Page 60

111 8 4
                                    




Kamar yadda nayi muku bayani a baya,A tsarin gidan sarautar josheon,sarauniya itace shugabar inner court domin ita kadai ce matar mai martaba ta aure,bayan sarauniya akwai consort wanda suma consort din matsayi matsayi ne,rank 1-5,sai kuma concubine wacce ita kuma consort tafi ta matsayi,sai chief madam,sune kamar su sumayya da su chief maids din kowanne quaters,sai palace maids sune kamar su ladies investigators,ladies in waiting,masu girki,da sauran masu aiki a sauran sassan masarautar,sai kuma slaves (bayi) wanda su suke aikin wahala na share share,goge goge,wanki,diban ruwa da sauransu,kuma dukkansu haka suke a jere a matsayi,kowa zai girmama wanda ya fishi matsayi a cikinsu.
Kuma nayi muku bayanin cewar dukkan matan da suke cikin masarautar ikon mai martaba ne,yana da damar da zai iya neman kowacce a cikinsu,wanda duk wacce ta samu damar kwanciya a gadon mai martaba zata samu matsayin special court lady, daga nan zai iya daga darajarta zuwa concubine ko kuma consort,ya danganta da yanayin matsayinta a wajensa.

A halin yanzu shukra ta samu zama special court lady,zamu iya kiranta da matar sarki ta hudu duk da bashi da wasu matan bayan sarauniya jaleelah,amma matsayin mata ta biyu da kuma mata ta uku babu kowa a kai.
Matakan sune kamar haka
Matar farko - Her majesty The Queen (sarauniya)
Mata ta biyu - Royal noble consort /Royal Consort
Mata ta uku - Concubine
Mata ta hudu - Special court lady.
Wadannan na sama dukkansu matsayin matan sarki suke,amma kowacce da matsayinta,kuma dole concubine ta girmi special court lady,haka consort ta girmi concubine yayinda Queen ta kasance shugabar matan sarki da kuma dukkan matan inner court gaba daya.

A nan muka zo qarshen littafi na farko,zamu cigaba da littafi na biyu bayan sallah in shaa Allah
Ina yi mana barka da shigowa wata mai alfarma,Allah ya karbi ibadunmu ya sa muna daga cikin 'yantattun bayi.

Godiya mai tarin yawa gareku 'yan group din ROYAL CONSORT FANS na whatsapp da kuma HAFSAT HAUSA NOVEL na facebook 🥰🥰

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now