafiya kuwa na ganka haka?"
Cewar queen dowager,tashin hankalin da ke fuskarsa ne ya canja ya koma mamaki tare da ce mata
"Your majesty ke ya kamata na tambaya ya na ganki haka?"
Murmushi tayi tare da bashi amsa
"Ai no bani da matsalar komai,idan ma akwai to bata wuce kasancewar jalila ta kubuta daga tuggun da na qulla mata ba"
Jinjina kai minister yayi tare da cewa
"Hakane your majesty,amma nayi mamakin yadda duk wandanda aka kama basuyi magana ba"
"Ban tari numfashin ka ba,amma kana tunanin zanyi abinda idan ta baci zai dawo kaina ne? Hahaha " tayi dariya sannan ta cigaba
"Ai duk wanda zai min aiki sai na tabbatar zai iya bada rayuwarshi saboda yi min biyayya shiyasa ko da aka kama su banji komai ba"
Kada kai yayi cike da gamsuwa da qara girmama qarfin rashin imani na queen dowager,mutum har kusan bakwai sun mutu saboda asirinta ya rufu
"Idan baka da wata maganar zaka iya tafiya,jalila kuma in ta san wata bata san wata ba,mu zuba ni da ita" tayi qwafa,minister dai jan qafafuwansa yayi ya bar quaters din jikinsa a sanyaye.

A daren ranar shukra,manager da sameer suka fito wajen fada domin shan iska,dukkaninsu cikin shiga irin ta mutanen gari,babu wanda zai gane ma'aikatan fada ne suna tafiya a cikin kasuwa suna hirar su suka hango wani shago da ake saida lemuka irin na gargajiya haka,akwai tebura da kujeru a wajen shagon inda zaka iya zama kasha a nan,isar au wajen yayi daidai da zuwan wasu mutane suma,daya daga cikinsu yana ganin shukra yayiwa wanda suke tare alama da ido nqn da nan suka watse shi kuma ya qaraso inda su shukra suke,shukra ce ta fara lura da zuwansa wajen,cikin murmushi da tarin farin ciki ta ce
"Ranka ya dade dansanda yau ma mun sake haduwa"
Murmushi yayi mata mai qara fitar da kuawun fuskar sa,cikin rada yace mata
"Yaya sunanki yan mata?" Rufe fuska tayi saboda taji kunyar yadda yayi maganar itama a hankali ta mayar masa
"Sunana shukra "
"Hmmm suna mai dadi...."
"Shukra waye wannan kuma" muryar manager ta katse su,shukra ce tayi saurin juyawa inda yake
"Shine dan sandan sirrin da muka hadu dashi jiya" ta bashi amsa kai tsaye,A tare sameer da manager suka gaishe shi ya kalli shukra
"Tare kuke dasu? Me kuke yi a nan?"
Sameer ne ya cafe maganar "Ehh tare muke yallabai,munzo shan lemo ne ko zaka zauna kaima musha tare?" Murmushi yayi tare da cewa "toh ba matsala" tare da zama,ganin haka suma suka zauna,nan aka kawo musu lemon kwakwa,na abarba,na tsamiya,da dai sauransu suka fara sha suna hirar su sama sama,sameer ne ya kalli manager tare da cewa
"Yallabai baka ganin dan sandan nan yana maka kama da mai martaba?" Manager ne ya kalli mai martaba cikin tsanaki daga bisani yace
"A ah mai martaba ai yafi wannan kyau,shi kyakyawane sosai"
"Da gaske yallabai,mai martaba yafi wannan kyau" shukra tayi saurin tambaya,sameer ne ya bata amsa da
"Ehh ai kinsan yallabai manager ya taba ganin mai martaba lokacin wata liyafa amma daga nesa nesa"
"Uhm uhm uhm" mai martaba yayi gyaran murya,shukra ce ta juyo ta nuna shi da dan yatsa tare da cewa
"Kai kaine jiya ka bawa mai martaba labarin ni na samo mutanen nan ko? Ai ka sanshi kenan? Wai kyakyawa ne har yafika kyau?"
Muryarsa ce ta fara rawa,ya daure yace
"Ta yaya zan fadi hakan da bakina"
"Ehh?" Shukra ta tambayeshi,kafin ya samu amsar da zai bata manager yace mata
"Ke meyasa to kike ta tambaya,kina son kyakyawa kamar mai martaba ne?" Tabe baki skukra tayi tare da cewa
"Chabb me sanyi da namiji kamar mai martaba,ni bana son namiji ya fiya haske,kuma nafi son mai qwanji tsayayyen namiji " dariya manager da sameer suka sheqe da shi yayinda mai martaba ya tamke fuska,gudun kada su gane wani abin kawai ya taya su dariyar,haka suka cigaba da hirar su har dare ya dan fara nisa su sameer suka tashi suka tafi,yayinda chief eunuch suka bullo daga inda suka ɓuya domin raka mai martaba zuwa gida.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now